Document Body Page Navigation Panel
An sami sabuwar Tashar Rediyon C D Yanzu a Africa.
Hanyar Samun Labarai Sabuwa: Sabbin Dokokin Aiyukan Internet. 1min 34
secs. 7
Sabuwar Tashar Rediyo dake kan Hanya.
TATTALIN ARZIKI.
Tashar Tauraron Dan Adam zai iya samar da dala biliyan 50 a shekara ta 2000.
1min. 38 secs 7
Binciken sararin samaniya, kwalliya ta fara biya kudin sabulu
ILMI.
Kungiyar UNESCO ta kammala babban tarihin Afrika 2mins 37sec. 10 Aiyukan
shekaru 35 na sake ganowa da kuma tsarawa kan gudunmawar
Afrika ga harkokin tarihin Duniya.
Sabon bincike ya baiyana ainihin dalilan dake hana mutum yin karatu.
2min. 22sec. 4
Yaran da ba sa iya karatu saboda lalura, mai yiwuwa su sami
ilmi tare da magani.
KIWON LAFIYA.
Yiwa Mata kaciya har yanzu ruwan dare ne a Najeriya. 3min. 48secs. 3 Sabon
nazarin da akayi ya tabbatar har yanzu anayiwa mata
kaciya a sassa daban-daban a Najeriya.
Kungiyara Najeriya ta sami kyauta ta Duniya kan ilmin jima'i. 1min. 34
secs. 6 Bayan kwashe shekaru masu yawa tana aiki kan ilmantar da jama'a
game da jima'i a Najeriya, yanzu ta sami kyauta.
Cutar Kanjamau Har Yanzu Babbar Matsala Ce, Ganin an 2min. 36secs. 5
Kusa a Ranarakula da Cutar ta Duniya
Koda shike Cutar Kanjamau babbar matsala ce a Duniya, kowani
uku daga cikin hudu na masu cutar sun fito ne daga Afrika.
TSARIN BIRANE
Gyaran Gari da akeyi a Khartoum ya sanya dubban mutane sun rasa gidaje. 2
min 14 secs. 9
Birnin Khartoum na shan suka saboda ragayyara iyalai da dama.
MATA
Hukumar samar da canji CFC ta shirya wani Silma kan Matan da mazan su suka
mutu. 2mins. 15secs 6
Irin matsalolin da Matan da mazajen su suka mutu ke fuskanta a Najeriya.
1 1
1 Page 2 3
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Yanayin Muhalli GADUN YANAYI
Ita tuwan da suak shekara dubu cikin littafi guda. 1min 33 secs. 5 Itacen
da yafi tsayi a duniya har yanzu yana raye.
ILMI
Yankin Neja Delta: Ana kara samun wayewar kai kan muhalli. 2mins 50 secs.
8 Kungiyar Rawya duniya tana aiki domin ilmantar da jama'a kan
yanayin muhalli a yankunan Neja Delta.
SHARA
Sabuwar hanyar kula da shara a kasar Argentina. 2 mins 7secs. 4 Wani
gagaramin Birni a Argentina ya samo sabuwar dabarar sarrafa shara.
DABBOBIN DAWA:
Sabuwar Dabara ta kara karfafa ilmin muhalli a kasar Ghana. 2 min 14sec.
9 An gano wau irin Nau'in Kwanta rafi da ake zato sun bace.
Wani Alkali a Amurka ya dakatar da sare itatuwan katako domin kare kifaye.
51 sec. 13
Wata kotun tarayyaz Amurka ta yanke shawarar kyautata wasu irin kifaye.
KIMIYYA:
Wata sabuwar hanya ta gano cewar babu Teku a Duniyar Mars. 1 min 3sec. 14
Wata kila ba a taba samun teku ba a Duniyar Mars.
KASUWANCI.
Sabuwar kawance domin yaki da bude kafofin kasuwanci. 1min 3sec. 14 Yaki
da abokin gaba.
Sashin Yara
Dalilin da yasa 'ya'yan Chafali ke da hawaye a idanun su 4mins 49sec. 11 Tatsuniyar
kabilar Zulu tayi bayani kan dalilin da yasa 'ya'yan Chafali ke da
hawaye a fuskar su.
Tsawon yaushe ne mutum zai rayu bayan kasa ta sare shi 1 min 50sec. 11
Yaya dafin dake cikin sarar maciji kasa?
Kofar Ruwa 10min 55secs. 12 Kurege na zato yafi kowa wayo, sai dai
kunkuru ;ya nuna masa ya fi shi.
Karin Maganar Muhalli. 51secs 14 Ina dan Adam ke zuwa bayan ya bar
duniya?
Sau Nawa Kudan Zuba Ke Yin Zuma A Shekara? 1min 28sec. 14 Sau nawa
itatuwa ke yin furanni a shekara?
2 2
2 Page 3 4
Vol II No. 13 December 1999 (Hausa) CHANGE Radio
Labaru
Har Yanzu A Nayiwa Mata Kaciya A A Najeriya. 3 Mins 48 Sec. Har yanzu ana
gudanar da al'adar nan ta yiwa Meta Kaciya a wurare da dama a Najeria. Wannan
kuwa an
gano ne cikin biciken da aka gudanar a sassa daban daban, wanda kuma gidan Rediyon
Najeriya ya gabatar cikin rahoton sa a watan Nuwamba, inda yace Gwammatin jihar
Ogun ta haramta yiwa meta kaciya. Kowani
daya cikin uku na ŭan Najeriya da shekarun su ya kai 18 yayi naám kan cewar
zai cigaba da yiwa ŭar sa
kaciya. Irin wadan nan mutanen sunfi yawa a sashin Yammacin Najeriya inda aka
sami fiye da kashi 50 cikin dari a binciken, wadanda suka furta haken. Binciken
da wani Kamfani dake Lagos ya gudanar kwanan nan
watau RMS ya nuna cewar za a cigaba da wannan aládar har zuwa karni na gaba
musamman a yammacin Kasar.
Kamfanin an RMS ya zanta da mutane dubu 5 wadanda shekarun su ya kama daga
18 cikin wasu manyan Kabilu Kasar 12 jihohi 36. Haka kuma ganawar anyi ta ne
tsakanin mazauna birane da kauyuka kuma yawan
maza da mata da aka tattauna da sun daidai ne. Sakamakon ganawar ya nuna kashi
70 cikin dari a yammacin Najeriya sunce anayiwa mata kaciya. A Lagos kashi 50
cikin dari, a Gabashin Najeriya Kashi arba 'in cikin
dari yayinda a Arewacin Najeriya Kashi 20 cikin dari.
Anfi gano samfurin sosai idan aka bi tsakanin jihohi dakuma Kaliba, inda ake
da Kashi 90 cikin dari na yiwa mata kaciya a jihohin Edo da Ondo da Bayelsa,
dakuma kashi 80 cikin dari tsakanin kabilun Urhobo da Ijaw
dakuma Edos. Kimanin kashi daya bisa hudu na wadanda aka gana dasu a duk fadin
kasar sunce anyi musa kaciya. Daga yankuna kuwa mutum uku daga cikin hudu da
aka yiwa tambaya a yammacin Najeriya sunce
anyi musa kaciya, sashin gabashi dakuma Lagos mace daya daga cikin uku tace
anyi mata kaciya yayinda a Arewacin Najeriya daya ne daga cikin mata goma ke
cewa anyi mata kaciya.
Da take bayayi a lokacin ganawar Ms Margit Cleveland na kamfanin RMS tace
dalilin dali da mutanen ke bayarwa sun sha bamban, saidai kusan dukkan su sunce
sunayi ne saboda al 'ada tayiwa yara maza da mata
kaciya a Najeriya. Wasu dalilan shine kaciyar tana hawa mata jaraba kuma tana
taimaka musu yayinda suka zo haihuwa. Amma Ms Cleveland tace kaciya bata hana
jaraba ga mata, domin akasarin mata karuwai duk
anlyi musu kaciyar.
Kamfanin an RMS bai gano ba daga mutanen da ya gana dasu kan a binda suke daukar
yiwa Meta kaciya a
Najeriya. Koda yake binciken shine mafi sahihanci yazuwa yanzu a Najeriya Ms.
Cleveland tace zata so gno wasu dalilan dake sanya akeyiwa Mata kaciya nan gaba.
Wadanda zasu hada da yiwa kananan kabilu intabiu wadanda ba ayiwa ba a wannan
lokaci tare da ganawa da Meta kadai, tare da hadawa da wasu kasashen kamar su
Camerou da Ghana ta yadda za a gano ainihin dalilan
dake sanyawa akeyiwa Meta kaciya tare da same sahihan dabaru da hanyoyin da
za abi wajen hanawa. In har ba ayi kokarin kawo karshen wannan al 'ada ba to
kuwa zai cigaba ne har zuwa 'ya 'ya da jikoki masu zuwa
nan gaba. Kuma ba za iya magance shi ba. Domin kuwa ba al 'ada bace da zata
mutu da sauki inji Cleveland. RMS.
3 3
3 Page 4 5
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Sabubuwar Dabarar Sarrafa Da Aka Fara A Kasar Argentina 2 mins 7secs Birnin
Salta dake kasar Argentina dake da yawan mutane dubu dari biyar ya shiga sahun
sauran manyan
biranen duniya wadanda suke daukar sabbin dabarun zamani domin shawo kan shara.
Kwanan nan ne birnin dake samar da shara Tan metan da hamsin ya bullo da wani
shiri mai karfi domin sarrafa sharar nan da shekaru 10masu zuwa. Babban abindake
cikin shirin shine na maida dibar shara na kasuwanci
inda ŭan kasuwa zusu rika tafiyar da harkar kwasa da zubarwa. Za Agudanar da
shirin ne bisa mataki-mataki har biyar wanda za afara da wayarwa da jama 'a
kai na tsawon shekara daya, tare da ilmantar da jama 'a kan
wannan sabuwar dabara. Kowane za a gudanar ne tsakanin shekara daya zuwa shekara
uku.
Sauran matakan sun hada da hada da ahekaru biyu, wanda a lokacin kamfanonin
'yan kasuwa zusu fara kwasar sharar kowace rana bayan da aka fara shirin kx
gwaji. Sauran ragowar shekarun biya zasu kasance
na tafiyar da irin ribar da aka samu kan shirin tare da tabbar da ganin akalla
rabin birnin mazaunan sa na tara
sharar su ta yadda zusu bambance tsakanin shara irin daban-daban misali shara
irin kwalabe da karafa da takardu da robobi da sauran su ta yadda za asake sarrafa
su domi yin amfani.
A rukinin karshe, wanda zai hada da shekaru na hudu da na biyar zai kasance
kashi dari domin tara sharar da za asake sararafawa ne.
Wani kwarare kan harkar sharar Mr. LUcas Seghezzo, wanda yana cikin wannan shirin
na birnin Salta yace birnin ya kuduri aniyar samun nasarar shirin.
Mr. Seghezze yace za akuma sa ido kan yadda za arika tafiyar da shirin baki
daya domin tabbatar da sahihanci da nagarta dakuma bada kwazo.
UWEP.
Sabon Bincike Ya Ganoni Ainihin Dalilin Dake Hana Iya kara Tu 2mins.
22secs. Sabon bincike ya nuna cewarwasu jijiyoyi sune ke sanya mutum ya
kasa karatu in har basa aiki yadda yakamata.
Mutane basa iya yin karatu koda kuwa suna da sha'awa dakuma damar yin karatun.
In har wannan sakamakon gaskiya ne to kuwa zai tabatar d cewar mutm na cikn
kasadar rashinyin karatu inji wani kwarare kn tatalin
arziki. Kafin wannan lokaci masana halayyar jama'a suna zato cutar rashin iya
karatu matsala ce ta daban.
Sunyi imani cewar masu fama da irin wannan cutar suna faane da rashini ya fahimta
abinda ake sara zasu karanta. Wannan zato kuwa ya tabbata ba gaskiya ba domin
irin wadan nan mutane basa samun matsala wajen
yin mu'amala da baki. Sabuwar hanvar gano irin wanman cuta yanzu ta nuna cewar
rashin iya karatun na faruwa ne saboda rashin aiki yadda yakamata na wasu jijiyoyi
dake kaiwa kwalwa. Wanna rashin aikin na
kawo saibi wajen aikin karatu cikin hanzari, wanda ita kwalwa ke karba daga
abinda idanu ke gani ko kunne
ke ji. Inji John Gabriele da Torke. Klingberg na Jami'ar Stanford dake Amurka
ne suka bull oda wannan sabuwar dabara ta cusawa irin na maganadisu (DTI).
Gano ita wanna cutar rashin iya karatu an gano ta ne ganin masu fama da ita
suna fushantar wahaloli wajen ji. An gano cewar su irin wadan nan nutane basa
iya karanta layukan rubutu wadanda suke da harufa kusan iri
guda musamman in har suna bin juna ne cikin hanzari. Dr. Gabriele da Dr. Klingberg
sunce binciken nasu ya gano iya karatu na tare da tafiyar sauti cikin jijiyoyin
dake zuwa kwalwa ne. DTI wata hanya ce ta auna motsin
ruwan dake cikin jijiyoyin jikin dan adam. Ta yin nazari kan irin saurin da
ruwan keyi cikin jijiyoyi har zuwa kwakwalwa masana kimiyar sun gano cewar akwai
ingantatun hanyoyin tafiyar ruwan sosai a jikin mutanen da
basa fama da irin cutar hana iya karatun. The Economist
4 4
4 Page 5 6
Vol II No. 13 December 1999 (Hausa) CHANGE Radio
Cutar Kanjamu Babbar Matsalar Kuniya Ganin An Doso Ranar Yaki Da Cutar Na Karatowa.
2mins 36sec.
Afrika ce ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar
kanjamau dakuma wadanda suke fama da cutar. Wanna kuwa na kunshe ne cikin rahoton
da aka bayar kwanan nan daga majalisar Dinkin
duniya. Gaga cikin mutane miliyan 34 dake fama da cutar ta HIV/ AIDS a duniya
kasashen dake yankin Afrika
kadai dake fama da cutar sunkai miliyan 23. Cikin wata kasidar da majalisar
dinkin duniyar ta buga kafin ranar yaki da cutar daya ga watan Disamba 1999,
ta nuna cewar Afrika ce ke kan gaba da wadanlda ke fama de
cutar. Kusan kowani mutumin da ya mutu a sanadiyar cutar. Kusan kowani mutumin
da ya mutu a sanadiyar cutar da ake samu daga Mata a shekarar 1998 wadanda suka
kamu da cutar ne. Daga cikin yara dubu dari
shida da aka haifa da cutar ta kanjamau dubu dari biyar yaran Afrika ne kuma
sune kashi 80 cikin dari na yaran
dake mutuwa a sakamakon cutar a duniya. Kamar yadda kasidar da akayiwa lakani
matakin majalisar dinkin duniya kan cutar kanjamau Afrika ce ke da Mata mafiyawa
da suka kamu da cutar a duniya..
Koda shike Afrika itace cutar tafi yin kamari, duk da haka cutar batada iyaka
tsakani nahiyoyi ko tsakanin kabila ko mukami. A yanzu haka akwai miliyoyin
mutane dake fama da cutar a sassa daban na duniya. Wadanda
suka hada ha mutane miliyan 7 a nahiyar Asia, kimanin miliyan biyu a Latin Amurka
da miliyan daya da Arewacin Amurka da wasu dubban daruruwan a yankin Caribean
da Turai da Gabas ta Tsakiya da Ausralia da New
Zealand dakuma tsibiran Pacific. Babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi
Anan yace tilas ne mu fahimtar da jama'a cewar wannan cutar babban baraz ace
kuma tilas a hada karfi da karfe waje guda domin
yaki da ita. Tilas ne duniya ta daura damara domin yaki da wanna mugunyar cutar
da duniya baki daya.
Majalisar dinkin duniya tana saran duniya zata kuduri aniyar yaki da cutar a
wannan ranar d aka kebe. Gaga cikin hanyoyin da ake sran bi domin yaki da cutar
sun hada da kudurin shugabanin kasashe ta fuskar siyasa, da
aiyukan hadin gwiwa tsakanin wadanda suke da sha'awa domin karya alkadarin cutar,
tare da kara kudaden da ake bayarwa domin gudanar da bincike da samar da allurar
da zata karya lagon cutar tare da kara yawan
aiyukan da suka shafi matasa. HIV/ AIDS MORE THAN A HEALTH CRISIS
Bishiyo Yin Shekara Dubu A Littafi Guda 1min. 33sec. Rannar 24 ga watan
Nuwamba a London hukumar kare gandun daji ta duniya WWF zata kaddamar da
gagarumin yekuwa kan wani littafi dake kunshe da wasu bishiyoyi da suka dade
a duniya, wadanda ake kyautata zato sun shekara dubu a duniya, sun kuma kunshi
iri daban-daban har ashirin da biyar. Haka kuma littafin ya
kunshi wasu ;sabbin tsirrai da aka gano cikin wannan zamani. Littafin da ake
kira Littafin karni na bishiyoyi, tsoffin bishiyoyin wani madaukin hoto mai
suna Edward Perkar da Anna Lewing ne suka hada shi. Shi Parker yayi
yawi a wurare dama a duniya na tsawon shekaru yana daukar hotunan bishiyoyi
a dazuzzuka.
Bayanan tsoffin iyatuwa, da ya kunshi irin bishiyoyi daban-daban a duniya dakuma
irin bayanan su, da al'adun
su da tarihin su dakuma yanayin su, ciki harda irin girman su da tsayi da shedaru
ciki harda bishiyar da tafi tsufa a duniya.. Akwai ma bishiyoyin da aka dauko
daga yankunan dazuzzukan yankin nan mai zafi na Amazon da
yankunan arid dake hamadar Namib. Dd' yake baiyana tsoffin bishiyoyi da cewa
abin mamaki ne kuma littafi mai kyau, wani mai harsashe yace ya hade da ;wasu
hotun mafiya kyanu da Mr. Parker ya dauka ana iya sautun
littafin daga Sonia Pugh dake Collins da masu buga litattafai na Brown dake
kasar Biritaniya (Tel+ 44171924
2575) WWF.
5 5
5 Page 6 7
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Wata Kungiya A Najeriya Ta Sami Kyau Ta Ta Duniya: Kan Il min Jimai 1min. 34sec.
Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira kungiyar sha yanzu magani yanzu
kan kiwon lafiya (AHI) wanda ta
shahara kan aiyukan ilmantar da jama'a game da jima't ta sami kyautar WAS ta
shekarar 1999. Kyautar kungiyar kula lda ilmin jima'i ta duniya WAS ce ta baiwa
kungiyar a Hong Kong a taron ta na 14 da akayi cikin
watan Agusta. An zabi kungiyar ta Najeriya ne bisa shawarar da kwamitin da
kungiyar ta WAS ta kafa yayi nazarin kungiyoyin da aka gabatar da sunayen su.
Da yake gabatar da kyautar Dr. Eli Coleman shugaban kungiyar ya baiyana muhimmancin
ta Ana bada kyautar ne ga kungiyar da tayi fice ainun wajen ilmantar da abubuwan
da suka shafi jima'i a kasar su ta hanyar shirye-shirye
masu gamsarwa, kuma ana bada kyautar ne da nufin karfafa gwiwa ga sauran kuingiyoyi
na duniya domin suma su bada himma. Kyautar ta zo a matsayin ba zato ga kungiyar
ta Najeriya, wanda ta taka muhimmiyar
rawa wajen shirya ka'idoji kan sahihan aiyukan ilmi kan jima'i a Nairiya. Ba
ma saran samun wannan kyautar
inji wani jami'in kungiyar Dr. Uwem Esiet yayinda yake karbar kyautar a madadin
kungiyar. Yace kyautar zata karfafawa kungiyar gwiwa wajen cigaba da aiyukan
kara kyautata rayuwar matasa ta hanyar gudanar da ilmin
jima'i a Najeriya. Growing Up
Hukumar Kyautata Muhalli CFC Ta Kaddamar Da Silma Kan Matan Da Mazan Su
Suka Mutu 2mins 15sec.
Za a kaddamar da wani hoton silma na tsawon mintoci 30 kan irin halin da
Matqan da mazan su ka mutu suke ciki a Najeriya a wau sassa uku cikin wannan
watan. Silman da adayiwa lakanin MUTUWA KA RABA, an
dauko shine a sashin gabashin Nageriya inda nan ne matsalar tafi kamari kana
taki jin magani. Za a kaddamar da silman ne a lagos, da Enugu dakuma Patakwal
tsakanin 29 ga watan Nuwamba zuwa 8 ga watan Desamba.
Hukumar ta CFC ta shirya silman ne a bara domin baaiyana irin wannan hali ta
al'adaa.
Silman yayi tsokaci kan irin tattaunawar da akayi da irin wadan nan Matan da
suka rasa mazajen su, da wakilan kungiyaar irin wadan nan Matan da sauran jama'a,
wadanda ke taimakawa wajen sauwakawa irin wadan nan
Matan wahalolon da suke fuskan ta. Da yawa daga cikin su, sun sami sukunin baiyana
irin abinda ke damun su a zuciya da irin halin da suke ciki da bakar wahalar
da suke sha na tsawon shekaru. Lallai ya tabo irin
sukurkucewar da burin su yayi a rayuwar su. Mutuwa ka rabaA ya tabo irin yadda
al'adu suka jefa irin wadan nan Mata cikin tasku.
Wadanda suka hada da zaman takaba na lokaci mai tsawo, da sa Matan su aske
kan su dakuma sanya su yin kuka mai tsanani ta yadda zasu wanke kan su daga
zargin ko sune suka kashe mazajen nasu tare da yin wasu
tsatsube-tsatsube domin kauda fatalwar Mazajen su da suka mutu. CFC ta shirya
silman ne tare da taimakon hukumat talabijin mai kula da harkokin yanayi dake
kasar Biritaniya (TVE), wanda ke samun kudaden sa daga
kungiyar tarayyar Turai. OBASI OGBONNAYA.
6 6
6 Page 7 8
Vol II No. 13 December 1999 (Hausa) CHANGE Radio
Tauraron Dan Adam Samar Da Dala Biliyan 50 A Shekara Ta 2000 1min 38sec.
Kusan shekaru arba'in da akayi ana bincike kan sararin samniya kwalliya
ta fara biyan kudin sabulu ta fuskan samr da makudan kudi da fasaha ga kasasshen
da suka fara tafiyar da sikin na turai da Amurka. Kimanin dalar
biliyan 36 aka samu ta fuskar kaswuwanci kan tasoshn tauraron dan adam da wasu
sauran taurarin na dan
adam a bara. Haka kuma an sami karuwa kan harkokin fasaha wanda ake saran kasashe
masu tasowa suma zasu amfana. Wannaan kuwa na kunshe ne cikin taro na uku kan
biciken sararin samaniya da aiki da abubuwan
dake sararin samaniya (UNISP) da akayi a Vienna cikin watan Yuli. Kamar yadda
taron na UNISP 111 yaayi bayani an kiyasta samun dala biliyan 50 cikin shekara
ta 2000. Waannaan ya nuna karuwa kan abinda za
asaamu na aiyukaan binciken sararin kamr yadda yaake ga taron na Vienna kan
yadda dan adam zai aamfana
daga sararin samaniyya.
Daga cikin batutuwan da aka zartar a taron na Vienna sun hada da shirin kare
yanayin sararin samaniya tare da albarkatun dake akwai domin amfanin tsaro da
zamantakewar bil-adama. Shirin an ruwaito cigaba ne kan
shirye-shiryen da akayi tunda farko a tarukaan da akayi ashekarar 1968 dakuma
1982. Tattaunawar ta Vienna
ta hada da taimakawa kaan harkokin fasaha da ilmi domin kasashe masu tasowa
suma su ci gajiyar fasahar. Gajiyar sun hada ta fannin aikin gonayanayin muhalli
tare da kare aukuwar haddurar kasa. Haka kuma samun
aiki da na 'urar Internet ta hanyar tauraron dan adam a wuraren da ba a dasu
domin bunkasa harkokin masana 'antu.
Development Update
Hanyar Samun Laa Barai: Bisa Dokokin Internet 1min. 34secs Yanzu kana
iya kama shirye-shiryen gidajen rediyo daga ko ina a duniya ta hanya yin amfani
da na 'urar
kkummputa. Wani babban kamfani dake Amurka daake samar da Internet ta hanyar
Biznes On line. Com, ne ya sanya shirin ya samu ta hanyar kaddamar dda irin
wannaan tashar rediyon na farko a A duniya a kasar
Amurka. Ana iya samun ttashar yanzu ta hanyar (htt:// www. the publicradiostation.
com) wanda ke gabatar da
shirye-shirye da dama a duk fadin Amurka da sauran duniya. Sun hada da jazz,
da rahoto kan kayayyaki, da wakoki da shirin Mata da yanaayi da labarai da sharfi.
Sashin aiyukan web ya maida hankali ne kan masu
kanana da matsakaitan masana 'antu dake Amurka.
Da yin aiki da na 'urar internet dokokin suna canjawa daga tasha zuwa tasha
inji Mr. E Munro babban jami 'in
BiznesOnline, yace yanzu haka muna aiki da tasoshin rediyo da dama da talabijin
da kamfanonin jaridu domin taimaka musu ta yin aiki da internet kamar fadada
kafofin su. Hakka kuma Munro yace anyi ttsare-tsaren
shirruka ta yadda mai sauraro zai san lokacin shirin da yake bukata ya saurara.
Akwai kuma karin karfafa gwiwa,. In mai sauraro ya rasa jin wani shiri yana
iya samu ta hanyar nema a rumbun adana shirruka.
Kusan dukkan kafofin yada labarai irin su jarida rediyo da talabijin suna amfani
da internet yanzu domin fadada
kafofin su. Ta hanyar taba na úrar za ka kalli shirye-shiryen da kake bukata
ta talabijin da karanta labarai ta jarida ko ka bude tashar rediyo domin jin
shirin. Wannan tashar ita ta farko da za a iya samun ta kan layi.
PR NEWSWIRE.
7 7
7 Page 8 9
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Sharhi.
Ana Samin Karuwar Kula Da Muhallia Yankin Neja Delta: 2mins 50sec. Wata
kungiya a Najeriya mai zaman kanta dake kare muhalli (LWNF) a karon farko ttana
baiwa mazauna
karkara damar baiyana ra 'ayin su a yankin Neja Delta ta wasu aiyuka. Aiyukaan
sun hada da shirin gidaan rediyo kaan muhalli da tattaunawa a harshen turancin
pijin da cikakken turanci da mazauna karkara, da wasanin
kwaikwayo kan irin halin rayuwar jama ' a ta yau da kullum dakuma hotunan da
ake likawa kan yadda jams 'a
zasuyi mu ' amala cikin yanayiin da suke. Wadanda suke cin moriyar shirin sun
hada da al 'umomindake zaune a Akipelai, da oloibiri da Biseni da ya kunshi
kauyuka takwas.
Aiyukan da aka fara a watan Nuwaambar 1998 ya sami gagrumin karbuwa ga jama
'a . Ba-saraken Akipeloi ya gamsu bayan ganin shirin wasan kwaikwayo, wanda
shine irin sa na farko da aka tabayi a kauyeen. A
karshen wasan kwaikwayo, wanda shine irin sa na farko da aka tabayi a kauyen.
A karshen wasan anji yana cewa 'lallaai yanzu ne naga kauye na ta cikin madubi
'. Kungiyar ta kuma kara da taimakawa kauyawan
wajen kafa kungiyoyin wasan kwaikwayo nasu da ake kira 'Odion ioobebh'kusan
dukkaan kauyuka uku dake ankin suna da kungiyoyin wasan kwaikwayo nasu na kansu.
Wasu ashirruka biya na rediyo mai warka 13 da akayiwa taken lokaci yayi me
ke faruwa ana gudanar dasu a tasoshin rediyoon jihohn Bayelsa, da Rivers dakuma
Cross River da jihar Delta. Da yaake baiyana ra 'ayin
sa bayan sauraron shirin na rediyo Cif Amakime Ogu basaraken Amananowei dake
Biseni yace: 'Wannan shine abu mafi muhimmaaci da ya faru da mu, shirin ba kawai
yanuna mana haaske ba ya kara fiddo da
matsalolin da al 'umomin mu ke fuskan ta ga duniya'. Wata budurwa a Akipelai
tace hirar na rediyo shine na
farko da wata Mace akauyukan Bayelsa suka sami damar fadar ra 'ayiin su a baiyane.
' Shugaban hukumar kare muhalli da tsare-tsare ta jihar Bayelsa Mr. Aureol D.
Vainana yace hukumar sa ta yaba bisa amfani da
rediyo da akeyi na wayarwa da jama 'a kai kan harkkokin muhalli. Ta hanyar
shirukan rediyo kungiyar zata iya hada al 'umomi kan yadda zasu kawo canji game
da yanayin muhalli. Yayi alkawarin cewar rediyon jihar
Bayelsa zai rungum shirin da zarar ya fara aiki. Koda shike shirin ya kara wayarwa
da jama 'ar yankin kai
kuma ya sanu karbuwa har yanzu ba za afayyace yadda aka sa gaba ba. Living
Earth/ Nig. Foundation
Habasha Ta Kaddamar Da Rediyo Irin Na Zamani Domin Afrika Da Gabas Ta Tsakiya
3min 9sec
kashen Afrika ta yamma zasu fara sauraron shirin gidan rediyo rangadadau
daga kko ina cikin yankin kafin shekara ta 2000 ta hanyar amfani da rediyo na
musamman da aka yi domin karbar shirye-shirye ta tauraron
dan adam. Wannan kuwa ta hanyar kamfanin rediyo mai aiki da dijital da aka kafa
domin saamar da shirrukan rediyo bai daya a likaci guda. Kamfanin cikin watan
jiya ya kaddamar da aiyukan rediyo irin sa na farko dake
amfani ds fasahar zamani, domin tabbatar da ingancin sauti a yankunan karkara
inda ba asamu kama tasoshine rediyo a nahiyar Afrika, inda za afara da kasasheen
Najeriya da Ghana da Senegal da Afrrika ta kudu, da
Keenya da Cote D 'Ivoire da Masar dakuma Morocco. Ana karfafa shirin ne ta dakin
wastsa labarai dake
London da Washington zuwa Afrika ta hanyar amfani da karfin hasken rana da aka
kaddamar a farkon wannan shekara. Shi wannaan rediyoon da ake kira AfriStar
zai samar da labarai ta hanyoyi 25 da wake-wake
da nishadantarwa da ilmantarwa a yankin da yakai kilomita miliyan 42 murabba
'i a Afrika da Gabas ta tsakiya. Wannan wata rana ce mai cike da tarihi a fannin
rediyo inji shuggaban kamfanin na World space Mr.
Noah Samara a wajen kaddaamar da tsarin na shekaru 1l0. A karon farko ya yaankunan
da ada basa samun
sauraron shirin rediyon duniya, ta dijittal. Shirin rediyon zai kai ga masu
sauraro miliyan dubu ddaya a duniya.
8 8
8 Page 9 10
Vol II No. 13 December 1999 (Hausa) CHANGE Radio
Ana bukatar akwati rediyo na musamman da akayi m ai eriyaal kama tauraron
daan adam ta hasken rana kafin sauraron shirin na AfriStar. Kimanin akwatunan
rediyo dubu 30 ne kamfanonin rediyo na Hitachi, da JVC dda
panasonic da Sanyo suka kera nnan da Disamba kimain irin wadan nan rediyon dubu
130 ne za a kera a saidawa kasasheen Afrika. Koda shike za a kera miliyoyin
irin wadan nan rediyon domin saidawa mazauna
karkaran Afrika bisa dan takadirin farashi a matsayiin makamin cigaba. Daga
cikin aiyukan da kamfain keyi harda damar zaben shirye-shirye labaru daga tasoshin
rediyo na kasa dana duniya da shirye-shirye cikin
harsuna ciki harda turanci da faransanci, da larabci da Afrikaan. Akwai kuma
shirin da AfriStar keyi na kaddamar da tshar AmerStar danufin kaiwa ga dukkaan
bangrorin dake baya wajen samun ahirukan rediyio,
a akalyi. PRNNEWSWIRE.
Gano Wata Dabba Da Akayi A Ghana Ya Sanya An Tashi Tsaye Wajen Kare Muhalli
2min 14sec
Gano wata irin nau 'in barewa da akayi kwanan nan mai suna sitatunga ya
sanya an tashi tsaye wajen yekuwar kare muhalli a kasar Ghana. Ita wannan nau'in
barewar sititanga ana samun ta ne a bakin rafi da yankunan
dake da ruw ko koramai a gabashi dakuma kudancin afrika dakuma Najeriya. Ita
wannan dabba ta bace baki daya a kasashen Africa irin su Cote d'Ivoire da Saliyo
da Liberia da Senegal dakuma Gambia saboda farautar
su da akeyi. Kafin wannan lokaci ita wannan dabbar ana zato ta kare a Ghana
na. Amma kokarin da akayi na shata yankunan yawon dude ido a yankin gabashin
kasar ne yakai ga gano ita wannan nau'in barewar a
harshen tekun Avu. Wani jami'in yankin mai kula da yawon bude ido Mr. Frank
Kofigah ne ya gano ta.
Ma'aikatar kula da dabobin dawa, da cibiyar bincike kan hallitu (NCRE) da hukumar
kula da aiyukan yankuna masu ruwa ta Ghana sun baiyana sha'awar su ainun bisa
gano dabbar da akayi. Sititunga da dabba ce da ake
kauna a yankin na Avu. Yanzu basaraken yankin ya kafa dokar haramta farautar
ta. Maatuka dai muna kaare ita wannan dabba a yankunan mu dabobin zasu cigaba
da janyo hankalin masu yawon bude ido. Sauran
kokarin da akeyi sun hada da kare wuraren da dabbobin suke. Jami'in kula da
aiyuka a wurare masu ruwa na Ghana Mr. David Kpella yayi magana kan shirin da
akeyi na yekuwar kare muhalli ga jama'a bisa cewar z a
samu amfani fiye da yadda ake zato ta fuskar masu yawon bude ido fiye da yanka
irin wadan nan dabbobin domin nama . Baya ga haka ma'aikatar kula da dabbobin
dawa ta shirya sanya kungiyoyin kare muhalli na
duniya cikin shirin yekuwar kare muhalli. Edward Ameyibor.
Gyarar Fuskar Da Akeyiwa Birnin Khartoum Ya Sanya Dubban Mutane Sun Rasa
Gidajen Su 2mins 14sec.
Wani yunkurin da akeyi na yiwa birnin Khaurtoum gyarar fuska a kasar Sudan
ya jefa dubban jama'a cikin rashin matsuguni. Wani jigo a kungyar kare hakkin
dan adam ta Sudan, da ta kunshi 'yan jaridu da lauyoyi da
malaman makarantu tace kokarin da akeyi na kauda masu karamin karfi daga birnin
domin gina manyan hanyoyi da wuraren ajiye motoci ya tilastawa mutane dubu 40
rasa gidajen su. Wadan nan mutanen sun bi
sahun mutane miliyan uku da tuntuni suke zaune a bukkoki da unguwanin marasa
galihu dake kewayen birnin, inda suke zaman gudun hijira bayan da suka tserewa
yakin basasar kasar na tsawon shekaru 16.
9 9
9 Page 10 11
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Aikin wanda Gwamnatin Khartoum ke gudanarwa tun shekarar 1998 ya sanya an
ruguje gidaje akalla dubu metan duk na masu karamin karfi. Shugaban kungiyar
kare hakkin dan adan na Sudan Ghazi Suleiman yayi
kukan cewa wadanda aikun ya tayar sun koma wuraren dake nesa da wuraren samun
aiki, da makarantu dakuma wuraren ibada dana kiwon lafiya. Duk da haka Gwamnati
tace iyalan da abin ya shafa an basu filaye
a yankunan da suka zaba, yanzu haka suna more rayuwar su. Gyarar fuskar da akeyiwa
Khartoum ba yana
nufin fidda mutane daga gidajen su da karfin tsiya bane inji wani jami'in gwamnatin
Sudan.
Gwamnan birnin Khartaum Mazoub al Khalifa ya bada sanarwa kwanan nan cewar
Gwamnatin sa tana shirin gyaran birnin danufin inganta shi irin na zamani a
Afrika. Khartoum zai zama birni mafi kayatarwa a Afrika in
har shirin ya sami isasun kudi. Kamar yadda Gwamnan yace birnin da aka kafa
shekaru dari, danufin mazauna miliyan biyu yanzu akwai mutane sama da miliyan
6, ciki harda mutane miliyan uku da yakin basasa ya yagayyara
daga kudancin Sudan. Al Khalifa yace dubban iyalai ne za a tsugunar da su a
sabon wuri domin gina hanyoyi da wuraren ajiye motoci. A bara gwamnatin kasar
ta kirkiro da hukuma da ake kirar hukumar raya birnin
Khartoum (KSDA) domin sa ido kan gudanar da aikin gyarar fuskar, da biyan diya
ga iyalan da aikin ya tayar. IPS.
Kungiyar UNESCO Ta Kamammala Aikin Rubuta Tarihin Afrika 2 mins 37sec.
An buga rukunin karshe na babban litafin tarihin Afrika, wanda kuma yakawo
karshen aikin da kungiyar UNESCO ta fara tun shekarar 1964, domin tara bayanai
da aiyukan tarihin hahiyar Afrika tun zamanin jahiliya
har zuwa yau. An tafiyar da aikin ne da nufin gyara daukar da akeyi na cewar
aiyukan kimiyan Afrika basu da
tarihi kuma basa iya kawo cigaba in ba hada da wasu aiyuka na wajen Afrika ba
irin su aikin soja da na zamantakewa dakuma al'adu. Kowani daya daga cikin rukuni
takwas na litafin yayi magana kan irin gudunmawar
da Afrika ta bayar ga cigaban dan adam ciki harda aiyukan karafa, da aikin
gona dakuma dadadiyar fasahar nan ta kasar Masar. Haka kumakulitafin ya nuna
cewar mutum daya ke ke rayuwa daga cikin kowani mutum
hudu da aka saida a matsayin bayi yayinda ake ketare teku dasu zuwa aikin bauta.
Rukuni na takwas na littafin
an gabatar dashi ne a Trabulus cikin watan Mayu domin kawo karshen aikin na
tsawon shekaru 35.
Babban taron UNESCO na 1964 ne aka kaddamar da aikin littafin a Paris yayinda
aka tsaaida shawarar tattaunawa tsakanin al'adu daban-daban na duniya, domin
mutane ba baan-daban zasu bada ra'ayin su kan
fahimtar juna. Sabbin kasashen Afrika da suka sami mulkin kai dana Aasia na
bukatar tabbatar da al'adun su
ga duniya tare da gyara su dakuma asan su sosai. Kamar yadda kuddurin aikin
ya nuna Afrika na bukatar gyara kura-kuran dake akwai na na cewa Afrika bata
da wani abin tarihin azo agani. An gudanar da aikin ne
bisa matakai da dama. Na farkon shekaru biyar 1965 zuwa 1970 anyi amfani dasu
ne wajen bincike kan asalin tarihin Afrika. An samu ne kuwa daga kunnen ya girmi
kaka, da wuraren adana kayan tarihi da kayan
tarihi na karkashin kasa.
Rukuni na biyu 1970 zuwa 1980 aka bullo da dabarun rubuta tarihin, wanda ya
haka da kafa kwamiti mai karfi na kasa domin sa ido kan aikin baki daya. Kashi
daya bisa uku na wakilan kwamitin mai wakilai 39 na 'yan
Afrika ba ne, sun fito ne daga Amurka da Biritaniya, da Brazil dakuma Carebean.
Tsarin aikin ya bada shirya hotuna da sauran aiyukan zane-zane, an kuma nada
mawallafa fanoni daban-daban na aikin dakuma darekto
ga kowani rukuni. An fara buga littatafan ne a she karar 1980. An sami jinkiri
wajen kammala wanna matakin
saboda rashin kudi, biyowa bayan fitar Amurka da wasu kasashe daga cikin kungiyar
ta UNESCO a shekarar 1990.
10 10
10 Page 11 12
Vol II No. 13 December 1999 (Hausa) CHANGE Radio
Rukuni na takwas yayi magana kan Afrika na wanna zamani. Darektan wanna
rukuni kuwa wani shahararen masanin tarihin anan ne dake zaune a amurka dan
kasar Kenya Farfesa Ali Mazrui. Aiki ne mai muhimmanci
da yayi nazari ainun wanda ya kauda mulkin mallaka ya sake tsarin nahiyar tare
da kyautata matsalolin ta dakuma dangantakar ta da sauran kasashen duniya inji
Christopher Wondji wani babban jami'in aikin. Mr.
Wondji yace babban takaicin sa shine aikin bai hada da abubuwan da suka faru
a shekarun 1990 ba. The Courier
Sashin Yaraa
Tsawon Yaushe Zakar Rayu Bayan Kasa Ta Sare Ka? 1 min 50secs. Wannan babbar
tambaya ce mai wuyar amsawa saboda watakila ba zaka mutu ba in kasa ta sare
ka. Kasa
macijiya ce dake da dafi, in har tayi sara ta kan sanya dafin cikin jikin
wanda ta sara. Abinda kasa take kashewa sune tsuntsaye da wasu kananan dabbobi
irin su bera. Bata cika damuwa da mutane ba, domin haka
mu bama cikin abinda take ci. Kasa tana saran mutane ne in har suka tsorata
ta, kana tana kokarin kare kanta. Takan saka dafi kadan ne ko ba ba ta sakawa
in har ta sari mutum. In har dafi ya shiga cikin jikin ka ya kan
sanya mutun yayi rashin lafiya domin haka zai bukaci samun magani a asibiti.
Koda bata saka ma dafi ba ciwon
da sarar zaiyi ma na iya ruruwa saboda dattin da zai shiga na hakoran ta. Masana
kimiya da sukayi nazari kan macizai sunce akasarin mutanen dake mutuwa saboda
saran maciji suna mutuwa ne saboda tsoro bawai
saboda dafin ta ba. Akwai kasa iri-iri daya daga cikin su itace kasan Masar.
Wanda take son zama a shuri. In ta fusata sai ta daga jelar ta wanda ke da kugiya.
Wani lokutan kacizai sukanyi likimo kamar sun mutu. Amma
mutanen da su kasan maciji sosai suka san halayyar su basa ta ba su koda a mace
ko a raye ne. Chongololo
Dalilin da Yasa 'Ya'yan Cafalike Da Hawaye A Fuska 4mins 49sec. A wani
zamani anyi wani mugu kuma malalacin maharbi, wata rana zaune a gindin bishiya
dake tudu yana kallon
garken wasu namun dawa suna tafiya suna kiwo cikin kwanciyar hankali,. Domin
haka shi maharbin bai ma damu da ya tashi domin farautar su ba, domin bai son
wahalar da kan sa cikin daji. Can sai yaji motsi cikin
ciyayi ta dama dashi. Ashe wata damisa ce ke kwanto tana jan ciki a hankali
domin farautar daya daga cikin
wasan nana namun dawan dake tafiya cikin garke. Damisar tans sanda tana dada
matsowa kusa da su wadan nan dabbobin. A hankali a hanali kana tana kokarin
boye kanta. Shi wannan maharbin lyana nan yaana kallon
duk abinda ke gudana, daga cikin dabbobin da lya bar garken shine damisar
take fako wajen wannan hari na ta. Nan da nan sai tayi wani irin kukan kura
ta aukawa wannaan dabbar da gudu kuma da karfin tsiya to kamo
ta. Daga nan sai damisar ta dauko wannan dabbar da ta kama zuwa wata inuwa cikin
ciyayi. Shi kuwa wannan
maharbin yana nan cikin al 'ajabi da mamakin irin wannan hanzari da karfi da
damisar tayi amfani dasu wajen kama wannan dabbar. A yayinda yake kallon ta
sai kuma yaga ashe tana da wasu 'ya'ya guda uku kyawawa
ita damisar wasaanda suka jiran ta a inuwar.
Daga nan sai kuma maharibin ya fara tunanin kko zai dauke wadan nan 'ya 'yaan
damisar domin ta haka yake
gani shima zaiyi nasara kamar yadda uwar tasu tayi nasara kan wannan dabbar
da ta kama. Domin haka sai lya shirya mugunta a zuciyar sa, yana sane da cewar
damisa bata tsare mutum, domin haka sai ya shirya cewa zai
dauke daya daga cikin 'ya 'yan tan nan uku ya kowa masa yadda zai rika yi
masa farauta. Sabode haka sai ya shirya har yazuwa lkacin da damisar zata bar
wurin da 'ya 'yan nata suke. Yayinda rana ke faduwa sai damisar
ta bar 'ya 'yan nata a wannan wurin ta tafi domi neman ruwan sha. Ganin haka
sai wannan malalacin maharbin
ya dauki mashin sa ya nufin wurin da 'ya 'yaan damisar suke. A nan ne yagan
su guda uku kanana ko gudu ba sa iyawa. Bai yanke shawara ko wanne daga cikin
su zai dauka ba, can sai yace gara ya dauke su duka uku
domin yafi kan ya dauki daya.
11 11
11 Page 12 13
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Yayinda damisar ta komo bayan minti 30 sai ta iske an sace 'ya 'yan nata
duka uku. Sai fa ta fara kuka tun cikin daren har washe gari kuka takeyi na
rashin 'ya 'yanta kuma tana kukan ne da karfi ta yadda mutanen
dake zaune a kauyen dake kusa kuk suna jin ta, sai wani tsoho yazo domin ganin
abinda ya same ta. Allaah Ya sa shi wannan tsoho yana da hikimar zaman duniya
yana kuma da ilmin dabbobi tare da kaunar su. Yayinda
lya ga abinda ya faru, sai yayi fushi ainun, bawai kawai malalacin maharbin
yayi satan 'ya 'yan ta ba har ma ya
karya dokokin farauta da suka shinfida a tsakanin kabilar. Kowa na sane cewar
maharbi tilas ne yayi amfani da karfin sa wajen yin farauta, amma ba daukar
kananan dabbobi ba, kum, a duk wanda ya karya wannan ka
'ida za a hore shi. Sai tsohon ya kooma kauyen ya shaidawa sauran dattawan
kauyen irin abinda ya faru. Sai mutanen kauyen suka fusata, sai suka je suka
sami malalacin maharbin suka fatattake shi daga kauyen baki
daya, bayan sun kwace ' ya ŭan damisar.
Suka daukko 'ya 'yan daamisar suka maidawa da ita damisar. Amma saboda tsananin
kukan da damisar tayi-taayi hawaye sukayi da zubo mata, shine ya sa yanzu haka
in kaga damisa za kaga fuskar ta akwai jiwayen
hawaye a idon ta. Domin haka har kwanan gobe kabilar Zulu dake Afrika ta kudu,
sun dauka cewar hawayen dake fuskar damisa, ta barli ne domin tuna mata irin
kukan da tayi saboda rashin 'ya 'yan ta da malalacin
maharbi ya sace mata. When Hippo Was Hairy
Rijiya 10mins 55sec. Fari babban ma tsala ce. Yayi tsanani ta yadda
dukkan dabbobi suna ji suna gani duk wuraren da suke samun
ruwa suka bushe daya-bayan-daya. Yayinda dabbobin suka ga cewar tsakanin lokacin
da fadamar su ta karshe ta bushe yazuwa lokacin faduwar damua akwai lokaci mai
tsawo, sai suka shawar ta yin wani abu.
Domin haka sai suka kira taron da kowani dalya daga cikin nau 'in dabbobin zai
halar ta domin bada shawara kan abinda za 'ayi. A ranar taron sai dabbobin suka
taru suka tattauna inda suka yanke shawarar su hada kai
tare domin gina rijiyar da zasu rika samun ruwan sha. Sunce rijiyar tilas tayi
zurfi domin gudun kada ta kafe in har farin yayi tsanani cikin 'yan shekarun
nan. Kowace dabba zatayi bakin kokarin ta wajen aikin gina rijiyar
kuma ruwan kowai zai samu ne daidai-wa-daida.
Domin dabbobin na matukar bukatar ruwa sai basu bata lokaci ba wajen amincewa
da wannan shawarar saidai kurege ne kadai. Me in haka rijiya domin wani ya amfana?
inji shi badai ni ba domin bana bukatar ruwa
domin haka mai zai sa na gina rijiya.? Manyan dabbobin sai suka ce in baka shiga
aikin gina rijiyar ba to fa ba zaka sha ruwan ba. Wannan sai yayiwa kurege dadi
yayi kwanciyar sa yadda yake so, yayinda saurasn
dabbobi suka dukufa kan aikin gina rijiya. Sukayi ta hakan kasa ba dare ba rana
sannu kan hankli rijiya sai zurfi takeyi kwana da kwanaki. Wata rana masu hakar
rijiyar suka iso sai suka samu hakar su ta cimma ruwa
domin ruwa ya cika makil sai murna.
Bayan aiki tukuru da dabbobin sukaayi kuma sukaayi nasara, sai suka kuduri aminyar
cewar malalacin kurege
da yaki aiki ba zai taba ruwan nasu ba, kana shawarta nada daya daga cikin su
domin ya rika gadin rijiyar dare da rana. Damisa wanda take ban tsoro daga halittar
ta tace zata fara yin gadin rijiyar domin duk wanda lya
ganta sai ya tsorata Fari dai sai kara tsanani yakeyi dukkan fadamu da koramai
sai dada bushewa sukeyi. Har ta kai ga ragowar fadamar dake da ruwa ita ma ta
bushe. Kurege yaga babu wurin samun ruwa saidai rijiyar
nan da dabbobi suka gina. Kuma yace tilas ne ya sami ruwan da zai sha. Yayi
ta sintiri a lyankin da rijiyar take
amma sai yaga akwaai mmai gadi.
12 12
12 Page 13 14
Vol II No. 13 December 1999 (Hausa) CHANGE Radio
Yayinda sauran dabbobi suka gana kurege ya yaudari damisa har ya sha ruwan
su sai dasmisa taji kunya. Sai aka zabi kura da tayi gadin rijiya, domin suna
gani tana da wayoon da ba zata yarda kurege ya yaudare ta ba.
Amma dda maraicen ranar sai kurege ya sake zuwa da zuma gun kura. Saboda kwadayi
ita maa ta yarda kurege ya yaudare ta da zuma har ya daure mata hannu ya sha
ruwa yayi wanka duk a rijiyar tasu. Sai kunkuru
yazo yace zaiyi gadin rijiya. Sauran dabbobi sukayi ta mamaki inda suke cewa
yanzu saka iya yin wani abu
inda damisa da kura suka kasa? Me zaka iya yi? Yace adai bashi dama, sai dabbobin
suka ce to mun baka.
Nan da nan kunkuru ya dagira ya kira matar sa don ta taimaka masa. Sai suka
tafi gid itaacen karo tra dibi karko ta shafa a duk jikin kunkuru ta ko ina.
Sai kunkuru yayi murmushi da ganin haka, kana ya kkoma bakin
rijiya. Ya gina karamin rami inda lya sanya kafafun sa da kansa ciki yabar sai
bayan sa kawai. Yla yazamana
kamar dutse ne kawai. Lokacin da kurege yazo bakin rijiya sai yaga babu mai
gadi yayi dariya kamar cikin sa zasiyi ciwo, yace ai nasan za ayi haka, domin
zanlyi amfani da rwawn kamar yadda nakeso. Domin kuwa
basusan halin kurege ba ne ainine sarkin wayo inji shi. Kurege ya dirki ruwa
a rijiya kamar yadda ransa ke so yalyi wanka kana yayi alkafura. Bayan day gama
sai yafito domin nema wurin da zai tsaya ko ya zauna domin
ya tsane a rana.
Con ya ga bayan kunkuru sai yace ah ga ma dutse kusa dake jira na zauna kan
sa. Domin haka sai kurege ya zauna kan balyaan kunkuru dake da kasro har sai
da ya bushe. Ylayinda zai tashi zuwa gida sai yaji abu lya
kama shi. Sai yace menene haka ya rike yayi kokari domin kubucewa daga inda
yake zaune amma ina dankon karo ya kama shi gam. Yayindda kunkuru ya ga lallai
kurege ya kamu sai ya tazso daga cikin ramin,
ya fara tafiya inda lyake cewa kurege yau kan Allah Ya kama ka. Sai kazo muje
dakai. kunkuru yayi farin ciki da nasarar da ya samu.
Kurtege ya san lallai ya shiga hannu, sai yayi ta maza yace da kunkuru gara
ka barni na lafi. Domin ba kasani ba hannu na na dama na da karfi ina iya yiwa
dundu a baya har na fasa beyan naka caka-lcaka. Sai kunkuru
yace bugi. Kurege ya daga hannun sas na dama ya daoki bayan kunkuru sai hannu
ya makale. Yace kuncuru hannu na na hagu yafi na dama yafi na hagu karfi zan
doka kama, yace doka, ya kkoka sai hannu ya makale
a bayan kunkuru Kurege yace kunkuru kafa ta ta hagu tafi hannun karfi zan doka
maka a baya. Kunkuru yace doka ba komai, sai kurege ye doka kafar sa a bayan
kunkuru, sai kafa ta manne a baya. Haka kuma ya doka
kafar sa ta hagu ita ma ta manne a bayan kunkuru shidai sai tafiya yakeyi da
kurege. Kunkuru dai yayi ta tafiya
da kurege a bayan sa makale har zuwa ga shugabanin dabbobi, domin yi masa hukuncin
da ya kamace shi. Shangani/ Folktale
Karin Magana 51 Sec. Munsha jin yadda Adamu da Hauwa'u suka bar cikin
aljanna zuwa duniya. Haka kuma tunda muka fara
rayuwa a tsaye muke tafiya.... kuma muna kyautata zato watan-wataran zamu bace
daga wannan duniya. Watakila bacewa ba itace kalmar da ta dace ayi amfani da
ita ba. Domin in har mun bar wannan duniya babu
wani'wuri da zamu sake bulla kuma kamar yadda Adamu da Hauwa'u suka bulla cikin
wannan duniya. Babu wata duniya dake makale a sama wanda zamu koma bayan mun
bar wannan duniyar. Ita dai wannan duniyar
kyakkyawa mai kuma cike da hatsari itace kadai muke da ita. Gerald Durrel
13 13
13 Page 14
December 1999 (Hausa) CHANGE Radio Vol II No. 13
Sau Nawa Kudan Zuma Keyin Zuma A Shekara? 1min. 28sec. Kudan zuma nayin
zuma ne yayinda itatuwa ke fidda furanni. Yayinda kudan zuma ke diban wani irin
ruwa mai
zaki daga furanni, haka kaka kuma kudan zuman ke daukar kwayoyin tsirrai daga
wannan fure zuwa wancan. Itacen da yafi bada zuma mai kyau a gabashin Afrika
shine wanda ake kira MUTUNDO haka kuma ana kiran
sa MUCHESA wanda yakeyin fure daga watan Maris zuwa na mayu. A wasu kasashen
Afrika misali itatuwa nayin furanni ne tsakanin watan Disamba zuwa Fabrairu
dakuma tsakanin watan Maris zuwa Mayu. A Zambia
ana samun zuma ne a lardin Mwinilunga, daKambompo dakuma Zambezi dake sashin
arewa maso yammacin
kasar. Wadan nan sune yankunan da ake samun zuma tun kaka da kakanni kuma nan
ne ake cinikin zuma sama da shekaru 150. Zuma na daya daga cikin abinci mafiya
dadi dake samu daga Allah. Ka san yadda
kudan zuma keyin zuma? Kudan zuma ne kadai ke yin zuma. Suna daukar digon
ruwan NECTA a bakin su da wasu abubuwa na musamman da Allah ya basu, sai suyi
ta furawa sai zuma yayi ta fita.
Chongololo
Abubuwa Mau Amfani
Alkalia Amurka Ya Hana Saran Itatuwa, Domin Kare Kifi 51sec. Wani alkalin
tarayya a kasar Amurka kwanan nan ya yanke shawarar da zai dadadawa wanda zaai
amfana da
batun rai. Cikin watan jiya wani alkali a Seattle dake washington ya dakatar
da cinikin katako daga gandun
dajin tarayya dake bakin kogin Umpqua dake arewa maso yammacin kasar bisa dalilin
cewa gwamnati ta kasa yin la'akari kan ko sare itatuwan katakon zaiyi lahani
ga kifafen dake cikin kogin. Me wannan ke nufi? Yana
nufi kenan yanzu gwamnati zata sake komawa baya komin bin umurnin kotu. Tilas
tayi cikakken bincike kan irin hanyoyin da suka dace ta hanyar aiyukan kula
da muhalli wanda a karshe gwamnatin ba zata rika sare
itatuwan katakon barkatai ba. ENN.
Sabuwar Kawan Domin Yakar Sassaucin Cinikayya 1min. 5sec. Yanzu haka
an shata layi a yashi domin yaki da dokar cinikayya ya duniya wadda ta sanya
kasashe masu
tasowa da matalauta cikin kunci ainun. Kungiyar cinikayya ta duniya wanda itace
mafi girma da karfi kan cinikayya a duniya tasha samun suka kan yadda take tursasawa
jama'ar dake kasashe masu tasowa wanda a
sakamakon haka take tilas ta musu dogaro kan dan albarkatun su da baitaka kara
ya karye ba. Yanzu kungiyar
ta WTO da sassaucin cinikayya suna karfafa yin kawance a dukkan fannoni. Kungiyoyin
kwadago dana kare muhalli a Amurka sun bada sanarwar kafa kawance danufin yakar
tsarin sassaucin cinikayya. Babban abin
sha'awa anan shine domin kungiyoyin dana muhalli sune ke sahun gabe wajen
kare albarkatun kasa. ENN.
Sabbin Halittu Zun Zama Faraki 1min . 5sec. Yau shekaru da dama kenan
masana kimiya sukayi imnin cewar akwai kafafun tekuna a duniyar Mars. Domin
tabbatar da haka da sauran tunanin su game da duniyar Mars hukumar binciken
kimiya ta Amurka (NASA) ta tura wani kumbo domin yayi mata bincike a shekarun
1970. Abubuwan da kumbo ya dawo dasu daga Mars
yaso ya tabbatar da wanna tunani da masana kimiyar keyi. Hotunan sun nuna dacan
anyi wasu manyan tekuna da suka rufe sashin arewacin duniyar ta Mars. domin
sun nuna hotunan da sukayi kama da hakan. Sabbin
hujjoji sun nuna wannan tuini ba gaskiya bane. Kamar yadda sakamakon binciken
da aka gudanar ya nuna a
watan Oktoba, wanda akayi da kwararun kayan aiki ya nuna babu irin wannan layukan
ruwan tekun. ENN.
14 14
© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw