Document Body Page Navigation Panel
1
Cigaban Kasa
TATTALIN ARZIKI
Bukata: Kyakkyawar Manufa, Ba Agaji Ba 1min 53 secs 5
Kasashe masu tasowa dake bukatar agaji, zasu fuskanci mawuyacin
hali wajen samun agaji daga kasashen dake bada taimako na duniya.
Shin Gwamnati Tana Kashe Abunda Ya Kamata? 2mins 8 secs 3
Abinda Gwamnati take kashewa domin cigaban kasa, kwalliya bata
biyan kudin sabulu kan tattalin arkikin kasa.
Kasashen Gabashi Sun Sami Agaji Fiye Da Na Kundanci A Shekarun 1990s
2 mins 26 secs 4
An kawo karshen mahawararda ta mamaye wadan nan shekaru
MATA
Shekaru Biyar Bayan Taron Beijin 1min 38 secs 14 Mata sun matsawa
gwamnati lamba a karon karshe domin kawo
karshen nuna bambancin da akeyi tsakanin maza da mata.
Birnin Da Akafi Yiwa Mata Fyade A Duniya 1min 31 secs 15
Afrika ta kudu ta cira tutar cin zarafin mata a duniya.
Tozartar Da Mata a Sassa Daban-Daban Na Duniya 1min 26secs 14 Munanan
rahotanin cin zarafin mata a wasu kasashen duniya
KWADAGO
Ma'Aikata A Kasar Mali Sunyi Nasarar Samun
Karin Albashi 3 min 30 secs 8 Ma'aikatan Mali sunyi nasara kan yajkin
aikin da sukayi
Kungiyoyi 2min 17secs 13
Kugoyoyi masu zaman kansu, suna kalubalantar kokarin da
Gwamnati keyi na matse su.
Yanahin Muhalli
Tsarin Kula Da Kare Muhalli 15secs 13 Rashin Sani da bambanci na barazana
ga tsarin muhalli
Madagasca Ta Kaddamar Da Sabon Gandun Daji Na Kasa 3 mins 11secs 10
Yanki kudu maso gabashin Madagasca yakai ga wurin yawon bude ido
Muhimman Hotunan Hallitu A Na'urar Zamani 1min 30 secs 3
Yanzu za ka iya ganin muhimman hotunan hallitu iri-iri ta hanyar
amfani da na'urar Internet.
Saran Itatuwa Ba Bisa Doka Ba Na Barazana Ga Dazuzukan Tanzania 2mins
19 secs 6
Gandun da jin kasar Tanzania da yakai kadada miliyan 33 na fuskantar
karuwar barazana. 1
1 Page 2 3
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
2
Gurbacewar Yanayi 2mins 13 secs 5 Kasar filifins na dubar sabo sabuwar
dabarar kula da shara manila ta
dukufa wajen samo sabuwar dabarar sarrafa shara, ganin tschuwar
dabarar da take bi ta citura
NAMUN DAWA
Ghana Na Fama Da Raguwar Kifi Cikin Hanzari 4 mins 7 Karuwar dabarun
kamun kifi irin na zamani ya sanya yawan kifin da
Ghana ke dasu na raguwa wasu irin ciyayi masu dafi na barazana ga
filaye a gabashin Afrika Ciyayin da aka sansu a sashin gabashin Afrika
yanzu sun fara mutuwa saboda wata irin ciyawa mai dafi.
Sashin Yara
Lokutan Da Bauna Ke Farauta 5mins 10 secs 11
Hadama ta sanya Bauna ta rasa rawanin sarautar sarkin Dawa ga Zaki.
Rezar Mikiya 2mins 7 secs 13
Mikiya da Hankaka da kawaye ne amma saboda batan reza, sai suka bata.
Meyasa Kuma Yaya Ne Jalbe Ke Yin Kofa A Busashen Itace 1 min 2 secs 12
Sadu da tsun tsun dake huda busashen itace domin yin gida.
Ta yaya Karkanda ke kare kan sa DagaAbokan Gara? 1 min 11sec 12 2
2 Page 3 4
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
3
Labaru
Gwamnati Tana Kashe Abu Mai Kyau? 2min. 8secs Zai baiwa akasarin 'yan Afrika
mamaki da jin cewar kudaden da Gwamnati ke kashewa na tauye cigaban
tattalin arziki. Binciken da wata kungiya dake Biritaniya mai suna kungiyar
nazarin cigaba DSA ta gudanar ya nuna cewa kashe kukaden Gwamnati kan aiyukan
da ba na samar da kayayyaki ba ko na cin jama'a ba
na dakile tattalin arziki. Wannan kuwa yafi baiyana a kasa irin Najeriya, inda
harkoki duk sunfi ta'allkewa kan kwangila daga gwamnati. Kwangila na karfafa
gwiwar shigo da kaya waje, kamar kayan aiki da
kwaraun da zasu aiwatar da aikin. Domin haka tattalin arziki baida wani tasiri
akai.
Binciken kan tattalin arziki an gudanar dashi ne a kasar Tanzaniya kasar da
ta zama zakaran kwaji, wadda
take fafutuka duk da irin bukatun jama'ar ta dakuma dan arzikin ta kalilian.
Daga cikin irin abinda binciken ya gano sun hada da, kashe kudade a kasashe
masu tasowa na tattare da gibin kasafin kudi, dakuma nawa
kan cigaba. Haka kum, a nazarin ya gano cewa rage kashe kudin gwamnati zai
taimaka wajen bunkasuwar tattalin arziki.
Nazarin ya gano cewar akwai wasu manyan hanyoyin kashe kudi a kasashe masu
tasowa, kamar, kashe kudi wajen zuba jari, aiyukan da basa tsinana komai dakuma
kashe kudi kan harkokin jama'a..
Daga ciki an gano kashe kudi kan zuba jari shine ke da rashin amfani ga tattalin
arzikin kasashe masu tasowa. Wannan kuwa da mamaki, domin anan ake saran samun
karuwar tattalin arziki, amma maimakon
haka shi yafi dakile tattalin arzikin. Amma kashe kudi kan harkokin jama'a irin
si. Kiwon lafiya da ilmi sukan kai ga karuwar tattalin arzikin.
Domin habaka tattalin arziki, Gwamnatocin kasashe masu tasowa kamata yayi
su maida hankali wajen bada ilmi da inganta kiwon lafiya. Haka kuma tilas su
karafa gwiwar'yan kasuwa domin zuba jari kan harkokin
kasuwanci. Wannan sabuwar canjin maufar kamati yayi a bita da yekuwar samar
da yanayi mai kyau wanda zai janyo hankalin masu zuba jari daga waje.
ID21/ Obasi Ogbonnaya
Muhimman Hotunan Halittu A Bukin Baje Koli 1min 30 secs Sama da hotuna
dubu goma ne na halittu iri-iri wata kila shine mafi girma da ban mamaki a duniya
nan gaba
kowa zai gan su a ko ina kake a duniya da zarar ka matsa butur. Wannan kuwa
hukumar kare hallitu ta duniya WWF da kamfanin na'urar kasuwanci ta duniya CANON
ne zsau samar.
Wajen bukin baje kolin litattafai na musamman a Frankfurt ranar 15 ga Oktoba
kungiyoyin biyu zasu kaddamar da abinda suka kira bisa tsarin hotunan muhalli.
Hotunan zasu kai ga jama'a ta hanyar na'urar
Internet kafin tsakiyar shekarar 2000.
Amma kugiyar kula da muhalli tana iya yin amfani da hanyoyin ta na cikin gida
domin kiran Internet wajen samun hotunan domin fara aiyukan ta, na ilmantarwa
da kuma na yekuwa. 3
3 Page 4 5
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
4
Hotunan sun kunshi dubban hotunan da akayi ta dauka ne tun shekarar 1964, wadanda
wasu masu daukar hoto su dari biyar sukayi a sassa daban daban na duniya. Sanarwar
da aka bayar game da hotunan tace
wannan somin tabi ne daga abinda zai biyo baya. Hotunan sun kunshi yekuwar muhalli
da aiyuka da
hatsarin da wasu halittu ke fuskana da irin matakan da yanzu haka ake dauka.
Wannan zai kara bisa sabuwar hanyar da aiyukan WWF ke samarwa ga kwararu kan
aikin watsa labarai a duniya inji sanarwar.
WWF
Kasashen Gabas Sun Sami Agaji Fiye Da Na Kudanci A Shekaun 1990s 2min.
26secs.
Fargabar da kasashen Afrika da sauran masu tasowa keyi na cewar agaji zai
koma gabashin Turai bayan faduwar taryyar Soviet ya tabbata. Tabbacin kuwa yazo
ne kusan shekaru goma bayan da kasashen Afrika
suka koka, amma kasashen turai suka ki yarda.
Tabbacin yazo ne cikin kasidar da aka gabatar. Kasidar tayi kan babban dalilin
canja alkibla wajen bada agaji da Kasashen Turaix dake bada agaji tattalin arziki
(OECD) sukayi a shekarun 1990s. Ta baiyana
cewar akwai raguwar bayar da agaji daga kungiyar (ODA) daga kudanci zuwa gabashin
Turai saboda a wannan lokacin kungiyar bayar da agaji ta OECD ta karkata hankalin
ta.
Akasarin kasashe masu tasowa ana dangantasu ne da kasashen dake kudanci domin
suna kudu ne da layin da ya raba duniya gida biyu.
Rahotanin hukumomi daga kungiyar ta OECD sun nuna cewa babu canjin alkibla da
aka samu tsakanin
1990-94 zuwa gabashin Turai, amma agaji zuwa yankin na gabas na kara samun sa
ido. Saidai kuma wasu rahotanin suncecanje-canje sun inganta yadda ake bayar
da agajin daga afrika zuwa gabashin
Turai dakuma yawan raguwar bayar da agajin da ake baiwa kasashen Afrika.
Haka kuma kungiyar nazarin cigaban kasar ta gano cewa anyi canji a hukumar OECD
kan ma'anar agaji ta
yadda zai kunshi taimakon warware matsalolin dake cima duniya tuwo a kwarya.
Wannan kuwa ya sabawa hanyar da aka saba bi wajen bayar da agaji domin cigaban
kasa. Wannan canji bisa sabuwar gabar da ta
bulla bayan yakin cacar baki tsakanin kasashen dake bayar da agaji sun isa
dalilan da ya sa suka rage bayar da agaji ga kasashen dake kudancin duniya.
Kungiyar ta bada shewarwari kan matakan da za abi domin shawo kan matsalorin.
? A raba kudaden taimakon warware matsalolin dake addabar da kudin da aka bayarwa
domin aiyukan raya kasa.
? Haka kuma kungiyar OECD na iya canja ma'anar agajin raya kasa ta yada zai
hada da kudin da
ake bayarwa domin warware matsalolin dake addabar duniya. ? Da kuma kyale jami'an
bincken kudade masu zaman kansu surika binciken kudaden da aka samu
daga kasashe masu bada maimakon kasashen da suka bada agajin surikayi da kansu
. DSA 4
4 Page 5 6
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
5
Kasar Filifin Na Dubar Sabuwar Hanyar Sarrafa Shara 2 mins 13 sec Birnin
manila hedkwatar kasar filifins dake kudu maso gabashin Asia ta kafa doka abota
wajen sarrafa
shara ga mazauna. Birnin. Dokar ta bukaci dukkan masu daukar shara da su raba
jakunan sharar zuwa
launi hudu. Bakar jaka domin daukar dottin da bai shafi magunguna ba, Tsanwar
jaka dottin makanikai jar jaka dattin masana'antu mai guba jaka mai launin rawaya
domin dottin da bai danganci magunguna cutuka
masu yaduwa,. Wadanda za arika tarawa a wurin tara sharar brinin.
Wannan sabuwardokar tazo ne a daidai lokacin da wuraren tara sharar manila ke
cika kuma ana kokarin
rufe suba akuma samu wasu sabbin wuraren tara sharar ba wani jami'in huumar
raya birnin manila ya bukaci dokar da ta rika sa ido wajenzubar da sharar domin
kaucewa matsalar dake tattare da hakan.
Masu hangen abinda kaje yazo sun soki wannan sabuwar dokar wanda suka ce bata
da tasiri. Sunce dokar bata fayyace hanyoyin da za a sarrafa sharar ba. Manila
dai na kona sharar da ake tarwa ne yayinda kuma
ake binne wasu a kasa. Amma hukumomin birnin sun kuduri aniyar daina amfani
da hanyar kona shara yazuwa shekara ta 2003, wanda zai bukaci samar da ma'aikatun
sarrafa sharar.
Sauran matsalolin da dokar ke fuskanta sun hada da kudin da masu gidajen zasu
rika sayen jakuna masu launi kimanin dalar Amurka daya kan jakuna 20, da kafa
wurin ajiye shara dakuma hukuncin da za arika
yiwa duk wanda ya fidda jakunan sharar kafin isowar motar daukar sharar ta iso.
Tarar tana kamawa ne daga dalar Amurka 25 ko daurin wata shida. Duk da wadan
nana matsalolin akasarin masu gidaje sunce
tuntuni yakamata wannan dokar ta fara aiki. Suna fatan hakan zai karfafa gwiwar
tarawa da sake sarrafa sharar dakuma binnewa a karkashin kas. Kamata yayi wasu
biranen Afrika suyi nazari da wannan sabuwar
dokar ta manila domin wasu daga cikin sassan dokar zasuyi amfani ga kasashen
Afrika.
Abin Bukata: Kyakkyawar Manufar Tattalin Arziki Ba Agaji Ba 1min 53 secs
Kasashe masu tasowa Zasu fuskanci wahaloli wajen samun taimakon kasashen
duniya domin habaka
aiyukan su na raya kasa a nan gaba. Tilas su tsammaci taimako kalilan na kudi
tare da koyon darasi mai yawa kan manufofin da za subi wajen kara inganta tattalin
arziki su daga kasashen dake bada taimako.
Wannan kuwa yabiyo bayan sanarwar da Bankin duniya ya bayar kwanan nan ne,
inda yace agaji na tafiya ne tare da kyawanan manufofin tattalin arziki. Akasarin
Kasashen dake bada agajin kuwa suna samun ka
'idojun aikin su ne daga shi Bankin duniya.
Binciken da jami'ar Nottingham ta gudanar kwanan nan, karkashin jagorancin sashin
kula da aiyukan raya kasa na duniya dake Biritaniya ya goyi bayan shawarar ta
Bankin duniya. Binciken ya nuna cewa rashin
daidaito ga agajin da kasashe ke samu yafi ga cigaban tattalin arzikin su.
Taimakon kudi a koda yaushe anayi ne da nufin zuba jari, amma masu zuba jari
suna fargaba in har agajin
bai zuwa a kan kari, inji Oliver Morrissey, wanda yana daya daga cikin wadanda
suka bada rahoton. Yawan rashin cigaban tattalin arziki. Binciken yayi kuma
nazarin dagantakar dake tsakanin rashin tabbas
wajen bada agaji da cigaban tattalin arziki tare da misalai daga kasashen
88 masu tasowa.
Kamar yadda nazarin ya nuna rashin tabbas ga agaji zaishafi tattalin arziki
a hanyoyi biyu. Na farko yana iya
nuna kasa bata da daidaito kan cigaban tattalin arziki irin yunwa. Ko ambaliya
ko rashin daidaito kan farashin kayan abinci. Na biyu rashin daidaito na iya
dagula manufar zuba jari ga kasa. 5
5 Page 6 7
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
6
Bugu da kari kuma binciken ya nuna rashin tabbas na rage kaifin samun agaji
dakuma marowar tattalin arziki.
Daga cikin matakan da aka gabatar domin gyara sun hada da inganta manufar tattalin
arziki a kasashen dake karbar agaji, da samun kasashe zaunanu dake bada agajin
dakuma bada fifiko ga kasashen dake kokarin
daidaita harkokin su na tattalin arziki. ID2/ Obasi Ogbonnaya
Sare Itacen Katako Ba Bisa Doka Ba A Tanzania Na
Barazana Ga Dajin Kasar 2mins 19secs Tanzani na asarar kimanin kadada dubu
dari biyar na gandun dazuzukan ta masu amfani kowace shkara
saboda masu sare itacen katako. Wannen kuwa kamar yadda aka buga a wata jarida
da akayiwa lakani 'Sare Ka Gudu' Sare katako ba bisa doka ba da sana a katako
a yankuna mai zafi, jaridar tace jami'an
Gwamnati suna daga cikin masu irin wannan laifi wanda ya sanya kasar mai kadadamiliyan
33 da dubu dari
biyar cikin hatsarin gaske.
Sare gandun dazuzzuka ba bisa doka ba da cin hanci da jami'an gandun dazuzzuka
keyi da na jami'an kostom suna daga cikin abubuwan dake fuskanta har ma da kasashe
irin su Kenya da Senegal, da Ghana
da Naijeriya dakuma Camerou.
Jaridar tace Tanzaniya bata da kuzarin tabbatar da kare gandun dazuzukan ta.
Da yake maida martani bisa wannan rahotan Firayi Ministan Tanzaniya Fredrick
Sumaye ya sha alwashin sanya kafar wando guda da
dillalan katako ba bisa ka'ida ba.
Babban sakataren ma'aikatar albarketun kasa da yawon bude ido Philemon Luhanjo
yayi na'am da cewar wasu jam'an gandun daji suna da laifi kan cinikin katako
ba bisa doka . Haka kuma ana zargin su da hada
baki wajen cutar da dabbobin dake gandun daji sai dai yaki yarda cewar jami'an
dake aiki a shain kula da dabobin dawa suna taimakawa masu cinikin fatun dabbobin
ta hanyar kungiyar mafarautar Tanzaniya.
Sauran wadanda ake zargi bisa wannan sana'ar dillalan katako da masu sarrafa
katakon da sauran mutanen
dake aiki a kamfanonin sarrafa itatuwan katako.
Luhanjo yace haka ma ana digba cuta a kusan dukkan kassar a dazuzukan da aka
kebe da wadanda bia kebe ba. Wadanda ake zargin suna gudanar da aikin sune domin
samar da katako ko itacen wuta ko
gawayi.
A kokarin ta na hana irin wannan ta'asa, hukuma ta fara neman taimakon mazauna
karkara dake kusa da gandun dazuzuka. Kuma saboda rashin zabi domin samun makamashi
irin wadan nan mazauna karkara
suke sare itatuwa domin yin girki. Yanzu ana ilmantar dau kan yadda zasu taimaka
wajen kare gandun dazuzuka maimakon lalatawa domin amfani na dan takadirin lokaci.
Haka kuma 'yan sanda na sintiri akan manyan hanyoyi danufin tsare wadanda
ake tuhuma dakuma kwace abinda suka dauka.
Enviromental News Network 6
6 Page 7 8
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
7
Ciyawa Mai Guba Na Barazana Ga Ciyayin Gabashin Afrika 2mins 12 secs Yankin
kasar gabashin Afrika dake da dausayi da ciyayi masu kyau, dake kula da dabbobin
dawa yanzu
yana fuskantar barazana daga wata irin ciyawa mai guba.
Ita wannan ciyar da ake kira Tarcharantus dake yaduwa a kasa tana daidai da
irin kainuwar nan dake addabar kogunada koramai a yankin Africa ta yamma yau
kusan shekaru kenan.
Ciyawar tana saurin yaduwa a wannan yankin kasa kamar yadda rahoton da aka
bayar kwanan nan a
jaridar kasar Kenya, ciki kuwa harda yankunan dake da duwatsu da kwazazafai
inda take girma tare da jijiyoyi masu karfi, wanda ke tauye albarakatun kasa,
kana sauran ciyayin basa iya jure mata musamman
ciyayi da akeyin magunmaguna dasu.
Ciyawar Tachanantus camphoratus wanda kabillar Msai ke kira 'leleshwa' an fara
ganin ta ne kimanin
shekaru 30 da suka wuce. Masana harkokin karkashin kasa sunce ciyawartana da
wata irin baiwa na sabo da duk yanayin da ta sami kanta ciki, kana kuma bata
da amfani. Tana kashe sauran ciyayi kuma ba a
amfani da ita dabobi ma basa cin ta.
Masanan sunce ciyawar ta karu har sau hudu tun daga lokacin da aka fara ganin
ta shekaru 30 din da suka
wuce, india ta mamaye fili mai fadin kadada dubu dari da talatin a Kenya, kadai
akasari a yankunano dake da kwazazzafai. A Laikipia dake yankin arewa ta tsakiyar
Kenya yaduwar ciyawar ta tilastawa dabbobin
dajin zuwa bakin sashin da ake kare su wanda hakan ya sanya ake samun matsala
tsakanin dabbobin da masu dabobin gida asboda neman abincin da zasu ci. A yankunan
da ciyawar ta leleshwa tayi kakagida
kuwa dabobin dake yankin duk sun bace baki daya.
Wasu masana karkashin kasar sunyi gargadin cewar, in har ba ashawo kan leleshwa
ba wsu sassan yankin savahna na gabashin Afrika Zasu Zama sahara. Amma kuma
akwai alamun dake nuna cewa ciyawar tana
da maiko a jikint, masana kimiya na bincike kan yadda za a sarrafa ta domin
kasuwanci. Wannan shi ya sanya ake saran ciyawar za a shawo kanta domin noman
ta a nan gaba.
AWF Wildlife News
Rahonti
Ghana Na Fuskantar Raguwar Kifi Cikin Hanzari 4 mins Masana'an tun kamun
kifi na kasar Ghana suna fuskantar mawuyacin hali saboda yadda mazauna bakin
ruwan kasar ke kamun kifi baji-ba-gani a sakamakon fasahar zamani na kamun kifi
a teku. Alamar farko na
wannan matsalar ta fara kunno kai ne a irin bukukuwan kamun kifi da aka saba
yi a yankunan dake bakin ruwa inda ake shirya kayan abincin da akayi dashuwa
da kifi iri-iri.
Baya ga iska mai sanyi babu kuma wata hujjar dake nuna cewar bukin kamun kifi
yazo ya wuce kamar yadda wani dan rahoton kasar Ghana ya bayar. Yace dukkan
bukukuwan kamun kifin kasar sun zi har sun
wuce babu kifin dake tukunya koda karfasa ne. Ba da jimawan nan ba ne bukin
kamun kifi na herring mastina ke sake maida kifin da suka kama cikin teku saboda
rashin kasuwa. 7
7 Page 8 9
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
8
Domin baiyana tsananin karancin kifin har yanzu an shiga tsatubar al'ada. Masinta
dake kauyukan dake kusa da brinin Accra sun dora laifin rashin samun isashen
kifin ne kar shirin kayyade iyali tsakanin kifayen.
Kauyawan dama can basa son maganar kayyade iyali suna daukar wannan batu danufin
sake komawa bisa
al'adar su ta tuntuni.
Yanzu haka kowani daya daga cikin aiki biyar na dan Ghana na fuskantar barazana
akasarin su'sun shiga aikin kamun kifi ko kuwa said inji mukadashin darektan
ma'aikatar kula da kifi ta Ghana Mr. George
Hutchful, wanda yace babu annuri nan gaba.
Yawan kifin da ake samu sai kara raguwa yakeyi ainun, wanda hakan ya sanya ake
kama kifin da basu kosa ba. Wannan kuwa ya haifar da koma baya ga irin kifin
da ake samu, wanda ya sanya kudin da ake samu
daga kifin ya ragu. Ya kuma dora laifin kan yadda masintaa Ghana basa bin ka'idojin
da aka shimfida wanda suke samar da kusan duk kifin da Ghana ke bukata.
Mr. Hutchful yace kokarin da Gwamnati keyi na bullo da manufar kayyade yawan
kifin da za arika kamawa (TAC) yana samun cikas saboda gasar dake akwai dakuma
ingantuwar hanyoyin kamun kifi irin na zamani.
Yawan kifin da aka amince a rika kamawa kowace shekara a Ghana shine ton dubu
metan da goma. Amma kumma ba abin wannan ka 'idar.
Shekaru goma da suka wuce yawan kifin da ake kamawa yana tsakanin ton dubu
dari uku da hamsin zuwa ton dubu arbamiyya. Mr. Hutchful yace ana kuma shigo
da wasu kifin tondubu dari bakwai daga waje a duk
shekara dominbiyan bukatun jama'ar kasar.
Kifi dai shine babban abincin mutanen Ghana domin samun abinci mai gina jiki
musamman a manyan birane. Wannan matsalar kuwa zata kara tabarbarewa ganin irin
halin da ake ciki. Nan da shekaru 20 masu zuwa
fiye da rabin mutane miliyan 18 da Ghana ke dasu zasu kasance a birane ne. Hakan
inji Mr. Hutchful zai
kara yawan bukatar kifi kenan.
Kungiyoyin masintan kasar sun fara daukar mataki. Yanzu sun fara sanya wakila
kungiyoyi yin yin rantsuwar ba zasuyi amfani da guba ba wajen kamun kifi. Kamar
yadda sarkin tarun al'umar Mumford yace suna
gudanar da rantsuwar ne ta hanyar yin amfani da burkutu, kan wan duk ya karya
rantsuwar to kuwa aljanun
ruwa zasu halakashi. Akwai sama da jiragen kwale-kwale masu inji kimanin dubu
tara wanda rabin su na da na'urar kamun kifi a kauyuka 189 dake farfajiyar ruwayen
kasar Ghana mai tsawon kilomita 550
A nata bangare, Gwamnati yanzu tana duba irin ragar da ake amfani dasu wajen
yin su. Ance kamfanonin Korea ne ke da akasarin jiragen dake kamun kifi a tekun
ruwayen kasar ta Ghana. Wannan mataki kuwa
kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, domin daga cikin biyar ana kame hudu na
tarun da ake dubawa a tashar jiragen ruwan Tema da ma'aikatar kula da kamun
kifi ke aiwa tarwa.
Edward Ameyibor
Ma'aikata A Kasar Mali Sunyi Nasarar Karin Albashi 3 mins 30 secs Ma'aikata
a kasar Mali sun sami karin kashi 7 cikin dari na albashin su bayan nasarar
da suka samu na yajin
aikin da sukayi karkashin babbar kungiyar kwadagon kasar (UNTM). 8
8 Page 9 10
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
9
Yajin aikin ya cimma fiye da karin albashi da ya fara aiki daga watan Oktoba,
haka kuma za a sake duba tsarin albashin ma'aikatan Gwamnati, wanda zai fara
daga watan Janairu shekera mai zuwa. Wata tawagar
kwararu kan tattalin arziki ne zai duba tsarin albashin tare da jami'an Gwamnati
dana babbar kungiyar
kwadagon kasar, wanda Ministan aiyukan Gwamnati Zai zabo su.
Bugu da kari yarjejeniyar da aka kulla da Gwamnati ta tabo wasu sassan kula
da jindadin ma'aikatan ciki harda kula da farashin kayayyakin abinci, wanda
yayi tashin gwauron zabbi da kashi 10 cikin dari a shekera,
da kuma ragi kan kilowatt na wutar lantarki da ma'aikatan na Mali ke saya. Akasarin
yarjejeniyar da aka
kulla sun fara aiki ne batare da jinkiri ba.
Wannan sabon tsarin wanda ya fara aiki nan take yana kara karfafa gwiwa inji
wani wakili a kungiyar kwadagon kasar.
Duk da haka wasu ma'aikatan suna nuna fargabar su kan farashin wasu muhimman
kayan zai tashi nan gaba kadan saboda karin albashin. 'Zamu tsaya muga yadda
'yan kasuwa zasuyi da hajar su game da karin
albashin, domin kuwa in har sun kara farashin kayan su, to kuwa za a koma gidan
jiya ne inji wani wakilin babbar kungiyar kwadagon UNTM, wanda ya sha jinin
jikin sa duk da yabon da jaridun kasar keyi na
cewar wannan babban abin tarihi ne. Ya tuna a shekarar 1994 yadda akayi karin
kashi 10 cikin dari na
albashi saboda rage darajar takardar kudin CF, wanda ya sanya kwalliya bata
biya kudin sabulu ba saboda karin farashin kayayyakin masarufi. Yazuwa yanzu
dai farashin kayan na nan kamar yadda suke ada a
kasuwani.
Mahmoudu Bathily, wanda ke shiga tsakani wajen tattaunawar karin albashin na
UNTM ya bada tabbacin
cewar farashin kayayyaki zai tsaya kamar yadda yake yanzu, kana za a shawarci
Gwamnati in bukatar hakan ta taso domin dakile tashin farashin kayan.
Karin albashin na nufin baiwa ma'aikata damar cin moriyar shirinne, wadanda
yanzu haka suke karkashin matsin lambar. Bazata sabu ba in har farashin kayan
masarufi kamar su masara da hatsi, da man girki da
man gas suka tashi wanda zai shafi irin na nasararda muka samu inji Bathily.
A nashi bangare Sidibe yayi alkawarin ganin cigaba da rike yarjejeniyar da aka
kulla da shugabanin kungiyar kwadagon.
Sauran kungiyoyin ma'aikata ma sunyi maraba da karin albashin, irin su kungiyar
hadin kasa na ma'aikatan Mali (CSTM) wadda taki shiga yajin aikin. Shugaban
CSTM din Amadou Amion Guidon yace koda shike
karin albashin matakin farko ne amma bai wadatar ba ma'aikata zsau cigabada
fafutuka.
Kungiyar ta CSTMtana shirin gudanar da nata yajin aikin domin bukatar kawo karshe
karancin wutar
lantarki, wand ke jefa kasar cikin mawuyacin hali. Haka sumama'aikatan dake
aiki a kamfanoni masu zaman kansu na shirin gudanar da yajin aiki, domin neman
karin albashi, wanda suka kasa samu ta hanyar
tattaunawa.. 9
9 Page 10 11
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
10
Madagasca Ta Kaddamar Daa Sabon Gandun Daji Na Kasa 3mins 11 secs Yanzu
haka gandun dajin Andringitra dake Madagasca ya kammala domin masu yawon bude
ido. An
kaddamar da gandun dajin ne cikin watan Oktoba, kuma anyi alkawarin zai sami
nasara kamar yadda
hukumar WWF take kokarin ganin an kirkiro da gandun dajin tare da wasu kungiyoyi.
Kungiyoyin kuwa sune kungiyar kula da yankunan da aka kebe na kasa (ANGAP),
da Gwamnatin Madagasca dakuma
kungiyar bada agaji ta kasar Jamus, KFW.
Shidai gandun dajin Andringitra na da fadin kadada dubu 31 da 160 yana kwance
ne tsakanin wasu tsoffin
yankuna biyu da aka kebe watau yankunan Ranomafana da Isalo. Daga cikin abubuwan
sha'awar dake ciki sun hada da manyan tsaunuka da dabbobi dakuma yanayi iri
uku, kamar su yankin daji mai yanayin zafi,
da yankin daji mai dausayi da kuma yankunandake da duwatsu da tsaunuka. Kana
wani abin baba sha'awar kuma shine kolouwar dutse mai tsawon mita dubu 2 da
dari 6 da 58 shine kuma dutse na biyu
mafi girma a kasar baki daya kuma yana da mashigi.
Wannan sabon yankin da aka kebe nada wuri mafi kyau da wannankasa na tsibiri
ke iya bugun kirji dashi. Huumar WWF ta fadi cikin sanarwar da ta bayar ranar
8 ga Oktoba' Yankin mafi kyau da albarkatu zai
kuma bada dama gudanar da bincike da yanayi tare da ilmantarwa da ynakunan dake
da duwatsu. ' An tanadi wurare masu tsawo kilomita 40 dakuma wasu sansanoni
daban-daban guda hudu cikin gandun dajin.
Aiyukan da akayi ta gudanarwa a gandun dajin na Andringitra tun 1993 anyi
ne da nufin karfafa gwiwar masu sha'awar au\ iyukankula da muhalli da halittu
a yankunan da aka kebe su. Mazauna yankunan karkara
suna shiga cikin shawarwarin yadda za a tafiya da gandun dajin ta yadda za arika
kulawa dakuma kare yankin.
Shirin kula da dajin na kasa shine na raya yankin domin yawon bude ido, wanda
zai kare albarkatun dake akwai a yankin dakuma taimakawa kan harkokin tattalin
arziki da zaman takewar mazauna yankin, tare da
inganta bukatun al'adun su.
'Baya ga 'yan kalilan na yankin dake sashin kudu da kudu maso yamma na tsibirin
Andringitra yana matsayin samfur na irin albarkatun kasa: ofishin hukumar WWF
a kasar Madagascar Mr. Lantosoa
Ramarojaona.
Fiye da mutane dubu 15 a kauyuka 196 ke zaune yankin da gandun dajin yake kuma
sun shiga cikin aikin
gadan-gadan.
Wata kila babban karfi da aikin ya samu shine goyon bayan da kabilun Betsileo
da Bara dakuma Tanala suke baiwa shirin inji darektan aiyukan Joseph Ralaiarivony.
Yace sun baiwa shirin goyon baya t hanyar
kyalewa a gudanar da aikin a yankunan su bisa al'adun su ta yadda suke kare
gandun dajin. Saboda irin
kudurin da suke dashi ya sanya aikin ya kasaita. WWF 10
10 Page 11 12
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
11
Sashin Yara
Zamanin Da Bauna Ke Farauta 5mins 10secs (Cikin littafin tatsuniya na kabilar
Bushman dake kudancin Afrika, da can Bauna tana cin nama ne kuma
sauran dabobi na tsoron ta).
A wani zamani anyi wata Bauna katuwa mai ban tsoro dake zaune kusa da wani kududufi.
Baunar tana farautar namum daji domin samun abin kalace, tana kuma da wasu kaho
da sauran namun dawa ke tsoro.
Saboda wannan karfin nata ba wadanda suke cika mata ido baya ga Giwa da karkanda.
Wata rana Batunar ta sami zaki na shan ruwa batare da sani ba, Baunar na kokarin
kashe zakin da kahon ta, sai zaki ya durkusa ya roke ta kan ta ji tausayin sa
kada ta kashe shi, Bauna ta yarda Zata kyale shi
amma bisa sharadin cewar, zakin zai zama bawan ta kuma shi zai rika zuwa yana
farauto mata naman da zata rika ci. Zaki ya amine tunda baida wani zabi.
Domin haka Bauna ta cigaba da baiwa zaki umurnin zuwa yi mata farautar naman
dawa wadanda ke kiwe, a wannan dajin yana kawo mata tana ci ko yaushe. Domin
haka Bauna tace wannan tsari yayi mata daidai,
domin sai tayi kwanciyar ta kawai tana hutawa, shi kuwa zaki yana yi mata farautar
namun dawa yakawo mata tana kwance abin ta.
Ranan sai Bauna ta kira zaki ta umurce shi da yaje ya kawo mata dan alfadari
domin shi take kwadayin karya kumallo dashi, nan da nan zaki yaje ya kaso ya
kawo Bauna ta cinye dan alfadarin nan kaf batabarwa
zaki koda dan kashi ba ya taba.
Bayan nan kullum sai Bauna ta umurci zaki da ya kaso mata namun daji dayawa
domin hadama, komai bata baiwa zaki saboda hidimar da yakeyi mata. A halin yanzu
saboda zaki ya maida hankali wajen hidimar
Bauna sai matan sa da 'ya' yan sa duk suka fara galabaita musamman yaran zakin
yunwa ta fara cin su. Yayinda iyalan zaki suke kara ramewa, ita kuwa Bauna sai
kara kiba da karfi takeyi. Har takai ga Bauna ta
fara cin abinci sau biyar kowace rana, inda zaki ke sama mata.
Wata rana Bauna ta sami zaki na kwance karkashin inuwar bishiya. Ta umurce shi
da ya tashi ya shirya zuwa farauta, tunda Bauna tayi kiba ainun dakyar take
tafiya. Haka kuma kahunan ta sun girma sosai.
Yau inji Bauna tace da zaki ina so ka shiga daji ka kaso kowani nau'in dabba
daya dake cikin dajin nan.
Nan da nan zaki ya ga wannan ba karamin aiki bane musamman da ya yanzu duk ya
galabai ta ga rashin hutu. Sai yace ranki dade ai wannan abu ne dake da matukar
wuya kin san ba zai yiwu ba. Zaki yace gashi
kuma iyali na duk sun galabaita, yunwa ta kassara su banda wani lokacin kaina
domin kulawa dasu saboda aikin ki. Domin haka ranki dade nake rokon ki da ki
taimakeni kyale ni haka domin inje in kula da iyali na.
Amma saboda hadama irin na Bauna sai ta fusata taki tausayawa zaki. Tace na
ki kashe ka ne kwanakin baya saboda alwawarin da ka dauka ta fada a fusace.
Domin haka tilas ne ka aikata abinda na umurce ka
da kayi. Nan da nan Bauna ta sanya kahon ta ta karci kasa ta tada kura sama.
11
11 Page 12 13
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
12
Sai zaki ya tashi tsaye. Ya san cewa babu sauran mafita cikin wannan sh'ani
sai ya yanke shawara a zuciyar sa. Yace ya ke Bauna tila ne na aikata abinda
kika umurce ni domin alkawari ne na dauka. Saboda
hadamar ki zan kashe daya daga cikin dukkan nau'in dabobi dake cikin wannan
dajin. Kuma zan fara ne
dake saboda kina daya daga cikin na'in dabbobin.
Domin haka sai zaki yayi kukan kura ya aukawa Bauna a bayan ta ya kafa hakoran
sa jikin ta da wuyar ta kafin kace meyen haka Bauna ta mutu.
Daga karshe zaki da iyalen sa suka sami kansu cikin naman Bauna faca-faca
sukayi ta ci. Kuma tun daga wannan lokaci ne zaki ya fara farautar Bauna. Kuma
darasin da Bauna ta koya daga nan sai ta fara cin
ciyawa ta daina cin naman dabbobi. Kuma Bauna ta yanke shawara kasancewa a garke-garke
maimakon yawo dai-dai, domin kare kansu daga sarkin dawa watauzaki
When Hippo Was Hairy
Dalili Dakuma Yadda Jalbe Ke Huda Bishiya Busashiya 1min 2 secs Jalbe
tsuntsaye ne dake da dogon baki mai kauri da karfi wanda ya hade da kashin kan
su. Haka Allah
yayiwa jalbe baiwa domin ya rika zama a wuraren dake da busasun bishiyoyi.
Yayinda akasarin tsuntsaye na zama ne a gidajen su da sukeyi da ciyayi da gashi
jalbe na gidan sa ne hanyar
yin rami a jikin busashiyar bishiya. Haka kuma suna yin kafofi a jikin bishiyoyin
ta yadda zasu sami damar kama kwari da tsutsotsi domin abinci.
Ana samun nau'in jalbe daban-daban a Afrika ciki harda masu geme da masu filafilai.
Jalbe mai geme an sanshi da yin wasu abubuwa kuma daban da wannan baki nasa.
A duk lokaci da ya fara kada fila-filan nan
nasa to fa yana aikawa da sako ne. Inda yake nuna cewa, n an ne gida na.
Yaya Karkanda Ke Kare Kansa Daga Abokan Gaba 1min 11secs Karkandana da
kananan ido kuma bata cika gani ainum ba don haka yaya take kare kanta? Duk
da haka
Allah yayi musu baiwar ji ainun dakuma sansana wanda yake taimaka musu wajen
rashin gani sosai. Haka
kuma karkanda na amfani da kahon ta wajen karen kan ta da 'ya'yan ta daga farmakin
abokan gaba irin su zaki.
Da yake suna girma ainun karkanda basu cika samun abokan gaba ba. Duk da haka
babu dabbar da zata kare kanta daga maharbi dake rike da bindiga ko mashi ko
tarko. Saboda haka karkanda iri biyu da ake
dasu a Afrika ake farautar su. Sune kuwa farar karkanda da bakar karkanda. Mafarauta
sun fi farautar bakar cikin shekaru da dama inda suke saida kahon ga 'yan kasuwan
kasashen ketare akasari kasashen
Larabawa, inda ake amfani dashi domin maganin gargajiya dakuma wuka . Muddin
ba munyi taka tsan-tsan ba tare da kula da 'yan bakaken karkandan da suka rage,
zamu wayi gari mu rasa su baki daya.
Chogololo 12
12 Page 13 14
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
13
Rezar Mikiya 2mins 7secs Can a wani zamani anyi wanti mikiya dake zaune
a wani kauye tare da kawarta sa hankaka suna zaune.
Wata rana sai hankaka taje wajen mikiya yua same ta ta fara gaishe ta bayan
nan yace na zo ne na ari rezar
ki domin zanyiwa yara na aski. Sai mikiya ta baiwa hankaka reza, kana hankaka
ta koma gida ta askewa ya'yan ta gashi. Bayan da ta kare sai ta ajiye rezar
a wurin da ya dace inda ba zaia bata ba domin maidawa
da mikiya daga bisani. Amma sai karamin dan ta ya dauki rezar ya tafi da ita
waje yana wasa, har ta bata.
Bayan 'yan kwanaki lokacin da mikiya ke bukatar amfani da reza domin yiwa 'ya'yan
ta aski, sai ta je ta
tambayi hankaka rezar ta. Sai hankaka ta shiga neman reza. Sai mikiya da hankaka
basa kawance. Domin in mikiya na wuri sai kaga hankaka ta kidime tana neman
inda zata sanya 'ya'yan ta, kuma sai kaga tana
nema ko ina domin gano rezar mikiya. Shangani Folktales
Sashi Na Musamman
Karin Maganar Muhalli 15secs 'Babu abinda yafi muhimmanci irin karantar
da 'yan baya masu zuwa kyawawan halittu da yanayin dake
akwai tsakanin al'umomin duniya , duniyar dake fuskantar barazanar jahilcin
mutane da bambanci'
Sir Peter Scott (Masani Kan Yanayi)
Kungiyoyin Masu Zaman kansu Na Kokarin Zama Da
Gindin Su A Sri Lanka 2mins 17 secs Kungiyoyi masu zaman kansu a Sri Lanka
sun ja damara domin takawa Gwamnati burki kan yadda take
tauye musu 'yancin hulda da kungiyoyi. Kwanan nan ne Gwamnatin kasar ta kafa
kwamitin kulawa da aiyukan kungiyar bada agaji ta Red Cross ta kasar (SLRC).
Wannankuwa shine karo na biyu da
ma'aikatar kula da walwalar jama'a ta kasar ta kafa irin wannan kwamiti cikin
watan Maris a sakamakon
zargin sama da fadi da rashin iya tafiyar da aiki cikin kungiyar da akayi.
Sabon kwamitin an nada shine bayan da Gwamnati tayi gyara cikin watan Mayu
ga dokar aiyukan sa kai na kungiyoyi masu zaman kansu na shekarar 1980, wanda
akafi sani da dokar kula da kugiyoyi masu zaman
kansu. (NGO)
Kungiyoyi masu zaman kansu sama da 500 ne suka sanya hannu bisa takardar dake
kira ga Gwamnati kan ta soke wannan dokar. Gyaran dokar da kafa kwamitin duk
kungiyoyin sunyi tir dasu, wanda suka ce wani
ci baya ne ga kokarin kungiyoyin.
Doka ta zama shishigi ne cikin harkokin kungiyoyin inji wasu 'yan kungiyaar,
domin dokokin da a ake dasu tuntuni sun isa wajen gudanar da binciken almubazziranci
cikin kungiyoyin tare da hukunta duk wanda aka
samu da laifi.
Fidda mutanen dake rike da mukamai cikin kugiyoyi masu zaman kansu bisa zargin
da akeyi musu tare da
maye gurbin su da wasu mutanen da Ministan kula da ma'aikatar walwalar jama'a
zaiyi kamar yadda akayi a kungiyar bada agaji ta Sri Lanka, zai iya sanya yin
aiki da iko fiye da kima inji sanarwar da wata jarida
mai zaman kanta a Sri Lankan MIRJE ta bayar. 13
13 Page 14 15
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
14
A halin yanzu kuma ana zargin wakilan kwamitin da Gwamnatin ta nada na farko
domin sa ido kan kungiyar bada agajin ta SLRC. Ana zargin su da laifin biyan
kansu wasu makudan kudin alawus, amfani da motoci
kungiyar domin amfanin kansu dana iyalan su haka kuma wasu daga cikin iyalan
wakilan suna bulaguru zuwa
kasashen waje domin karo ilmi, wanda iyalan'yan kungiyar na asali ya kamata
suyi haka, SLRC. BAOBAB
Shekaru Biyar Bayan Taron Beijin 1min 38secs Wakilan Gwamnatoci zasu
hadu a wani taro na musamman na babban zauren majalisar dinkin duniya domin
nazari cikin watan yunin shekara 2000 yadda aka aiwatar da kudurin da aka zartar
a babban taron mata na
duniya da akayi a Beijin kasar sin a shekarar 1995. Duk da haka kungiyoyi masu
zaman kansu da suka shafi mata sun fara kira ga Gwamnatoci da su aika da wakilan
su wajen taron da hujjoji dake nuna cewar
sun soke dokokin dake nuna bambanci tsakanin maza da mata. Biyu daga cikin
irin wadan nan kungiyoyin watau DAIDAITO YANZU dake Washington D. C kasar Amurka
da YEKUWAR KAWO KARSHEN
NUNA BAMBANCI GA MATA CEDAW.
Kirian yabiyo bayan kungiyoyin 'yantar da mata ke fadin cewar irin wadan nan
dokokin suna nan daram da gindin su.
Yekuwar mu zatayi kira ga Gwamnatoci da su soke wannan dokar ko kuwa suyi
gyara domin shekara mai
zuwa, watau shekaru biyar bayan taron Beijin. A wajen wannan taro na musamman
ne za a tabo irin wadan nan dokokin, danufin ganin an aiwatar dasu bawai kawai
fada da fatar baki kawai ba, inji kungiyar
DAIDAITO YANZU.
Wata mace mai fafutukar neman 'yancin mata Brooke Ackerly kuma farfesa a fanin
kimiyar siyasa a jami'ar
California ta kasar Amurka tayi imanin cewar hakkin mata yayi ya shige maganar
dokokin daka nuna bambanci, ya maida hankali kan dalilai dakuma yadda abin ke
shafar keta haddin matan.
www. equality. com
Keta Hakkin Mata a Sassa Daban? Daban Na Duniya India 1min 26secs Wata
yarinya 'yar shekera 10 ta tsallake rijiya da baya, yayinda wata ma'aikaciya
jirgin sama ta ceto ta
yayinda ta ganta cikin jirgi tana kuka.
Ma'aikaciyar jirgin daga bisani ta gano cewar tana kuka ne saboda mahaifin ta
ya saida ita ne ga wani
tsohon balarabe dan kasar Saudi Arabia dan shekaru 60 dake zaune kusa da ita
akan kudi dalar Amurka 240.
KENYA ? A wata makaranta da dalibai ke kwana, wasu dalibai maza su
300 suka shiga dakin kwanar dalibai
mata da karfin tsiya, sukayiwa wasu 'yam mata saba 'in da daya fyade. Goma sha
-9 aka tattake su suka mutu a kokarin da sukayi na tsirar da kansu.
Mataimakin shugaban makarantar daga bisani yace yaran ba sunje ne da nufin jiwa
'yam matan lahani ba. Sunje ne kawaidomin yiwa 'yam matan fyade. 14
14 Page 15 16
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
15
BRAZIL ? Wani mutum da ya furta da bakin sa cewar ya soki matar sa da
wuka da wani farkar ta har lahira
kotu ta sallame shi inda dukkan alkalan kotun maza ne. An sallame shi ne bisa
hujjar cewar ya
aikata laifin ne domin kare martabar sa da wani ke tauyewa.
AMURKA ? An soki wata mace 'yar shekaru 51 har goma sha-9 inda aka
kashe ta. Kuma wani tsohon farkan
ta ne, yayinda take zaune a cikin kotu tana jiran sakamakon shari'ar da akeyi
mata. Wanda har sau
biyu ana watsi da karar da ta shigar domin kare kanta. Equality Now
Hedkwatar Yiwa Mata Fyade Ta Duniya 1min 31sec Yanzu haka dai an baiyana
kasar Afrika ta kudu da cewar itace hedkwatar da akeyiwa mata fyade a duniya.
Wannan kuwa ya biyo bayan kididdigar da aka bayar kwanan nan ne daga kasar,
wanda ta nuna cewa fiye
da kararraki dubu hamsin ne aka samu na yiwa mata fyade cikin shekara guda.
Wata majiyar 'yan sanda tace adadin bai hada da wadanda suka faru bisa rashin
sani ba. Sama da kashi 93 cikin dari na irin fyaden
da ke faruwa ba a shaidawa 'yan sanda, kodai saboda tsoro ko kunya ga wadanda
suka fada cikin irin wannan ta'asar.
Kamar yadda rahoton da aka bayar ta gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) fyaden
na hade da cin zarafi da tozartar da matan.
Cin zarafin da yafi daukar hankalin jama'a shine na wata mace da aka kama aka
rufe mata ido da kyalle, wasu zaratan samari, suka kaita wani wurin sukayi ta
lalata da ita har na tsawon kwanaki biyu, kana
daga bisani suka yarda ita, inda wani mutum ya ganta. Hancin ta ya kone da leban
bakin ta kuma tayi targade a wurare da dama na jikin ta tare da kujewa a duk
jikin ta.
Ma'aikatan kiwon lafiya sun ce tana cikin wani irin mawuyacin hali na jin jiki
zata kuma bukaci yin aiki a jikin ta.
Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu Dr. Jacob Zuma, ance shine mutumin
da yafi nuna damuwar sa kan aikata irin wannan laifin.
Amma masu zargin Gwamnati sunce dalilin da ya sa shi Dr. Zuma Ke nuna damuwa
kan laifin yiwa mata fyaden saboda shima kwanakin baya wasu katti sun auka gidan
sa dake can garin su a lardin Kwa-Zulu
Natal, inda sukayiwa matar sa fyade. 15
15 Page 16
Vol II No. 12
November 1999 (Hausa) CHANGE Radio
16
Kalmomin Da Akayi Amfani Da Su
ANGAP -Kungiyar Kular Da Yankunan Da Aka Kebe Ta Kasa
CEDAW -Yekuwar Kawo Karshen Nuna Bambanci Tsakanin Maza Da Mata
CFA -Kungiyar Kula Da Kudade Ta Afrika
CSTM -Hadiyar Kungiyar Ma'Aikatan Kasar Mali
D. C -Gundumar Colombia
DFID -Ma Aikatar Raya Kasa Ta Duniya
DSA -Kungiyar Nazarin Cigaban Kasa
GNP -Karuwar Kayan Masana'Antu Na Kasa
KTW -Kungiyar Bada Agaji Ta Kasar Jamus
NCRC -Cibiyar Bincike Kan Halittu
NGO -Kungiyoyi Masu Zaman Kan Su
ODA -Aiyukan Agajin Raya Kasa
OECD -Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki Da Raya Kasa
TAC -Adadin Da Aka Yarda Kamawa
UNTM -Kungiyar Kwadago Ta Kasar Mali
U. K -Hadadiyar Daular Biritaniya
U. S. D -Dalar Kasa Amurka
UWEP -Shirin Kauda Shara Na Alkari'a
WWF -Asusun Kare Halittu Na Duniya 16
© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw