Document Body Page Navigation Panel
1
CHANGE
ABUBUWAN DA KE CIKI Locaci Shafi
Samun Ci Gaba SADARWA
Sabuwar Hanyar Yada Sakamakon Bicinke Ga Alumma. 2mins. 1sec 5 Sabon
rohoton da ya duba kokanton da masana suka yi a kan
hanyar isar da bayanan sakamakon nazari ga alumma.
ILIMI
Najeriya Da Sauran Kasashe Suna Amfana Da 1min. 51secs 3 Gudamawar
Litattafai.
Fiye da litattafai milyan biyar ne aka baiwa kasashen Afrika
gudamawa a cikin shekaru 30
KULA DA LAFIA
Yaki Ba Tare Da Nakiyoyi Ba 2mins. 1sec 7 Gaganmin haramta amfani
da nakiyoyi na samun nasara.
BATUNWAN DA SUKA SHAFI MATA
Ghana Ta Tsara Hanyar Baiwar Mata Karfin Iko. 1min. 5secs 13 Ghana
ta shirya shiga sabon karni da ingantacen shirin jinsi.
Matan Da Mazansu Suka Mutu Na 2mins. 58secs 6 Fafutukar Neman Izinin
kamun kifi a Afrika ta kudu. Mata tsofafi da mazajensu suka mutu
a Afrika ta kudu suna neman
izinin kamun kifi dai dai da maza.
Fafutukar Nemawa Mata Ikon Gado. 1min. 13secs 12 Matan kasashin
Afrika ta yamma suna neman yancin cin gadon
Kadarori
Muhalli AIKIN GONA
Kwari Na Kalubalantar Samar Da Abinci A Ghana. 1min. 39secs. 8 Sashin
Arewacin Ghana da ake noma zai iya asarar kashi 50 na abincin
da aka shuka a bana
Neman Ingansi Na Iya Rage Sha'awar 1min. 52secs. 4 Manoman Gargajiya
Manoman gargajiya Matsalolin cimma ingancin abinci na iya zama
binda zai hanawa kasashe masu tasowa samun nasu kason a kasuwar
kayan abincin da aka nama ta hanyan gargajiya.
SAUYIN YANAYI
Ruwan Guba Ko Zafaffar Duniya? 2mins. 9secs. 7 Maganin matsalar sauyin
yanayi ya yiwu baya da alaka ta kai tsaye
da muhalli
MANUFOFIN KARE GANDUN DAJI
Kalamai A Kan Yanayi Da Bani Adama. 33secs. 10 Wajibi ne mutane su
banbanta tsakanin rayuwar zamani da yanayi 1
1 Page 2 3
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
2
CHANGE
Zambiya Ta Fayyace Yawan Muhallinta. 1min. 45secs. 4 Kungiyayoyin
kasa da kasa da gwamnatin Zambia sun gudanar da
kididigar halittu da tsiran da ke kasar
AIKIN KAFA MASANAIANTA
Masana Kimiyya Sun Nuna Rashin Amincewarsu 1min. 24secs. 4 Da Aikin
Kamfanin Mitsubishi.
Shirin kafa masanaantar gishiri a muhallin da ake alfahari da shi ya gamu
da
fushin sanonun masu ilimin kimiyya.
GANDUN DAJI
Gandun Dajin Kasar Ghana. 26secs. 14 Takaitaccen bayani a kan arzikin
kataikon Ghana
GINA JIKI
Dankali Mai Ban Mamaki 45secs 13 An samar da irin dankali mai yalwar
yaya a Amurika
MASIFAR GURBACEWA
Kasan Yawan Iska Mai Guba Da Motarka Ke Samarwa? 31secs 14
Sabuwar hanyar da ake samar da iska mai guba.
Bukatar Sabuwar Naurar Kashe Gobara Mara Hatsari. 1min. 13secs. 5
Sinadarin kashe gobara yana gurbata ruwan karkashin kasa
KIMIYYA
Yiwuwar Karo Da Wata Hallita Daga Sama 52secs 14 Masana duniyar wata
sun yi imanin cewar wata hallita na iya fadowa daga
samaniya zuwa kasa.
MANYAN NAMUN DAJI
Magen Daji: An Fi Ganinta A Miyafiye Da Daji 1min. 40secs. 3 Magen
daji na fuskankar barin wanzuwa..
Kwaguwa Ta Sami Wazen Kiwo 2mins. 9secs. 8 Bayanai sun nuna cewar
kare lafiyar dabobi yana taimakawa muhalli.
SASHIN YARA
Kunkuru Da Kwakwa. 5mins. 24secs. 10 Yadda halin zarria kunkuru ya
kaishi ga jawowa iyalansa wahala.
Tsinken Da Ya Bace 3mins. 21secs. 11 Wani labarin ndebele daga kudancin
Africa wanda ya bayyana dalilin da
ya sanya dorina take da yagagen hanci.
Ko Cizon Mesa Na Kare Mutane Daga 1min. 7secs. 11 Cizon Sauran
Macizai?
Cizon mesa baya kare dafin cizon maciji.
Kadangaru Saukan Tsinke Bindinsu Ne 50secs 12 Don Gudun Masu Halaka
Su
Nemo dalilin da yasa kadangare ke tsinke bindinsa
– hatsari ne ko haka aka halice su. 2
2 Page 3 4
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
3
CHANGE
Labaru
Najeriya Da Wasu Kasashe Sun Amfana Da 1min. 5secs.
Kyautar Litattafai. Kasashen Afrika bakwai hadi da Najeriya zun samo wadanda
suka fi cin moriyar gudamawar litattafai
da wata kungiya a Amurika ke bayarwa, tun a Shekarar 1962. Sauran kashashen
sune na Zimbabwe, Zambia, Uganda, Liberia, Ghana da Ethiopia.
An saka Afrika ta kudu cikin jerin kasashen, da wanan ta shiga tarihi a fanin
samun gudamawar litattafai milyan 40.
Kungiyar da bata alaka da gwamnati mai suna (Brothers Brother Foundation) Watau
BBF tana baiwa kasashe masu tasowa taimakon Litattai domin "su sami ci gaba
a fanin samun ilimi mai martaba" Inji
Shugaban BBF Mr. Luke Hinson. Kungiyar tana bada gudamawar litattafai milyan
uku a kowace shekara ga kasashe masu tasowa. Ya yuwa wanan lokaci an barwa nahiyar
Afrika kyautar litattafai fiye
da milyan biyar.
Cibiyoyi da yawa sun taimaka samun nasarar kungiyar BBF na bada kyautar litattafai
inji Mr. Hingson,
fiye da kantunan walafa litattafai 50 suka ba da gudamawar litattafai sun hada
da lippincott – Raven, McGraw-Hill, Simon da Schuster, Scott-Foresman Highlights
sai litattafan yara wanda zaner Bloser da
John Wiley and sons suke bayarwa. Hukumar gudanar da aiyukan ci gaba ta Amurika
ce ke samar da kudin gudanar da aikin da kuma sashin kula da aiyukan gona na
Amurika, da sauran hukumomi na
Asia.
Kasashe da ake ba kyautar suna taka tasu rawar, domin ana nuna masu sunayen
litattafan da aka bayar domin su zaba, ta haka ana basu abinda su ke bukata.
Newslink Africa
Magen Daji: An Fi Ganinta A Tukunyar 1min. 40secs Miya Fiye Da A Daji
Magen Dajii dabba mai gashi da hakora kamar kugiya ta kasance tana fuskantar
barin wanzuwa, saboda ana daraja ta a matsayin abinci da magani. Wanan ne sakamakon
nazarin farko a kan halin da wanan
dabbar ke ciki, wanda asusun kula da halittu da tsirai WWF ya gudanar, Binkinken
ya nuna cewar sare itatuwa, aikin gona, farauta, ringinmu, tsakanin mutane da
kungiyoyin cinikaiya na duniya a matsayin
abubuwan da ke kalubalantar rayuwar wanan Dabba.
Farauta ta lahanta Dabobi uku na asiya, watau sloth, sun da black, Ana tsoron
cewar dabbar sun tana
fuskantar daina wanzuwa a indiya, aiyukan noma da fataucin kwayoyi, ya sanya
dabbar daina wanzuwa a Mexico, a nahiyar turai da arewacin Amurka rigingimun
mutane da dabobi ya hanata wanzuwa.
Ba'ada cikakkiyar masaniyar Dabbar a nahiyar daji sune nahiyan Turai, Asiya,
Arewaci da kudancin Amurica, Sanan an amfani da su domin yin maganin ciwon zuciya
da na anta a china, rohoton WWF
yace ana cin dabbar da kaji tankar…. 3
3 Page 4 5
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
4
CHANGE
Masana Kimiyya Suna Yaki Da Aikin Kamfanin Mitsubishi 1min. 2secs.
Shirin baya baya nan na kamfanin Mitsubishi a kan gina masana'antar gishiri
a mexico ya sanya sananun
masana kimiyya 30 su nuna adawarsu da aikin.
An tsara yin aikin a yankin Laguna san ignacio wanda aka yi shelar cewa muhalli
ne mai daraja, wanda hukumar UNESCO ta sanar a 1993. Kogin ya zama wanda ya
rage a yankin India manyan ifayen whale
ke rayuwa.
Kamfanin mitsubishi ya shirya tsotso galan 6,000 na ruwa a kowace dakika guda
daga kogin Zuwa filin kasa mai fadin sikwaya 116. Masana Kimiyya sun ce aikin
wani hatsari ne da baza'a amincewa muhalli
ba, sun dauki nauyin wallafa sakonin nuna adawa da aikin a jaridar New York
Time da sam Fransisco Bay ta jaridar Guardian da kuma jaridar la reforma da
ke Mexico.
Jagorar adawar Dr. Roger Payne wani sananen mai nazarin halittu wanda ya gano
cewar kifin whale yana rera waka, shin ya tattara bayanan kudurin masanan yace
"akwai bukarar kamfanin mitsubishi ya
yi amana da manufofin masana kimiyya fiye da bukatar mayar da muhallin kiwon
kifin whale zuwa masana'antar gishiri.
Agitprop
Zambia Ta Fayace Hilitun Da Ke Muhallinta 1min. 45secs. Kasar Zambia
tana da kimanin tsirai da halittu 8,000 a cikin kasar, binciken da ake kan gudanarwa
ya
nuna cewar kasar tana da yanayi iri daban-daban har 96, akwai gandan daji 500
da kebabbun gandin
daji da wadanda ake kulla da su, ga wasu muhallai na tsintsaye inda suke hayaiyafa.
Wuraren da ake kebe da su a gabacin Afrika sun kai fadin sikwaye mita 750,000.
Hukumar kula da halittu da tsivai ta duniya ce ta samar da bayanan gudanar
da bincike ta bukaci kasashe su tanttance irin halittun da suke da su, irin
amfanin su, ko ana jefa rayuwarsu cikin halaka,
hanyoyin da za a iya kula da raywarsu.
Binciken ya gano yadda ake dogaro da juna tsakanin dabobi da tsirai a Zambia,
donim tsirai na samar da muhalli su kuma dabobi suna samar da muhalin hayaiyafarsa.
Inji rohoton tsiran na taimaka samar
da ruwa mai tsafa da kare yanayin kasa, yabanya mai yalwa.
Sananen mai nazarin yanayin kasa na Zambia farfessa Emmanuel Chidumayo Shine
ya yayata rohoton binciken, chidumayo shine ya yara rohoton binciken rohoto
kungiyar kare muhalli ta duniya ta hanyar
hukumar gudanar da aiyukan ci gaba ta majalisar dinkin duniya ne ta dauki nauyin
binciken ana fatan rohoton Zai inganta yanayin halittu da tsirai, tare da tsara
hanyar da zara yi aiki da ita a Zambia.
PANOS
Tsadar Neman Cimma Inganci Zai Ragewa Manoma Da Basu Lahanta Muhali Kwazon
Noma 1min 52secs.
Ana samun karin bukatar kanyan abincin da basa yi amfani da maganin feshi
wajen nomasu ba a nahiyar turai da Amurika, manoma a kasashe masu tasowa na
kokarin kara yawan nomansu, sai dai
dokokin shiga da kayan da kungiyar alumma turai ta kafa, zai dakushe wanan noman
mara lahani ga muhalli, a kasashe masu tasowa. Tuni suka fara sukan kasashen
turai da laifin mulkin daniya. 4
4 Page 5 6
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
5
CHANGE
An bayyana sanya dokar ingancin da cewa nuna rashin damuwa da abinda
ke gudana a kasashe masu tasowa, musamman kananan manomma, misali shine manoman
da basu amfani da magani feshi su
ware gonakinsu da gonakin da ba'a nomawa, wanan abu ne da talakawa manoma ba
zasu iya yi ba.
Waba matsala ita ce bukatar manoman da ke so a tabbatar da concantar kayansu,
su biya masu bada shawara da ke turai, domin su amince da gonakinsu ana noman
garajiya ne.
"Samun wanan concantar domin shiga ksauwar nahiyar tuari yana da tsada ga
wahala ga kananan manoman kudanci". Inji Nick Robins na cibiyar kula da ci gaban
muhalli da ke London, wanda ke aiki
tare da shirin nazarin chanjin samar da abinci da cin sa.
Duk da cewa ana samun karuwar kasuwancin kayan gonan noman gargajiya, inda ya
kai dolla milyan
dubu 11, akwai alamar cewa kasashen Afrika basu san da wanan kasuwar ba, amma
kasashen kudancin Amurika suna tsara tattalin arzikinsu ta yadda zai bi wanan
hanyar, kasar chile kawai tona fitar da fiye
da ton 2,000 na kayan noman gargajiya a shekara 1998, inda ta sami dolla milyan
uku. PANOS.
Akwai Bukakar Naurar Kashe Gobara Mara Hatsari 1min 3secs. Ana amfani
da sinadarin kumfa domin kashe gobarar hatsarin jirgin sama wanda zai iya gurbata
ruwan
karkashin kasa, masu bincike ne suka gano wanan. Gobarar jiragen same tana faruwa
ne ta dalinlin konewar mai wanda ruwa ba zai iya kashaewa ba. Saboda hala aka
samarda sinadarin (Aqucouss)
watau AFFF Musamman domin kashe gobarar cikin hanzari ta hanyar fesa shi shi.
AFFF yana kunshe da sinadarin huorocarbons da hydrocarbons, wadanan na daga
cikin sinadaran da ake zargin idan aka
fesa su, zasu iya gurbata muhalli.
Dr. Jennifer Field ta jamiar Oregon da ke Amurika ta yanke Shawarar binciko
inda sinadarin AFFF ke shiga idan an fesa shi a muhalli. Ta yi nazarin ruwan
karkashin kasa da ke barikin soja da tsoffin kayan
kashe gobara da ba'a aiki da su, inda ta gano abin mamaki cewar sinadarin AFFF
baya narkewa a muhalli, a wasu wurare sinadarin ya taru wuri guda a karkashin
kasa.
Bincike na ci gaba da kokarin tantance zahirin hatsarin da gurbatar sinadarin
AFFF zai iya haifarwa ga rayuwar bani Adama.
Environmental News Network
Shirye Shirye (A Cikin Nishadi) Sabuwar Hanyan Sadarwa Tsakanin
Masu Bincike. 2mins. 1sec.
Wani rohoto ya bada Sahawarar sabuwar hanyar sadarwa da zata cike tazarar
da ke akwai tsa kanin masu bincike, masu tsara manufofi da masu aiwatar da aiyukan
ci gaba, an wallafa rohoton domin cike
gibin a fanin sadarwa, Arren Saywell da A. P. cotton ne suka rubuta rohoton
da fatan samun amfanin binciken da ake yi ya kaiga talakawa da kungiyoyin da
ke wakiltarsu.
An rubuta rohoton ne bisa binciken da aka gudanar a Jamai'ar coughborough,
inda aka yi nazarin hanyoin da ake bi wajen gudanar da bincike. Nar 29 irin
ya binciko hanyoyin sadarwa da zasu biya
bukata da matsalolinsu, tare da hanyoyin taimakawa sadarwa. 5
5 Page 6 7
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
6
CHANGE
Masu binciken sun gano cewar yanwan aiyukan binciken da aka gudanar
a fanonin a gaba basu kaiwa ga alumma talakawa da kungiyoyin da bana gwamnati
ba, soboda ana raraba bayanan ne a karshen
binciken kawai.
Rohoton yace "Aikin bincken a wanan matakin na kokarin biyan bukatar kungiyoyin
da suka dauli nauyin samar da shi, ba wai maida hankali ga wadana zasu amfama
ba.
Manufa ce a sama da bayanai daukacin lokacin aikin binciken. "Kamata ya yi
a samar da bayani kafin bincike do lokacin da ake yi da bayan kamala shi" Inji
rohoton. Wanan tsarin ya bada damar samun
sakamakon binciken a lokacin da ake nazari.
Sauran shawarwarin samun sadarwa mai inganci ta hada da samar da kyankyawan
manufar mutane da
ake fatan sadarwa ta kai garesu, tare da tabbatar da samuwar nazarin bi yadda
zai zama abin sha'awa da saukin amfani. Haka nan za'a yi amfani da kafofin yada
labaru domin shiryawa do watsa bayanan a
takaice.
Wadanda suka rubuta rohoton sun yin Imanin cewar, kamata ya yi a ce samar da
sakamakon binciken ya
zama aikin da ake yi kowane lokaci, kuma ya zama manhajar shiyawa da aiwatar
da bincinken. id21 Report
Matan Da Mazajensu Suka Mutu Suna Fafutukar Neman
Izinin Kamun Kifi A Afrika Ta Kudu 2mins 58secs Kimanin mata 14 da mazajensu
suka mutu a birnin Cape Town na Afrika ta kudu suna fafutukar neman
izinnin kamun kifi kamar mazaje. 1zinnin kamun kinfinsu ya daina aiki da zaran
mazajenbu sun mutu, gashi an barsu da nauyin kula da iyali ta hanyar dan kundin
da suke samu ta hanyar kamun kifi a garin
kalk bay.
Matan sun aike da takardun neman izinin kamun kifi tun a 1994, amma kowane lokaci
ana han su izinin.
"Bamu san dalilin da yasa basu bamu izini ba muna cinkin fatan samu ne," inji
Mrs. Edward, wadda
mijinta masunci ne na shekaru 40.
Kakakin matan melody kingma yace sun shirya amfani da kudin da zasu samu wajen
kamun kifin, domin gina dakin shan magani da kayan jin daddin rayuwar matan
da mazajensu suka mutu da nakasasu
a kalk bay.
Daya daga cikin matan Mrs. Gairnssa Fortune tace kungiyar ta samai cikakken
bayanin dalilin da yasa ake kin amincewa da bukatar tasu. "Ina tuanen cewar
basu son raba kudin da suke samu da mu" Inji ta.
Mafi yawan matan suna rayuwa rayuwa ne a kan kudin fasho na dolla 100 a kowane
wata, wasu suna iya ajiye wani abu daga ciki. Monica Collison mai shekara 68
wada take kula da yara bakwai bayan
mutuwar mijinta shekaru 20 da da suka gabata tace garin baya da kaya irin su
kantin sayar da magani mayanka, gidan biredi da kasuwa, wanan ya tilastawa mata
tafiya wasu wurare domin biyan bukatunsu,
suna tsoron shiga halin rashin lafiya su kasa samuin magani a yankin. 6
6 Page 7 8
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
7
CHANGE
Maitaimankin Daraktan kula da hallitun teku willelm kroon ya kasa cewa
uffan a kan dalilin hanawa matan iz\ inin kamun kifi. "Wajibi ne su bi sharuddan
da aka gita, su kuma yi fatan alheri" inji Daraktan.
Kamun kifi abu ne mai girma da mutane da yawa ke son shiga cikin sana'ar.
Matan sun hada da Sybil Edward mai shekaru 73 da kawayenta 13 masa shekaru 56
– 188 a yanzu suna son a basu wani abu, suna fatutukar a basu nasu kason izinin
kamun kinfin, sun shirya daukar hayar
masu kamun kifi a kalk bay wadanda zasu ji masu aiki idan su sami nasara Africa
News On Line
Yaki Ba Tare Da Nakiyoyin A Da Ake Biznewa A Kasa Ba 2mins. 1sec Fiye
da nakiyoyi milyan 250 ne aka samar a duniya, kuma banya gangami na shekaru
da yawa na kawar
da nakiyar, milyan 12 ne kawai aka lalata. Amma masu gangamin kawar da nakiyoyi
sun yi imanin cewar duniya bazata zauna lafiya a da nakiyoyi ba a lokacin zaman
lafiya. An kiyasta cewar kashi 10
na alumna duniya suna tarne da nakasa sassan jikinsu ta dalilin nakiyoyi da
aka bizne a kasa.
Alal misali kusan dukanini kasashen duniya sun sanya hanu a kan yarjejeniyar
haramta amfani, ajiyewa
da samar da nakiya, da ma safararta, kimanin kasashe 38 da suke samar da nakiyoyi
sun haramta yin hakan, sauran kasashe 16 basu samar da nakiya ko guda daya ba,
Iraqi ce kawai bata bar safarar nakiya
ba. Abu mai muhimmanci shine kasashen da ke cikin-rigima baser amfani da nakiyoyi
wajen yaki.
Binciken da aka gudanar domin kokarin kawar da nakiya ya nuna cewar an lalata
milyoyin nakiyoyi,
kuma an rage samr da su da raguwar safarar su. Rohoton kula da nakiyoyi na shekari
1999 watau " kokarin samun duniyar da babu nakiya wanda kungiyar kula da nakiyoyi
ne ta walafa, Wanan gamayyar
kungiyoyi ne da ke aikin haramta amfani da nakiya, fiye da masu bincike 80
da ke kasaseh 100 da kungioyi 1300 suka bada taimakon rubuta rohoto mai shafi
1100.
A kwananan aka gabatar da rohoton a wajen taron kasashen da suka haramta amfani
da nakiya a maputo, mozambique, wadanda suka rubuta rohoton sun alkawani bitarsa
kowace shekara a matsayin gangamin
kawar da nakiya. Newslink Africa
Ruwan Guba Ko Zafattan Duniya 2mins. 29secs. Fafutukawar rage gurbata
yanayi da masana anta ke yi zai gamu da cikas nan gaba kadan idan har
gargadin da wani farfesan wata jami'a ya zama gaskiya. Farfesa Michaeil Schelsinger
Kwarare a Fanin Kimiyar Zamani na Jamiar Illinois da ke Amurika, ya yi gargadin
cewar kokarin rage sinadari mai guba
na acid zai iya haifar da yawaitar zafaffar duniya.
Sindarin sulfur da na carbon masu guba wadanda suke fitowa daga masana'antu
da motoci zuwa samaniya sune musabbabin zafaffar duniyar. A cikin iskar da ke
sama sinadarin sulfara yan haduwa da iska mai
lafiya da ruwa, inda yake rikidewa ya zama ruwa mai guba da ke saukowa kasa
ta hanyar ruwan sama.
Domin dakacar da wanan, masana'antu na rage sinadarin sulfur da suke samaruwa,
suna barin iska mai guba, wanan yana da lahani mara tushe ga yanayi wanda ake
kira zalarrar duniya.
Yanyin da iska mai guba take haduwa da rana ta kara yawan zafin yanayi, sinadarin
sulfaur da ke 7
7 Page 8 9
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
8
CHANGE
haduwa da ruwa da iska a yanayi wanda ke haduwa da hasken rana ya koma
samaniya domin a samun sauyi. Wani mai tuntubar juna a kan samun chanjin yanaji
ya goyi bayan a sami dakatar da samar da
wadanan sinandaran domin dakatar da ruwan guba.
"Abin mamaki ne a locain da kake kokarin shawo kan wata matshaal sai ka gan
wata matsalar" inji Schlesinger.
Nazarin da Schlesinger da abokan aikinsa suka gudanar sun gano cewar rage
samar da sinadarin sulfur
na dalilin samuwar zafaffar yonayi a arewacin Amurica da nahiyar turai da Asiya.
"Wanan ya nuna cewar rage yawan sinadarin sulfur domin rage samuwar ruwa mai
guba na iya dalilin kara samun
matsalar zafaffar yanayi a yankunan da aka sami raguwar samuwar sinadarin
sulfur ta iska, " inji Schelensinger".
Environmental News Network
Kwaguwa Ta Sami Zama Muhallinta 2mins. 9secs. Akwai alamun da ke
nuna cewar rayuwar manyan dabobi na dogara ne a kan sauran dabobi, alalmisali
dabbar kwaguwa da rayuwata kecikin hatsari na bukatar teku mara inganci domin
ta rayi, sabon bincike
ya nuna cewar gabar takun na iya bukatar dabbar sosai domin rayuwar tekun.
Kwaguwa mai tsawo da ke Amuriak an santa da tafiyan kilomita 2000 domin ta
nasa kwai a cinkin yashin gefen teku, inda suke kyankyashe su masu kare muhalli
suna fafutukar kare bakin tekunan
domin dabbar, binciken da warri dalibin Jamiar Florida ya gudanar a ka bakin
tekan Melbourne ya nuna
cewar kwan da wanan Dabbar ta sakea, na kunshe da muhimman sinadaran inganta
yanayin gabar tekun da kyautata kasar yankin tare da samar da abinci ga dabobi
iri daban-daban.
Sarah Bouchard dalibin jami'ar Florida ya gano cewar sinadarin da ke cikin
kwan kwanguwa na taimakawa rayuwar bakin teku ta hanyoyi da yawa. " Kananan
halittlu, tsintasaye da sauransu na cin
kwan tare da wawatsu su cikin kasa da yashi, ciyayi kan fito a kan kwan su fasashi
domin samun kaiwa ga sinadarin mai gina giki, da zaran an kyankyashe kwan, ruwan
ya kan zuba cikin kasa ya inganta
yanayin kasar yankin" Bouchard ya gano a bicinkensa.
Fiye da kwayaye 65,000 ake nasawa a kowace shekara a gabar tekun Florida, kuwaguwa
ta kan yi
tafiyar daga wajen kiwonta da ke Bahamas, Cuba da jamhuriyar Dominican da yankunan
Florida a sauran wuraren da ke kudu ma so gabaci da gaba tekun carribean. Biciken
da za'a yi nan gaba zai gano
abinda ke faruwa a fanin taimakon rayuwar gaban tekunan da kwaguwa bata na
sa kwai a yankunan Environmental News Network
Tsutsa Na Kalubalantar Samar Da Abinci A Ghana 1min. 39 Secs. Tsutsa
ta mamaye yankuna uku da ake noma a arewacin Ghana, inda ta lahanta amfanin
gona irin su
dawa, masara, gero da shinkafa. Haka ta lalata ciyawar kiwon dabobi, kwarin
sun lalata fiye da necta 72,000 a gabacin Ghana da wasu hecta 10,000 na shuka
a yammacin kasar, ga wasu yankuna shida da
abin ya shafa.
Bisa damuwar cewa za'a yi asarar kimanin kashi 50 na amfanin da aka shuka a
bana, ministan kula da yankin gabacin Ghana Alhaji Amidu Sulemana ya yi gargadin
cewar rayuwa a yankin Arewacin kasar 8
8 Page 9 10
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
9
CHANGE
na fuskantar kalubale, minstan ya bukaci, gwamnantin Ghana ta hanzarta
samar da magnin kwari
Matsalolin lalalewar mu hualli da rashin ruwa shine ke kawo matsalar kwari,
ma'akatar gona tace idan
aka sami ruwa mai karfi za'a sami saukin matsalar. Mataimakin shugban kasa Ghana
farfessa John Atta mills wanda ya ziyarci yankin, ya yi alkawarin cewa gwamnati
za ta taimaka da iri domin a sake
shuka, tare da baiwa manoman da tsutsar ta yiwa bana taimakon takin zamin.
A halin da ake ciki hukumar talafawa wadanda balasiya afkawa ta Ghana da ma'aikatar
abinci da
aiyukan gona na jagorantar shirin yaki da kwarin, a yayinda ake ta addu'oin
rokon ruwan soma a wajen Ibadan.
Edward Ameyibor.
Ghana: Matakan Sadidan Na Kawar Da Sare Itatuwa 2mins. 41secs. Kasar
Ghana wadda ta yi asarar kashi 2 /
3 na gandun dajinta a wanan karnin, ta dauki matakan magance
sare daji da bada kwarin guiwar kare gandun daji. Kasar ta sake dawo da dokar
da ta bada izinin a sare itace a daji bayan shekaru 15 ana renansu na shekaru
40.
Sauran matakan da aka dauka sun hada da haramta safarar itacen da ba'a sarrafa
ba daga irin katako 14 da suka hada da icen mahogany. Wani bincike kan dokoki
da aka yi ya nuna cewar wanan bai hanawa
masu sare icen ba bisa doka gudanar da aikinsu ba, gandun dajin Ghana ya ragu
daga hecta milyan 23 a shekarar 1901 zuwa hecta milyan 8.3 a yau gwamnati da
masu kare muhalli suna ta kokarin dakatar da
a sarar gandun dajin kasar.
"Aiwatar da wa'adin shekaru 40 ya 20 dai dai da lokacin da mafi yawan itacen
da ake fataucinsu iri 14 zazu isa sare su" Inji Mr. Water Gyabaah-Atuomi jami'in
kula da gandun danjin Lardin offinso. " An
tabattar da sanya wanan dokar duk da cewa an samu rigingumu a wasu lokuta da
masu sare daji ba izini, wadanda kan saran itace da dare"
A kwanaki wata kotu ta ci masu sare itace ba Izimi tarar ceids 400,000 kimanin
dolla 160, tare da amshe katakon da zasu yi safararsai, jamin'in kula da ngandun
dajin yace zasu iya samun ribi 10 fiye da
katakon da suka samu ma'alkatar kasa da gandun daji ta kiyasta cewar Ghana na
osarar fiye da dolla milyan 10 ta hanyar masu fasa-kwaurin katako. An ce sabuwar
doka mai tsanani tana gaban majalisar
dokokun Ghana domin neman amicewa.
A dai dai lokacin da ake samun ruwon sama yanzu an fara gangamin dashen itace,
mafi yawan larduna sun sanya gasa a tsakanin makarantu a kan dashen ice, yayinda
kungiyoyi suna ta gangamin ganin an
kare muhalli ta hanyar fadada dajin kasar. Kafintoci da kungiyar manoman da
na kwadago suna ta
neman ganin an haramta safarar kalako, amma mai yiwuwa gwamnati ba zarta amince
ba, saboda katako ne hanyar samun kudin shiga ta hudu da gwamnanti ke dogaro
da ita wanan ne matsalar da kazar
Ghana ke ciki yayinda gwamnati ke son kare muhalli da iganta gandun daji,
haka nan tana son daloli domin cimma bukatar shiga da kaya.
Edward Ameyibo Accra. 9
9 Page 10 11
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
10
CHANGE
Sashi Na Musamman Kalamai A Kan Yanayi Da Dan Adam 33secs
Daya daga cikin kalubalen kare gandun daji shine samar da dai daltuwa tsakanin
bukatun rayuwa ta yanzu, bukatar samun abinci tare da rayuwa a muhallin da ke
akwai damar tattalin arziki. Tare da
samun amfanan jin dadin rayuwar birane tare da jin dadin shakatawa a gefen birane,
inda za'a sami rafuka da magudanan ruwa: tare da tabbacin samun tsintsaye da
zasu ci gaba da kwantar da hankalin
mutane. Conservation Quotations/ George B-Director Of U. S. National Park
Service.
Sashin Yara Kunkuru Da Kwakwa 5mins. 24secs.
An yi wani lokaci da aka yi fari a dajin dabobi, abinci ya yi wahala kuma
kowane tsuntsa, daba da kwari suka bace, abinci ya yi wuya da tsada, sabode
haka rayuwa kowane dabba ta dogara ga abincin da ya
nemo.
Wata rana kunkuru ya fita neman abinci sai ya sami kwakwa, a lokacin da ya zo
dauka sai kwakwar ta kufce ta fada ramin da ke kusa da icen kwakwa, saboda bukatar
ya danko ta sai ya shiga ramin inda ya
hady da dodo ya tambaye shi kwakwar ya shaidawa kunkuru cewa ai dansa ya cinye
kwankwar.
Sai kunkuru ya fara kuka inda nan take ya suma, yana ikirarin zai kashe kanshi
muddin ba'a bashi kwakwar ba. A maimakon haka ya bukaci a bashi diyar dodon
a madadin kwakwar, bayan duk an yi
kokarin bashi hakuri abin yaci tura, sai aka bashi drum na abinci a matsayin
diyya, duk lokacin da aka buga drum din sai abinci iri-iri ya yi ta fitowa,
dodon ya yi garadin cewar kada a sake a wanke drum din,
idan do aka wanke shi to shine zai baci ba zai sake samar da abinci ba.
Kunkuru ya godewa dodon ya tafi da drum na abinci. Yana isa gida ya tara matanshi
da yayansa a daki ya rufe dakin. Ya buga drum din sai abinci ya fara fitowa
iri-iri, duk suka ci, bayan sun gama kunkuru
ya garagdesu da su yi shiru da bakinsu saboda baya son raba abincin da sauran
dabobi da tsuntsaye, ya
kuma gargade su kada su wanke drum din.
A lokacin da sauran dabobi ke tsukewa kukuru da iyalansa sai kiba suke. Da
sauran dabobi suka tambaye shi sai yace uwarsa da ta mutu ne ke ciyar da su,
wadanda ke so to su kashe uwarsu, tunda sauran dabobi
basu yarda da kunkuru ba sai suka rabu da shi suka ki kashe uwarsu, suka daina
batun son sanin hanyar
samun abincinsa.
Bayan wani lokaci sai kunkuru ya yi tafiya, a lokacin ne matansa suka lura
cewar drum na abincin ya yi datti, sai suka wanke shi domin tsaftace shi. Bayan
da suka wanke suka shanya shi a rana suna tunani
sun yi aiki mai kyau, amma a lokacin da yunwa ta kamasu suka buga drum din babu
abinda ya fito, sai
suka aikawa kunkuru wanda ya zo domin nemo wani drum din.
Ya nufi wajen itacen kwakwan na da ca ya yi sa'a ya sake samun wata kwakwar,
wadda ta fada caikin ramin, sai kunkuru ya nufi dodon ya zargi diyarsa da cewa
ta cinye mashi kwakwarsa. Dodo ya karyata
ya dauko kwakwar. Kunkuru yace ai ba ita bace saboda haka zai hashe kansa ko
a bashi wani drum din,
sai dai ya yi kuskure daya bai umuci dodo ya buga drum din kafin ya dauka zuwa
gida ba. 10
10 Page 11 12
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
11
CHANGE
Yana isa gida ya kira iyalansa ya rufe kofa suna sa ran ganin abinci
ya fito abin mamaki sai dai suka ga kwari irin su kudan zuma suna ta fitowa
suki yi ta harbinsu, saboda kofar na rufe suka yi ta harbinsu sai
da aka kwantar da su a asibiti.
Darasin wanan labarin shine mu yi kokarin zama masu gaskiya, mu guyi daukar
abinda ba namu bane. Character Moulding Stories For Better Citizenship.
Tsi Nke Da Ya Bace 3min. 21secs Wata rana a zamanin da giwa da Dorina-Suka
yi yar gardama wadda ta kaisu ga fada dukaninsu dabobi
ne masu saurin fushi, dorina ta yi fada inda ta yiwa giwa rauni saboda kahonta
mai tsini, amma zuciyarta ta sa ta yi fada a makance. Giwa ta kwantar da zuciyarta
saobda sanin cewar tafi ta karfi kuma idan ta
yi amfani da haurenta nan take sai ta sami nasara, a karshe dole dorina ta hakura
inda aka kukujeta ta
gudu Dorina ruwa na cikin azabar radadi inda ta ke zubar da jini, sai ta nemi
taimakon bushiya wadda ta yi fatan zata taimaka mata ta nemi da bata tsinkenta
guda mai tsini wanda zata iya amfani da shi
domin dinke raunin da ta ji.
Bushiya bata yi farin ciki ba yadda aka tashe ta daga barci, ta matsu da ta
koma barcinta sai ta ta amince
ta bata daya daga cikun tsinin bisa sharaddin idan ta gama zata dawo da shi,
ta numa tausayi gareta.
Tsinkena ta ce da su nike amfani domin kare kaina daga makiya, kamar zaki
da sauransu na dogara gareki ne ki dawo mani da shi
Dorina ta amince tace zata dawo mata da shi a gobe dorina ta dinke fatar tikinta
ta amfani da tsinken da zaren tacen baobabi, dalilin wanan ne kake ganin fatar
dorina a tattare Bayan ta gamsu da kamala aikin
sai ta kwanta a ciyawa domin hutawa tare da warkewa, sai ta ajiye tsinken bushiya
a kusa da ita domin boye shi.
Wata ran da maraice bayan yan kwanaki sai dorina ta hadu da bushiya nan take
ta tuna da alkawarinta, amma ta kasa tuna wurin da ta ajiye tsinken, ko kuma
halin da tsinke yake, abinda kawai ta tuna shine
yadda ta yi amfani da bakinta ta dinke jikinta, wayoh ni! Ta tuna " ko na hadiye
shi ne bisa kuskure?
Bayan tunani mai tsawo dorina ta kamala cewar ko ta hadiye tsinken ne, amma
idan ko ta badiye shi to
zai gamu da irin halin da ya samu sauran abubuwan da ta hadiye a kullum. Dorina
ta yiwa bushiya wanan bayanin tare da neman gafara, ta yi alkawarin maido da
tsinke. Wanan ne ya sanya dorina kan ta
buga kanta a kasa da fatan gano tsinken bushiya domin zaton ya fadi ne. When
Hippo Was Harry.
Shin Cizon Mesa Na Iya Kare Muttum Daga Cizon Sauran Macizai? 1min. 7secs.
A'a, wanan ba gaskiya bane, babu shaidar kimiya da zata nuna cewar cizon
mesa na iya kare mutun daga dafin sauran macizai, kamar yadda wasu kasashen
da ke gabacin Afrika suka yi imani duk da
cewa ita mesa tana cizo tana daga cikin rukunin macizai na (constrictions) wadanda
basu da guba a jiki kashe gbinda suke son ci sukan murde dabar ta hamyar zagaye
ta har ta mutu.
Cizo daga mafi yawan dabobi na dalilin kamuwa da cuta, mesa bakayi cizo ne
idan ta esorata, mutanen 11
11 Page 12 13
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
12
CHANGE
da mesa ta ciza suna iya mutuwa idan cizon da yawa, ba saboda guba ba.
An gano cewar mutane na mututwa ne dalinlin cizon mesa saboda tsoro ba don guba
ba. Saboda haka muna shawartar ka da
gujewa macizai, sai dai idan ka sansu, in ba haka ma zaka sha mamaki Chogololo
Ko Kadangare Na Karya Bindisa A Kokarin Gajewa Hallanka? 50secs.
Wanan gaskiya ne, mafi yawan kadangaru kanana ne kuma suna da makiya da
yawa, suna amfani da gudu damin bada da kama bindinsu domin gujewo halake, kamar
bera, maciji da tsuntsaye. Masu
bincike kimiyya sun yi binciken cewar sun gano bindin kadangare bashida karfi
a sauran jikinsa, motsa jiki da yawa na iya sa ya tsinke. Bindin da ya stinke
yakan ta motsi sabodo yana da hallitu a cikinsa.
Lokacin da mai neman kamashi ke kalon bindin, kadangare ya gudu da nisa.
Akawi irin katangaru 3,000 a duniya, akwai masu alaka da kada da maciji, mafi
yawansu suna sama a yanayi mai zafin suna cin kwari domin su rayu.
Chongololo
Batutuwan Mata Fafutukar Bawa Mata Izinim Sum Gado 1min 13secs
Gamayyar kungiyanyin mata daga kasashen Afrika bakwai sun yi bikin ranar
nemawa mata yancin karbar gado, ranar ta 29 ga wantan yuni an yi binkin a ksashen.
Burkina Faso, kamaru, Gambia, Ghana,
Liberia, Nigeria Senegal da Togo tare da taimakon kungiyar kare hakin jama'a
da ke a Washington Amurika.
Ramar tunawar da kokarin baiwa mata ikon cin gado wani gangami ne da aka dade
anayi, da nufin jawo hankalin kasashe kan dokokin gargajiya da suka hanawa mata
izinnin gadon kaya da dukiya. An fara
shirin ne a wajen taron d aka dira wanda kungiyan kare hakin jama ta gudamar
a watan nuwambar Shekari 1998 a Ghana. A wajen taron matan sun amince a giwatar
da aiyukan da suka hada da batun
samun yancin mata su yi gado, da nufin kawo karshen matsalolin.
A wasikar da suka yi kiran goyan bayan gongamin, Marie-Elena John Smith mai
kula da harkokin kungiyan a Afrika ta yi kiran a sami karin wayar da kan jama'a
game da matsalolin a matakin kasashen
duniya.
Ana ci gaba da aikata wanan hallaiya duk da samuwar dokokin/ hukuma a mafi yawan
kasanshe da suka samarda da dan karamin dama ga mata su yi gado wanda ya yi
sakamakon, jefa milyoyin mata da yara
cikin halin barace barace.
A yanzu kungiyar tang rababa wasiku zuwa ga majalisar dinin duniya da kungiyan
hada kan kasashen
Africa OAU, Inda ta bada shawara kawar da bambacin jinsi ga mata. International
Human Right Law. 12
12 Page 13 14
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
13
CHANGE
Ghana Ta Tsara Hanya Baiwa Mata Karfin Iko A Kasar 1min. 5secs.
Majalisar kula da yawan alummar Ghana ta tsara shirin da zai maida hankali
a fanin mata da kanan
yaran mata a karni mai zuwa. Da yake jawabi a Accra Ghana Sakataren igudanarwa
majalisar Richard Rerrison yace barwa mata karin iko, ilimin yan mata da zubar
da ciki ta hanyan mata da zubar da ciki ta
hanyan mai hatsari shine dalilan da za'a sanya gaba a cikin shirin. Majalisar
zata yi aiki tare da ma'aikatu da sassan gwamnati da kungiyoyi domin wayar da
kan alumma a kan tasren jinsi. Inji Turson, yace irin
wanan aikin dadin quiwar ya rage dubarun rage hayaiyafar alumma a can baya.
Nasarorin da cibiyar ta samu a lokutan baya sun hada da tsarin kula, da lafiyan
matasa, atsakaicin tsaren kula da lafia, dubarun sadarwa da dokar yara kanana
da aka amince da ita aiyukan ciyan ya sayan an
sami raguwra haihuwa daga fiye da yara shida ga kowace mace, zuwa ga kasa da
yara biyar.
Akwai Yawaitar Muzguanawa Yara Kasar Uganda 1min 41secs Ana azabatar
da yaran Uganda ta hanyan duka, a yiwa wasu fiyade tare da horada su wanda iyaye
da
baki ke aikatawa, kuma da alamu ba'a daunki wani mataki ba wanan ne rohoton
da jaridar monitor ta ranar 13 ga watan yuli ta wallata.
Jaridar ta ruwaito cewar ana bugun yara har su kaiga suma a gidaje da makarantu,
ana kashe wasu saboda mugun dukar iyaye saboda aikato kanana, laifi kamar sata
ko kasa mikawo mahifisn agogo idan
ya yi latin zuwa wurin aiki "wata hanyar horon da suka fi yin amfani da ita
shine hanyar daure hanyen yara da igiya sanan a arika nana masu bawon ayaba
ko takaru da aka sa a wuta inji rohoton jarida
Jaridar monitor ta karya rohoton cewa ana yiwa yaran mata fyade musamman mata
masu shekaru 3 da haihuwa. A yan kwanakin nan gwamnatin Uganda ta kara yawan
shekaran baiwa yarinya ikon yakenwa
kanta kuduri daga shekaru 15 zuwa 18. Don a kare yara mata, alumma Uganda da
abinda yadamu su suna kura ga gwamnati ta bincika batun muzgunawa mata. " Babbar
matsala daya ba'a dauki battu
matsala da za'a shawo kanta ba" Jaridar monitor ta bayyana a shirinta "Baya
ga kungiyoyi masu zaman
kansu gwamnati bata sanya ko kwabo ba a fainin nazari ko taron karowa juna sani
donim a sanni saniyan abind ke faruwa tare da karfin gwiwar shawo kan matsalar.
Africanews
Bayanai Masu Amfani Dankali Mai Ban Mamaki 45secs
Kimanin watani biyu da suka gabata mun baku rohoton warni dankali mai albarka
wanda ya sanya
yanayin rayuwar mutanen kayukan kudu masu gabacin kamaru, muka ce an fara amfani
da dankalin a gandun dajin obudu da ke kundacin najeriya yanzu zamu iya shaida
maku cewan an sake gano wanan
irin dankalin a Amurika.
Ana kiranj dankali mai yabanya an bayana cewar wanan dankalin zai iya kara yawan
kudin da manoma
ke samu da dolla 200 a kowace hecta, kuma zaa iya amfani da shi domin ci da
kuma a masanatu inda za yi amfani da shi don samar da sinadarin Etanol wanda
ake hada magunguna da shi
Environmental News Network 13
13 Page 14 15
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
14
CHANGE
Yiwuwar Karo Da Wata Hilitta Daga Sama. 52secs. Yi tanane a kai
a lokacin da kake barci a you wata halitta ta fado daga sama wadda tayi girm
babban
tsauni kaman wanda ke a jihar plateau, zai iya kauce hanya ya fado kasa zuwa
duniyarmu ya yiwu ka yi
tunenem cewa wanan ba zai yiwu ba, Amma uwaui mutanen da suka yi imanin hakan
zai alku sun han zai fever kum sun yi tari a wan yali a hamilar cornell da ke
itchacal a Amurica a wajen taron kasa da
kasa a kan wati halitta mai haske da ka fado daga sama.
Masu nazarin duniyan wata suna tunane cewar kashi 10 / 100 na halittun da ke
sama ne aka sami ilmin
sanisu kum akwai yiwuan wan sahi na iya fadowa zuwa dunyarmu. National Geographic
News.
Gandun Dajin Kasar Ghana 26sec
Akwai gandun dazuzuka 280 a kasar Ghana wanda ke kushe da ken kabko 190,
amma an gama sarewa da da sayar da guda 50. Dokar Ghan ta bada 1zinim a sare
cubic mita milyan 1.4 na itace katako a
kowace shera.
Alummar Ghana suna amfani da cubi mita 4 na itace ga kowane mutun a shekara,
yayinda a Najeriya
mutum guda ke amfani da cubi mita 1.5 a shekara. George Ameyibo/ Obasi Ogbonnaya
Ko Kasan Yawan Gubartaciyan Iskar Da Motaka Ke Samarwa? 31secs
Shin kasan yawan iska mai guba da matarika ke samarwa? Bari mu baka misali.
Idan kana tuka moto da aka samar da ita a nahiyar turai wadda ke amfani da lita
man teriguda a kilomita 13 to idan ka yi
tafiyar kilomita 16,000 iska mai guba da motar zatta samar zata kai ninki uku
na nauyin motraka! Yi
tunane a kan wanan.
An Sami Karin Yawan Mutanen Da Ke Gudun
Hijira Saboda LacewarMuhalli, Maimakon Dalilin Ringingimun Yaki 43secs
Yan gudun hijira da ke gudu saboda matsololi muhalli na fari, karancin abinci,
sare itatuwa da zaizayawar kasa, kimanim mutane milyan 25 ne suka yi fudess
nigeria a bar wanda ya samr da kashi 58 na yan
gudun hijira da ake da su, wanan ya wuce yawan yan gudun hijira da ake dasu
dalilin yaki.
"Kowa yana sane da matsalolin mushalli da na zafaffar da duniya ke yi da sare
itatuwa a daya hanun ga matsalolin Zamantakewar rayuwa da samuwar kananan garuruwa
kamar yadda rohoton kungiyar Red
Corss a Kan Balai a Shekarar 1999, wanda kan yi nazarin halin da alumma ke ciki
"Amma idan wadana matsaloli biyu suka hadu dole ne a samu sabon balai".
WWF 14
14 Page 15
Radio
Vol II No 9 August 1999 [Hausa]
15
CHANGE
Kalmomin Da Aka Yi Amfani Da Su
APL : Nakiyoyin da ake biznawa a kasa
BBF : Gidauniyar Brothers Brother
CBD : Yarjejeniya a kan rayuwar hallitu
EA : Kungiyar alummar turai
IPCC : Majalisar kula da sauyin yanaji
NAJA : Hukumar kula da sararin samrriya da jirgen sama
OAU : Kungiyar hada kan kasashin Africa
UN : Majalisar dinkin duniya
UNDP : Hukumar gudanar da aiyukan ci gaba ta mojalisar dinkin duniya
UNESCO : Hukamar kula da ilimi kimiyya da al'adu ta majalisar dinkin
duniya
USAID : Cibiyar samar da aiyukan ci gaba ta Amurika
USIA : Cibiyar samar da bayannai ta Amurika 15
© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw