Go Back
Communicating for Change

Document Body Page Navigation Panel

Pages 1--13


Page 1 2
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

1
CHANGE
Abubunwan Da Keciki
Samun Ci Gaba Lokaci Shafi

SHIRIN SAUKAKA TALAUCI
Sauyi a fanin noman dankali. 5mins. 57secs 5 Wata kungiya a Najeriya ta fara shirin koyon dubarar inganta tattalin arziko

irin na kamaru.
Samun Kudin shiga 14secs. 12 Kusan rabin iyalai a Amurika suna Samun Naira milyan biyar a shekara.

Tsalakawa zuwa neman rayuwa mai inganci 46secs. 12 Al'umma Zimbabwe suna gudu zuwa Afrika ta kudu damin Inganta rayuwarsa.

KIWON LAFIA DA GINA JIKI
Rigima a kan sinadarin halitta 3mins. 29secs. 7 Amurika ta arewa da nahiyar Turai suna cikin rigima a kan ingancin naman

shanun da ake safara.
Gina Jiki 22secs. 11 Da alamun duniya zata yi asarar samun kifi

Masu dukiya sun handame harajin kula da lafia 1min. 23secs. 4 Masu kudin Amurika suna samun ingata cen Kiwon lafiya ta hanyar
harajin talakawa.

RAYUWA
Yanayin muhalli 9secs. 11 Fadamu masu dausayi suna taimaka hayaiyafar alumma.

Matsalar yan gudun hijira tana kalubalantar Zaman lafia a kudancin Afrika 4mins. 17secs. 7
Dawainiyar yan gudun hijira a Afrika ta fara zama Babbar dawainiya
Babban Alfanun mulkin malaka 1min. 28secs. 8 An Tsara Nairobi da nufin ya dace da yanayi mai dausayi

SASHIN MULKI
Matsalar tsuke bakin aljihu ta halfar da rigingimu a Nicaragua. 1min. 30secs. 5 Tarzomar dalibai ta kusa kifar da gwamnatin kasar Nicaragua.

A Kan Dimukradiyya 1min. 37secs. 10 Baiwa mata ikon mulki abu ne da zai Tabbatar da nasarrar dimukradiyya a Najeriya.

ILIMI
Daliban Afrika a Burtaniya da Amurika 29secs. 12 Yan Afrika nawa ne da ke Amurika suke karatu?

ABINDA YA FARU
Ranar 16 ga watan yuni 1999: Ranar tunawa Da yaran Afrika 1min. 6secs. 4 Shirin mika mulki a hanun farar hula, zata iya shafar ranar bikin tunawa da

yaran Afrika 1
1 Page 2 3
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

2
CHANGE
Muhalli
Biyar ga Watan Yuni Ranar Muhalli ta duniya 1min. 12secs. 3
Duniyarmu guda ce, ka kareta.
MANYAN NAMUN DAJI
Dogon hancin giwa domin kare hatsari 1min. 50secs. 3 Giwaye na da dubara mai ban mamaki na kare kansu daga hatsari. Biran da ke

kan tsaunuka na cikin hatsari. Kisan masu yawan shakatawa a gandun da ke
Bwindi na iya kawo cikas ga aikin kare gandun dajin.

FADAMU MASU DAUSAYI
Fadamu masu dausayi a duniya 33secs. 11 Fadama mai dausayi da tafi fadi a duniya tana a kudancin Amurika.

Yaki a Yugoslavia: Sauran abinda aka lahanta 1min. 20secs. 3 Bayan an kamala yaki a Yugoslavia, akwai Sauran yakin cetar muhalli daga
shiga balai.
Ranar Teku ta duniya ta 1999 1min. 7secs. 4 Binliken kimiyya na baya ya bayyana illar zafaffar yanayi.

RAYUWA
Hawa kan Damisa a Cambodia 2mins. 57secs. 9 Ka ziyarci iyalin da suke rayuwa a muhallin da ke da nakiyar da ke gab

da fashewa

KARE GANDUN DAJI
Lafuzza a kan kare gandun daji daci gaban kasa 26secs. 9 Jinkirta magance matsalar muhalli na kara Lahanta matsalar.

Sashin Yara Mutane 56secs. 10
Yara 20,000 na Birtaniya suna bada Labarin garinsu a telbishin
Wane tsuntsu ne ya fi dadewa a duniya? 41secs. 11 Wasu tsuntsayen sun fi mutane dadewa a raye.

MANYAN NAMUIN DAJI
Hanyar da Barewa ke taimakawa kada 4mins. 10 2
2 Page 3 4
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

3
CHANGE
Labaru
Ranar Kare Muhalli Ta Duniya 5 Ga Watan Yuni 1min. 12secs. Domin bikin tunawa da ranar kare muhalli ta duniya, hukumar kare muhalli ta majalisar dinkin duniya ta yi kiran
a himmatu domin kare muhalli. Wajibi ne ga kowanenmu ya nuna a zahiri niyyar kare muhalli da Lahanta duniyarmu' inji majalisar. Taken wanan shekarar shine, Duniyarmu makomarmu ta gaba ka kareta" A Najeria
za'a yi taron karawa juna sani da gasa kanana, jamman gwamnatu zasu dasa itatuwa. Bikin ranar kare muhali ta zama bikin duniya, ana tunawa da ranar ta hanyar jerin gwano, muhawara da tsaftale muhalli, bikin ya wayar
da kan alumma a kan Lahanta muhalli da sanya alumma da gwamnati su canza halayyarsu da dokokin da ke Lahanta muhalli.
Obasi Ogbonnaya/ UNEP

Dogon Hancin Giwa Na Cikin Hatsari 1min. 50secs. Giwayen da kan zura dogon hancinsu domin neman abinci sun san inda hatsari yake daga masu farauta, sukan
kauce masu dare da rana, sai dai wanan ba abu ne mai sauki ba.
Binciken da kungiyar kare giwaye ta gudanar ya bayyana cewar, dabobi sukan nemi abinci ne tare da shirin
yaki na sari ka noke.

Sukan nemi kariya a gandum dazzukan masu duhu, suna yin hakan cikin kankanin lokaci musamman a dajin da masu farauta suke inji Douglas Hamilton shugaban kungiyar.

Binciken farko ta hanyar amfani da naurar daukar sauti ta kasa gano wanan, wanan ne karo na farko da aka yi binciken ta hanyar amfani da tauraron dan Adam an yi amfani da Giwaye 14 na Afrika domin gudanar da
binciken.
An tara bayanan da aka samu a kowane wata, Wanan ba kaman tsarin bin dabobin ta mota ba inda ake nuna
inda suka nufa da hanu. An san giwaye da son walawa, amma ba'a sansu da balagoro a yankuna masu hatsari ba, masu ilimin kimiyya suna son gano abinda ke haifar da wayewar su.

Mujalar economist.

Yakin Yugoslavia: Sauran Wadanda Abin Ya Shafa 1min. 20secs.
An yi gargadi a kan sinadarin guba da ake zubawa a rafin Darube, baa maida hankali a kan batun ba saboda matsalolin lardin kosovo da kazancewar fadan.

Rohotani sun dora Laifin zuba gubar a kan yakin rohoto daya ne ya gano an zuba mai a gefen rafin Darube. Masu kare muhalli sun yi gargadin cewar zuba guba a rafin na da mumunan sakamako a kan alummar yankin.
Alumma Yugoslavia na cikin hatsari, duk wani ci gaba da Lahanta kasashen Balkan zai kara matsalolin da ake ciki inji Philip Walter Daraktan kare muhali na WWF. Fiye da kasashe 10 ke samun ruwan sha ta rafin
Darube, sun hada da Yugoslavia, Bulgaria da Romania. WWF 3
3 Page 4 5
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

4
CHANGE
Ramar Tunawa Da Teku Ta Duniya. 1min. 7secs. A dai dai lokacin da ranar 8 ga watan yuni ke ka matsowa, domin tanawa da tekuna da albarkatun da ke ciki,
bincike ya nuna cewar yanayi mai zafi na da illa a kan albarkatun teku.
Masana kimiyya sun nuna cewar, raguwar kama kifin salman a Arewa maso yammacin tekun pacific na daga yanayin zafi ba saboda yawaita kama kifi ba, Sauran halittun ruwa na raguwa.

Wanan bincike ya zo dai dai, domin ya kawo karshen zargin da kasar Canada da Amurika ke yiwa juna, kan
Laifin kama kifi da yawa.

Faifan bidiyo a kan sakamkon binciken za'a samar da shi, wanda kungiyoyin kare muhalli na WWF da TVE zasu dauki nauyi.
Obasi Ogbonnaya/ TVE.

Masu Dukiya Sun Mamaye Shirin Yiwa Alumma Inshora 1min. 23secs. Ta ya zaka tabbatar da cewar shirin inshora na kasa da gwamnati ta saukaka domin ya amfani talakawa fiye da
masu dukiya? Wanan ne babbar tambayar
Da ke fuskantar Amurika a yan, Wanan ya biyo bayan abinda aka gano cewar, rage kudin haraji ga wadanda
suka sammar da shirin kula da Lafiyar ma'aikatansu, ya fi amfanawa Amurikawan da zasu iya biyan kudin kula da Lafiyarsu.

Rohoton mujallar Lafia ta Amurika ya nuna cewar, fiye da Dolla bilyan 100 da Amurika ta kashe a wanan fani a bara, ya koma aljihun Amurikawan da keda dukiya, kashi ¼ na kudin ya koma hanun mutanen da ke samun
Dolla dubu 100 a shekara, Naira milyan 10 kenan, yayinda mutum guda cikin Amurikawa biyar bashi da wata inshora.

"A yayinda fiye da Amurikawa milyan 43 basu da Inshora, wajibi ne mu tambayi kanmu, ya dace kashi uku na harajin kiwan Lafiya na shiga aljihun kashi 1/ 3 na yawan Amurikawan da suke da dukiya – "Inji John Sheils
wanda ya yi na zarin. Daily Health Care.

Ranar 16 Ga Watan Yumi Rana Domin Yaran Afrika 1min. 6secs. Hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya ta zabi taken "Ilimin zaman lafiya domin tunawa da ranar
yaran Afrika, duk da cewar an sanar da taken ranar, amma babu wani shirin bikin ranar a Najeriya inji jamiin
hukumar.

Yace hukumar takan fitar da taken ne, amma aikin gwamnati ne ta shiriya bikin.
An samar da kayan da za'a baiwa yan jarida da sauran kungiyoyin da zasu yi bikin, amma shirin mika mulki a
Najeriya zai shafi, bikin, kuma huumar ta fara tunanen canza ranar. Obasi Ogbonnaya. 4
4 Page 5 6
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

5
CHANGE
Matsalar Tsuke Bakin Aljihu Ta Jawo Rigingimu A Nicaragua 1min. 30secs. Tashin farashin mai da tsadar ilimi na iya zama ci gaba mai wuya a kasa, kammar yadda yake a Nicaragua,
kasar latin Amurika ta fuskanci yajin aiki kwanaki shida wanda maaikatan sufuri suka yi, dalilin shirin tsuke
bakin aljihu (SAP) wanda kasashen da ke bada bashi suka bada shawarar kafawa, yajin aikin ya kusa kawo karshen mulkin shugaba Arnoldo Aleman, wanda ke neman bashi daga kasashen duniya.

A ranar 4 ga watan mayu aka kamala yajin aikin bayan da aka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati da direbobin tasi da bus.
Sun yarda gwamnati ta ci gaba da shirinta, amma ta raje farashen fetir daga Dolla 1.50 zuwa Dolla 1: 35, direbobin duba goma sun so a mayar da galon fetir a kan Dolla I kacal.
Tarzomar wadda mutane biyu suka mutu tare da raunata wasu, ta faro dag a dalibai wadanda ke son a kara
kudin daukar nauyin ilumin jamia a kasafin kudin bana, an kashe mutum guda lonaun da yam sanda suka kori daliban daga bankin kasar.

Agitprop.

Kare Lafiyar Birai A Tsaunuka Ya Gamu Da Cikas 1min. 29secs. Harkar yawon bude ido da ke samar da kudi domin kare birai a tsaunuka ta gamu da cikas a uganda, Inda aka
kashe masu yawan shakatawa 8 a watan maris.
An kashe mutanen takwas tare da mai gadinsu Mr. Paul wagabe, a Lokacin da yan tawayen da ake zargi tutsi ne suka kai hari a gandun dajin Bwindi.

Masu yawan bude idon sun hada da Amurikawa biyu, yan Birtaniya 4, da mutanen New Zealand biyu, haka nan akwai mutanen Uganda 4.
Gandun dajin Bwindi ya shahara Inda ake samun Birai 620, ya zama wurin da ake kare Birai wanda gidauniyar kare dabobi ta Afrika ke yi, a cikin karnuka uku, Sir Michaeal Wright ya nuna takaicin Lamarin.
"Mun damu da matanen da rayuwarsu ke cikin hadari, bale batun rayuwar Birai". Inji shi.
Sauran Biran sune a tsaunukan Uganda Rwanda da jamhuriyar Congo, dukaninsu ana tafka rigima, gandun dajin Bwindi ne kawai yaki bai shafa ba a can baya.
Africa Wildlife Foundation.

Kasidu Juyin -Juya Halin Dankali 5mins. 57secs.
Kwanaki da yawa a kowane wata ana cika motoci da dankali, daga kudu maso yamacin kamaru. Ana kai shi har zuwa wasu kasashe na Najeriya, Gabon, Equitorial Guinea, Chad da Jamhariyar, Afrika ta tsariya, Wanan
Sabon abu ne ga mazauna kauyukan Bamenda wanda ya Inganta rayuwarsu.
Makasudin wanan shine dankalin turawa, wanda ke da kyan kalaci idan aka soyada kwai, cibiyar nazarin
dankalin turawa ta duniya ce ta yi dalilin wanan, domin cibiyar ta kwashe shekara bakwai-tana amfani da dankalin turawa, domini canza rayuwar alummar Bamenda. 5
5 Page 6 7
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

6
CHANGE
A tsalaken kasar, wanan sauyin ya jawo hankalin kungiyar samar da ci gaba ta Najeriya, ta shirya gabattar da wanan shirin domin canza yanayin rayuwar alummar kauyen Becheve da ke gandun dajin obudu a jihar Cross
River, wanan muhallin yana da yanayi iri daya da na tsaunukam Bamenda.
Shugabar gudanarwa kungiyar Mrs. Caroline Ifeka ta ziyari cibiyar nazarin noman dankalin turawa domin duba aiyukanta, "Na dawo gida daga kamaru cike da murna" Inji Ifeka, "Na ga irin nasarorin da cibiyar ta
samar na samar da hanyoyin kimiyar noman dankalin turawa.
Cikin abubuwan da Ifeka ta gano sun hada da, irin shuka wanda ke samar da dankali mai yawa, a dankali kilo guda da aka shuka, za'a sami kilo 1000, manoma a kauyuka 100 da ke Bamenda sun fara noman dankalin
torawa, suna hadawa da noman kabeji, albasa da karas Ta Lura cewar manoman da suke samar da iri sun fi samun kudi fiye da masu noma dankalin.

"Wanan ya samar da sauyin tattalin arziki" Inji ta, alumma sun sami rayuwa mai kyau, wanan sakamakon aiki tukuru ne. Matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da marasa ilimi ta zama tarihi, duk sun kama noma.
A matakin farko Ifeka ta ziyarci cibiyar nazaarin noman dankali da ke vom kusa da jos da ke jihar Plateau. Inda ake aikin nazarin dankalin turawa, a Jos ake noman mafi yawan dankalin da ke Najeriya, saboda kyauyawan
yanayi.
"mum gano abubuwa da dama, da Farko yanayin Jos ya fi na Bamenda sanyi, ina ganin suna da matsalar karancin ruwa, don haka sai sun yi ban yuwa, yayinda muna iya shuka so biyu a yankinmu. Haka nan ina ganin
cibiyar ta samar da ingantacen iri fiye da wanda ake shukawa a Jos, kuma tana aiki tare da manoman kafin
girbi". Inji Ifeka.

Kungiyar matan garin Belheve da kungiyar ci gaba a Najeriya sun shuka irin dankalin da cibiyar ta samar, sun kuma gina dakin ajiye irin dankali bisa tsari, kowane kauye na son samun nashi dakin ajiye iri.

Ifeka ta yi imanin cewar wanan zai Inganta matsayin, rayuwar alummar kauyen kammar yadda ta yi a kauyen Bamenda, Inda shekaru 20 Mutane suka bar zama a ginin kasa, sun koma ginin zamani, yaransu na zuwa
makaranta, gashi suna ciyar da kansu wadatacen abincin, aikin shuka dankalin na kungiyar zai nazarin kudin shigar da iyali ke samu, tare da sare nazarin wanan bayan watani 12.

Bayan samun kudi, aikin zai duba kare muhalli da Inganta abincin da alumma ke ci, kasuwanci naman daji shine hanyar samun kudin yankin, ana kama dabobi ne ta hanyar kona daji . Otel da ke kusa da yankin zai sayi
dankacin, amma kungiyar ta yi imanin cewar mutanen da ke gefen tsaunukan zasu sayi dankalin, mutane zasu zo daga udi da ke jihar Enugu da Makurdi a jihar Benue domin sayen dankalin, saboda wadanan dalilai Ifeka
ta yi amanar cewa zaa sami sauyi mai ma'ana a kudancin Najeriya.
Duk da cewar akwai matsaloli, domin irin shuka na cibiyar za'a iya amfani da shine a damina uku kacal, wanda zai kai shekaru biyu, bayan an gineshi a karo na uku, kunguyar zata sake zuwa cibiyar domin sawo wani sabon
iri Obasi Ogbonnaya. 6
6 Page 7 8
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

7
CHANGE
Rigima A Kan Ruwan Halitta 3min. 29Secs. Amfani da ruwan halitta domin barbarar shanu zai haifar da rigima tsakanin Amurika da kungiyar kasashen
turai, wanan ya faru saboda rashin tabbas na irin illar da naman shanun da aka samar ta wanan hanyar ka iya
yiwa mutane, kungiyar ta haramta amfani da irin wadanan magunguna, da safarar naman shanun da aka sammar ta wanan hanyar, amma har yanzu Amurika da Canada suna amfani da wanan hanyar, suna cewar

babu cikakkiyar Shaidar da ta nuna haramcin, Amurika ta zagi kungiyar da hanata gudanar da kasuwanci".
Ana amfani da ruwan halittu shida a Amurika domin sarrafa naman shanu, takadama ta tattare ne a kan uku
daga cikinsu, watau sinadarin estradiol 17 beta, Testosterone da projestrone, wadanda ke faruwa a dabobi da mutane.

Dukansu Amurika da kungiyar sun amince cewar maganin zai iya hadasa cutar sankara ga mutane, idan aka sanya suka wuce wuri, kungiyar tama zargin cewar manoman Amurika sun zarce ka ida, a naman da suke
samarwa.
"Akwai shaida ta zahiri da ke nuna cewar sinadarin estradiol 17 beta na hadasa sankarar nono" Inji johanna Fink-Gremmel, Wani farfesa magungunan dabobi wanda ke shugabantar Tawagar nazarin amfani da sinadarin
na kungiyar tarayyar turrai.
Kodayake baa yi bincike a kan sinadarin ba, amma kungiyar ta yi imanin cewar zasu Hadasa cutar sankara, domin suna kai hari ga kwayoyin halitta na DNA, sun ce irin wanan magani yana da hatsari. Irin wanan
takadama hukumar cini ki ta duniya ke shiga tsakani, a nan ta goyi bayan kasashan Arewacin Amurika, cewar sinadarinsu bashi da hatsari, zaa iya sayen namansu a turai.

"Idan aka dasa su da kyau a fata ko kunen daba, wadanan sinadaran basu da hadari" Inji hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurika.
Kwamitin hukumur Lafiya ta duniya, da na hukumar abinci da aikin gona sun ce sinadarin bashi da hadari,
wanan kwamitin yana duba illar da maganin ke yiwa Lafiyar mutane, tare da baiwa hukumar ciniki ta duniya shawarar matakin da ya dace a yi amfani da shi, kwamitin ya amince cewar sinadarin estradiol 17 – beta na iya

jawo sankara ne idan ya hadu da wasu kwayoyin halitta, ba wai yana kai hari kan sinadarin DNA ba. "Zaa iya gwada yawan irin wadanan sinadaran, kowane bangare na jiran sakamakon binciken da aka gudanar, domin
samun shaida ta zahiri ko si nadarin na da illa ga Lafiyar bani Adama. The Economist.

Matsalar Yan Gudun Hijira Tana Kalubalantar Zaman Lafia A Kudancin Afrika 3mins. 53secs.
Yakin da yaki cinyewa a Angola da wasu rigingimun siyasa a kudancin Afrika, ya raba milyoyin mutane daga gidajensu, ya sanya Afrika zama Nahiyar da tafi yawan yan gudun hijira.

Afrika na da yan gudun hijira fiye da milyan shida, mafi yawansu a tsakiya da kudancin Nahiyar, da kasashen da ke kusa da manyan rafuka aikin kulawa da su ya jefa bukata a kan dan abindu Afrika ta malaka, a wasu
wuraren wanan ya dagula danganlaka tsakanin alummu. 7
7 Page 8 9
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

8
CHANGE
Fiye da mutane 600,000 ne suka rasa muhalinsu a Angola, tun lokacin da aka fara yaki a watan Afrilun 1998, wadanan mutanen sun arce zuwa Namibia, Zambia, da Malawi masana sun yi hasashen cewar yawansu zai iya
karuwa.
Zambia na da yan gudun hijirar 200,000 daga Angola, Burundi da jamhuriyar Congo da Rwanda, yan gudun hijirar Congo suna arcewa zuwa Tanzania wadda tattalin arzikinta ya durkushe saboda bashi, Lisafin baya ya
nuna akwai yan gudun hijira 50,000 a yammacin Tanzania.
Malawi da tafi kowace kasa talauci tana da yan gudun jirira 1000 daga Somalia, Rwanda, Burundi da jamhuruyar Congo, ta taba samun yan gudun hijira fiye da milyan guda a lokacin yakin basasan Mozambique wanda aka
kamala a shekara 2o da suka wuce, kwanakin baya yan gudun hijira daga Namibia su 3,000 suka shiga Botswana saboda rikici a Lardin Caprivi.

Mozambique, Afrika ta kudu da Namibia da Zimbabwe sun sami yan gudun hijira daga Angola, jamhuriyar Congo da yankunan gabacin Afrika.
Kusan dukaninsu suna fama da rashin kulawa ko tusasawa, a shekarar 1998 an kashe yan gudun hijira goma a Afrika ta kudu saboda an zargesu da aikata taadanci a cikin alumma. A halin da ake ciki Angola tana zargin
Zambia da cewar, tana goyon bayan yan tawayen da ke fafutukar kifar da gwammatin kasar, amma Zambia ta musanta zargin.

Lucius chikuni kwamishinan hukumar shiryawa afkuwar balai da bada taimako a Malawi yace, Kudancin Afrika na fuskantar matsalolin yan gudin hijira, saboda kasashen na da nasu matsalolin na daban.
"mafi yawan wadanan matsalolin tattalin arziki ne, yawan hayaiyyafar jama'a da' dimbin bukatun yau da kullum daga gwamnati" inji chikuni a wajen taron hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, wanda
aka gudanar a Afrika ta kudu, matsalolin sun hana su duba nasu saboda na yan gudun hijira.
Wata Babbar matsalar kulawa da yan gudun hijira shine yadda wasu ke malakar bindigogi, wadanda ke fakewa a sansanonin domin cimma bukatunsu na siyasa. Ana zargin cewa suna samun taimako daga kasashen
da ke goyon bayansu, kasancewarsu yakan mayarda sansanin wurin kai hari ga sojoji. Wanan ya sanya kwararu na kira ga kasashen duniya, da su magance matsalar yan gudun hijira tun daga tushe. Ya zama wajibi
a dauki manufofin rage dalilan samuwar yan gudun hijira daga kasashen yankin da na duniya Inji-Phylis Johnson
shugaban cibiyar nazari da adana bayanai ta kudancin Afrika. Newslink Africa.

Bayanai Na Musamman Babbar Akidar Mulkin Malaka 1min. 28secs.
Wani baturen ingila da aka tura zuwa Nairobi a bana, yana da niyya mai kyau a kan inganta birnin na gabacin Afrika, manufarsa zata sanya sunanshi cikin tarihi mai amfani.

Manufarsa ce ya samar da dokoki domin birnin Nairobi. Ko ta yaya zai yi? Ya rubuta wasika zuwa ga birninsa na Blackburn a Lancashire da ke Ingila, Inda ya nemi a aiko mashi da dokokin birnin, da ya samo sai ya baiwa
mai buga keken rubutu, "Rubuta wanan kamar yadda suke" ya bada umurni, amma duk Inda kika ga "Blackburn" 8
8 Page 9 10
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

9
CHANGE
to ki rubuta Nairobi cikin dan lokaci sai Nairobi ta sami dokokinta na farko. Kuma babu wanda yaga wani aibi a dokokin, duk do cewar Nairobi birni ne mai yanayin mai zafi.

Sai a 1970 ne gwamnatin Kenya ta gano cewar an samar da rufin dakuna a Nairobi ne da nufin su jure kankara mai nauyin inci tara.
Intermediate Technology.

Hawa Bisa Damisa a Cambodia 2mins. 57secs. Shin zaka so rayuwa a tsakiyar nakiyoyi? Tawagar masu yawan bude ido wadand ke son ganewa
idanunsu sun ziyarci Cambodia daya daga cikinsu yayi tsarabar irin yadda wani iyali ke rayuwa su yi aiki a wani fili.

"Shi mutum ne mai shiru shiru wanda yake kai da komowa a cikin kayan marmari da ya shuka, yakan tsaya ya juya ganyen amfani gonar, a wanan karon yana yi a hankali, ya yiwu saboda zafin ranar, kuma ma saboda kafa
daya gareshi ya dogara ne a kan katakon da yake dogarawa, ya sanya katakon kusa da kafadarsa, gashi gonarsa na a kan hanyar da ke Arewa maso yammacin Cambodia, wadda ke da nakiyoyi, mutun zai tsamanin
shima nakiya ce ta lahantashi.
"Akwai kyalle mai Launin ja da fari wanda ya zagaye gidansa, amfanin gonar da ya fitar da hanyar zuwa diban
ruwan pampo ya nuna cewar yana zaune a wurin da aka kebe mai hadari, an rubuta kalaman" yi hankali da nakiya" an rataye a sassan gidan.

"A Lokacin da muke kalon yarinyar ta nufo shi daga filin gidan, tana sanye da kudadden tufa, sai ya nufi inda yarinyar ta fito Inda wata siriyar mata ke jira, wanan yanayi, na ban tausayi da wanda ya fada bada sani ba,
tamkar wanda ke haye da Damisa a jeji zai wuya a yi imanin cewar suna zagaye da nakiyoyi ne wadanda ke jiran fashewa, wanan ne sakamakon shekaru ana rigingimu a kan malakar kasa.

Babu wurin tsira ga wanan iyalin, fita daga gidansu hatsari ne. A Lokacin da muka nufi kan hanya, mun gane cewar ba wai a filaye ne kawai aka bizne nakiyoyi ba, har da makarantu, rafuka, gadoji da dakunan ibada.
"Amma me ya sa wanan mutum ke zama a muhallin mai hatsari Inda kuskure kadan na iya lahanta rayuwarsa. Amsa mai sauki ce, wa zai dauki manomi mai kafa guda aiki?, kuma ina zai kai iyalansa India babu hatsari?

Fiye da Nakiyoyi milyan shida aka bizne a Cambodia, masana sun ce zaa iya daukar shekara 25 kafin a share nakiyoyin, a halin da ake ciki daruruwan manoma sojoji, mata yara da dabobi na afkawa cikin waman balain
a kowace shekare. World Council of Churches.

Lafuza Na Kare Muhalli Da Ci Gaba. Game Da Muhalli 18secs. "Datti da gurbacewa na lahanta ginshikin dogon Lokaci domin ci gaba mai inganci, kasar da ta Lahance a
yanzu bazata kula da ci gaban yaran gobe ba, ruwan da aka gurbata domin tara dukiya cikin sauri ba zaa iya
tsaftace shi domin samun amfani nan take ba. Barber canable: tsohon Daraktan, Bankin duniya. 9
9 Page 10 11
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

10
CHANGE
A Kan Dimukuradiyya 1min. 37secs. Mafi yawan mata suna cikin talauci, a yanzu su ke ciyar da iyalansu, suna daukar nauyin yaransu, mazansu da
ma sauran iyalan gida wanan aiki ne mai wahala a kansu, ba zasu iya ci gaba da shi ba, shi yasa kake ganin suna
bara gida gida…………….. basu a natse, basu da ilimi kuma basu da wata hanyar samun kwabo …….. babu wata hanjar samun kudi.

"Matsalar ita ce yanzu a Najeriya muna da matsaloli na tattalin arziku, amma abin ya fi tsanani a yankunan karkara musamman a Kano. Wasu mazajensu bazasu iya ciyar-dasu ba, saboda uwa tafi kusa da yaranta
bazata iya cemasu babu ba, uwaye sukan nemi hanyoyin ciyar da yaransu.
Shi yasa a yanzu muke da mata da ke yin kananan samao'i, duk abinda hanunsu ya kai, yanzu da zaa mika mulki a hanun farar hula, mata na son samun yan kudi a hanu idan ba haka ba, babu wata dimukradiyya mai
inganci da zamu samu. Laila Buhari, jamia'a kungiyar lauyoyi mata ta Najeriya.

Sashin Yara Labarin Wanan Karni 56secs.
Fiyeda yara 20,000 a Burtaniya sun dauki salon bada labaru da ake hadawa da dandanon majigi irin nada. Kimanin yara daga makarantu 200 sana shiga cikin shirin bada Labarin garinsu a telbishin cikin shirin Garinmu
a yau" Ana gudanar da kowane shiri a dakin shiryawa mai daukar mutane 500 da ke a Ingila, Inda yara ke
gabatar da tarihin garinsu.

Shirin na "Tarihin Garinmu yana da inganci", to amma akwa, irin wanan shirin a telbishin na Scotland, domin girmamawa sai aka fara gabatarda Labarin birnin a dakin shiryawa na Dome.
London Press Service.

Manene Yasa Barewa Ke Taimakon Kada 4mins. Lokacin mai tsawo bayan da mutum ya baiyana wanda ya kawo farauta, dukanin dabobi suna tsoron zaki.
Shine Babban masu Farauta, har mutum yana tsoronsa saboda karfinsa.
A farkon wanan Lokaci Barewa tana zaune tare da sauran dabobi, a Lokacin da zaki ke farauta barewa takan
gudu tare da sauran dabobi, cikinsu, giwa ce kawai ke iya kare kanta saboda karfinta. Zaki yana da zafin nama kuma yakan yi farauta cike da alfahari, mafi yawan dabobi sukan fada hanunsa.

Wata rana dole Barewa ta gudu Lokacin da zaki ya farma garkenta, amma bayan da suka fafata Barewa ta sami tserewa. Tayi gudu mai nisa Inda ya iske daji mai girma, tayi ta yawo a cikin gandun itatuwa, Barewa ta
yanke shawarar cewa wanan kyakyawan wuri zama ne, ga yalwatacen abinci, wadataccen ruwa, sanan ga damar tserewa zaki.

Ana cikin wanan hali sai Barewa ta ji kuka ana neman taimako, a kusa da rafin kada ta sagale ta kasa tafiya, da ta ga Barewa sai tace "Don Allah taimakeni kamar yadda kika gani na sagale kuma zaniya mutuwa saboda
yunwa. 10
10 Page 11 12
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

11
CHANGE
A yanzu Barewa ta san yadda kada take, ana tsoronta a ruwa kamar yadda ake tsoron zaki a fili. Barewa sai ta ji tausayin kada, ta yanke shawarar taimakonta. Amma da farko sai tace "Duk da karfinki kada, da zan tafi
in barki da sai ki mutu, amma zan taimakeki bisa sharada guda". Bayana sharadin ya ke mai tausayi saboda
raina a shirye nike in amince" kada ta yi roko.

"A madadin cetonki zaka barni in shiga ruwa kodai domin in sha iska Lokacin zafi, ko in boyewa makiyana wajibi ne ki barni cikin aminci a muhatinki",

Bisa wanan sai kada ya amince, nan take sai Barewa ta fara cire kada, duk da sarkakiyar wurin, ta yi amfani da kahonta ta kubutar da kada.
A Lokacin da kada zata shiga ruwa sai Barewa tace "Tuna da alkawarinka kada, na tabbatar da karfinka, idan ka karya alkawari ta ba za ka ji da kyau ba".
Kada ya yi alkawarin ba zoi ci amana ba, ya yi nutso a ruwa ya godewa taimakon da Barewa ta yi. Tun wanan Lokaci da Zaran Zaki ya farmaki Barewa sai ta gudu zuwa rafi, (mafi yawan dabobi dangin mage basu son
ruwa ya taba jikinsu) amma Barewa tasan cewa ta tsira daga harin kada, kuma ya yiwu kada tana dan jin tsoron Barewa.
When Hippo was Harry.
Wane Tsuntsu Ne Ya Fi Dadewa A Raye? 41secs. Wanan tambaya ce mai wuyar amsa, domin abu ne mai wuya a san shekarun tsuntsayen amma wadanda a ke
tsare a gidan zoo ko gidajen mutane, ta wanan hanya mun gano cewar tsuntsaye kan rayu fiye da shekaru 80.
Tsuntsun da yafi dadewa a duniya shine wani irin Aku da ake kira cockatoo, an fi saminshi da cocky, domin iyalan da suka ajiyeshi a gidansu tun shukarar 1902 harzuwa 1982 kafin ya mutu.
Chongololo.
Bayanai Masu Amfani Gina Jiki 22secs.

Fiye da kishi ¼ na kifayen da ake samarwa a duniya a shekaru goma da suka gabata suna fitowa ne daga ruwa mai tsafta. Wanan abu ne mai muhimmanci domin kuwa kifi ne Babbar hanyar samun abinci mai gina jiki ga
talakawa, gashi ruwa mai tsafta na raguwa cikin sauri saboda masu aikin masanaantu.
Muhalli 9secs. Fiye da kashi goma cikin dari na yawan alumma duniya, Bilyan biyar suna dogara ne a kan ruwa mai tsafta
domin su rayu.
Muhallai Masu Dausayi A Duniya 33secs. Muhallai biyar masu dausayi a duniya sune na Pantanal da ke Latin Amurika, sai na Congo da Zaire da ke
tsakiyar Afrika. Sai Fadamar taster da ke Australia da Fadamar mekong da ke kudu maso gabacin Asiya da kuma rafin yangtze da ke china. Rafin da yafi girma da yalwa shine na pantanal wanda kasashe uku na Brazil,
Bolivia da Paraguay suke amfana da shi.
An bayyana cewar rafin Niger Delta da ke Najeriya shine na uku a girma da dausayi a duniya. WWF. 11
11 Page 12 13
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

12
CHANGE
Samun Kudin Shiga 14secs. Ko kasan cewar kimanin ma'aikata milyan 90 da ke Amurika suna samun Dolla dubu hamsin a kowace
shekara. Wanan ya yi dai dai da Naira milyan biyar a shekara. Agitprop.

Gandun Dajin Da Baa Kula Da Shi 18secs. Tambaya: ko kasan gandun dojin da ba'a kula da shi ba?
Amsa: Wanan shine halataccen gandun dajin da aka kare, amma rashin kudi da iko ya hana a kula da shi.

Daliban Afrika A Birtaniya Da Amurika 29secs. Alkaluman Lissafin da hukumar ilimi kimiyya da al'adu ta majalisar dinkin duniya tare da hukumar kula da yan
gudun hijarar majalisar suka bayar, ya nuna cewar kimanin mutane Afrika 11,000 da ke karatu a Birtaniya mafi yawansu daga Kenya da Najeriya suka fito.

Daliban Afrika da ke Amurika sun ninka wadande ke Birtaniya yawa, kuma kashi 40 cikinsu daga gabashin Afrika suka fito.
Newslink Africa.

Tsallake Kan Iyaka Domin Samun Ingancin Rayuwa 46secs. Bisa dukan alamu rashin aikin yi a Zimbabwe ya kai mumunan mataki, alummar kasar suna bi kowace hanya
domin ficewa daga kasar, kimanin mutane 18 suka mutu a sindukin da babu taga wanda suke ciki a Lokacin da suka yi kokarin tsallallawa zuwa Afrika ta kudu ta Botswana.

Ofishin kwamishinan Afrika ta kudu da ke Harare yace bai da masaniya ko hanu a cikin batun ya bayyana cewar ya bada takardun visa ga mutane 136,000 yan asalin Zimbabwe a farkon watani tara na shekarar 1998.
Wani bayanin ya nuna cewar tsakanin shekarun 1996 da 1997 mutanen Zimbabwe 200,000 da suka shiga Afrika ta kudu na niyyar kasuwanei sun ki komawa gida.
Newslink Africa.

Masu Ajiye Kudan Zuma 24secs. Mutanen kauyukan Zimbabwe aka fi sani da ajiye kudan zuma, akwai mutane fiyeda dubu 6,000 da suke
wanan aiki, sukan ajiyesu a matsayin abinci da kuma sha'awa. Godiya ga sabuwar hanyar tatsar zumar da suke samarwa, suna samun kudi ta hanyar sayar da zuma a shagunan cikin gari.
Intermediate Technology 12
12 Page 13
Radio
Vol II No 7 June 1999 [Hausa]

13
CHANGE
Kalmomin Da Aka Yi Amfani Da Su
W. W. F : Gidauniya Kula Da Gandun Daji Ta Najiriya Afrika
C I P R : Cibiyar Nazarin Noman Dankali
D N A : Kwayoyin halitta gane dangantakar haihuwa
D. R. C: Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.
E. U: Kungiyar alummar Turai.
F. A. O: Hukumar abinci da aikin gona.
F D A: Hukumar kula da abinci da magunguna.
JECFA: Kwamitin hadin guiwa na kungiyar Lafia ta duniya da hukumar abinci da aikin gona a kan tabbacin Lafiyar maganin dabobi.

W. H. O.: Hauukmar Lafiya ta duniya
W. T. O: Kungiyar ciniki ta duniya. 13

Page Navigation Panel

1 2 3 4 5 6 7 8 9
10 11 12 13

 

© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw