Go Back
Communicating for Change

Document Body Page Navigation Panel

Pages 1--15


Page 1 2
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

1
Ga Abubuwan Dake Ciki
Locaci Shafi
Kudancin Afrika na fuskantar matsalar cutar kanjamau
1min. 45secs 6
Kimanin mutane dubu 50 ke kamuwa da cutar kanjamau
a Afrika ta kudu kowani wata.

Afrika na fuskantar yunwa 1min. 37secs 3 Yake-yake, kamfar ruwa da kwari suna sayawa abu
mawuyaci ga kasashen Afrika wajen ci da kansu

BUNKASAR ALKARI'U CIKIN HANZARI A AFRIKA
Alkari'un Afrika suna bunkasa cikin hanzarin fiye da sauran kasashen duniya 21secs 13

Afrika na samawa kanta kasuwa 2min. 45secs 7 Afrika na shirin jayo hankalin masu zuba jari na duniya
Gibi Tsakanin Maza da mata kan ilmi a makarantun
Afrika
46secs 13 Yaran maza ke shiga makarntu fiye da mata a yawancin

kasashen Afrika

Sabon Maganin kare jarirai daga cutar kanjamau 1min. 32secs 6 Sabon maganin da aka samu a Uganda da Amurka na
bada kwarin gwiwa ga 'yan baya masu zuwa

Azabtar da yara ya zama ruwan dare a Uganda 2min. 3secs 10 Yara a kasar Uganda suna fusukantar bakar azaba
daga iyayen su

Mata da yawa ke zaman jarun a kasar Sudan 1min. 53secs 5 Cinikin barasa ya jefa matan kudancin Sudan
dubbai gidan jarun a kowace shekara

Bacewar halittu a Duniya 2min. 45secs 7 'Yan baya masu zuwa bazasu gafarta mana ba
saboda halakar da wasu halittu da jama'ar yanzu keyi.

Za'a gabatar da wani shirin kare kogunan turai 1min 11secs 5 Hukumar WWF ta shirya kaddamar da yekuwar kare
kogunan kasashen turai.
1
1 Page 2 3
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

2
Kasar Canada na da muhimmanci kan gandun dazuzzuka a duniya 26secs 14
Kimanin kashi goma cikin dari na gandun dajin
duniya na kasar Canada

Matsalar karancin ingantacen ruwa 14secs 13 Kusan kowani mutun guda daga cikin mutane uku
a duniya zai fuskanci matsalar karancin ruwa nan
da shekaru 50

Shinkafaa mai yawa da ruwa kalilan 2min. 34secs 8 Rashin isashen ruwan sama a duniya na jefa noman
shinkafa cikin mawuyaci hali, masana kimiya na
samo sabbin dabarun noma da ruwa kalilan.

Zanzibar ta haramta shigo da kifin tabki 1min. 50secs 4 Zargin yin amfani da guba ya sanya an haramta shigo da
danyen kifi da ake kamawa daga Tabkin Victoria a
gabshin Afrika.

Najeriya ta kafa sabbin Gandun Dazuzuka 51secs 3 Wasu gandu dazuzzuka biyu an maida su na kasa

Italiya na daukar Tsauraran matakai kan masu cinnawa dazuzzuka wuta 44secs 13
Italiya ta kuduri aniyar dakatar da masu cinnawa
gandun dazuzzuka wuta

Tauraron dan adan zai iya gano alamar barkewar annobar zazzabi 2min. 7secs 9
Bayanin tauraron dan adan zai taimaka wajen kare
mummunar annobar dabbobi.

Tsuntsayen dake sanin lokaci 59secs 14 Masana sun gano abin mamaki a kasar Indonesia

Zaki da bera 10 Aikata alheri
Meyasa jemagu ke tashi da dare? 1min. 5secs 11 Jemagu suna gani da dare
Mumunar laifi da kadima kurege ya aikata 4min. 10secs 11 Gano dalinlin da yasa damisa ke farauta ita kadai 2
2 Page 3 4
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

3
Labaru
Afirika na fuskanta yunwa 1min. 37secs
Sama da mutane miliyan goma daga kasashen Afrika goma sha-6 ne ke bukatar taimakon gaggawa na kayan
abinci domin kaucewa yunwa. Wanan kuwa na kunshe ne cikin bayanin da hukumar kula da abinci da aikin
gona ta duniya dake birnin Roama ta bayar.

Yakin basasa, kamfar ruwa da kwari, sune suka gurgunta aiyukan samar da abinci a sashin Sahara na Afrika,
inda dubban daruruwan mutane ke fuskantar barazanar yinwa inji hukumar a ranar 16 ga watan Agusta.

Ance kasar Angola ce barazanar tafi muni, inji jami'in hukumar ta abinci Mrs. Mwita Rukandema, wadda tace
kazancewar yaki kwanan nan tsakanin dakarun Gwamnatin Angola dana 'yan twayen kungiyar UNITA, ya
sanya baby damar kai duk wani taimakon kayan abinci ga jama'ar da suka gudu suka bar gidajen su a sandiyar
fadan.

Dakarun na UNITA, wadanda aka bada rahoton cewar su nayiwa motoci kwanton bauna tare da harba
mayan makamai a manyan garuruwan kasar.

Jami'ar Rukandeman tace in har wannan hali ya cigaba man da watani biyu, za a ji mugun labari game da
matsananciyar yunwa.

Rukandema tace hanya guda da za'abi domin kaucewa wannan bala'i, itace ta matsawa dakarun Gwamnati
dana 'yan tawayen lamba, domin kyale yin amfani da jiragen sama, sauka a wasu filayen jiragen same 'yan
kalilan wajen kai kayan abinci da magunguna.

Dayawa daga cikin 'yan kasar ta Angola da baki 'yan kasashen waje da sukayi kokarin kai kayan abinci, 'yan
twayen su kashe su.
Africa News On Line.

Nageria ta kafa sabbin gandun dazuzuka 51secs
Ranar 3 ga watan Agusta Gwamnanti Najeriya ta kaddamar da gandun dajin Okomu dake kudancin kasar da
gandun dajin Kamuku dake arewacin kasar a matsayin gandun dazuzuka na kasa. 3
3 Page 4 5
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

4
An kafa gandun dajin Okomu nee shekaru goma sha-5 da suka wuce dake gandun dajin a matsayin na gwaji,
wanda hukumar kula da dazuzuka na Najeriya, wanda ke karkashin hukumar kare dabbobi da halittu ta duniya
(WWF). Gandun dajin dake da fadin kilomota dari da goma sha-2 murabba'I, wuri ne dake da dausayi da
tsuntsaye iri-iri dakuma namun daji iri-iri ciki har da giwaye dakuma birra masu farin wuya.

Wanan kuwa gagarumin ci gaba ne da aka samu inji darektan kula da gandun dazuzika na kasa, Alhaji Lawan
Marguba.
Paddy Ezeala/ WWF

Zanzibar ta haramta su a tabki 1min 50 secs
Kasar Zanzibar ta harmta shigo da kifin da aka kama daga Tabkin Victoria, watanni biyu bayan kungiyar
kasashen Turai ita ma ta haramta shigo da irin wadan nan kifin daga yankin, a sakamakon rahotanin da aka
bayar na cewar masintan yankin na amfani da guba wajen kamun kifin.

Cikin sanarwar da Ministan gona da, raya dabbobi da albarkatun kasa, tace anyi haka ne domin kare masu cin
kifin ciki harda masu zuwa yawon bude ido dakuma tattalin arzikin tsibirin.

Burgediya-Janar Adam Nwakanjuki yace koda shike babu tabbas kan ko tabkin na Victoria ya gurbace da
guba, kasar Zanzibar ba zata yi kasadar kasancewa wurin da za a rika jigbe kayan abincin da suka lalace ba.

Haramcin wanda ya hada da kifin da aka samu daga kogin Nilu ya biyo bayan yadda ake kara samun irin
wadan nan gurbatatun kifayen daga kogin na Nilu. Yanzu haka Gwamnati ta sanya jamian da zasu rika sa ido
a tasoshin jiragen ruwa dake tsibirin dakuma tasoshin jiragen sama da Otel-Otel dakuma manyan kantunan
ciniki irin na zamani, danufin hana shigo da kifayen da ake samu daga tabkin na Votoria da kuma kogin na Nilu.

Wani babban jami'in hukumar kula da yawon bude ido na Zanzibar yace duk Otel din da aka samu yan amfani
da wadan nan kifin, za a soke lasisin sa. A makon jiya ne Gwamnatin Tsibirin ta umurci dukkan otel-otel din da
suke da kifayen na kogin Nilu da su lalatasu.

Haramta sigo da kifaye daga Gudarin kasar Tanzania da Kenya dakuma Uganda yazo ne makwani uku kacal
bayan da Zanzibar ta haramta saida wani irin ruwan kwalba da ake kira MASAFI, wanda akeyin sa a Dar es
Salam. Gwamnati Tsibirin tayi ikirarin cewar kwajin da aka gudanar daga jamin'an kula da harhada magunguna
an gano cewar ruwan bai dace jama'a su sha ba.
Africa News On Line 4
4 Page 5 6
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

5
Shirin kare kogunana turai 1min 11secs
Za afara wani gagarunin shirin kare kogunan kakashen Turai daga wannan watan na Satumbar 1999. Shirin
wanda akayiwa taken 'Rayayyun Koguna' zai kunshi dukkan nhiyar, wada hukumar kare halittu da dabbobi ta
duniya WWF zata aiwatar. An tsara shirin ne ta yadda za a wayarwa da jama'a kai su san muhimmanci da
aiyukan koguna tare da nuna irin barazanar da suke fuskanta saboda rashin kulawa tare kuma da irin rawar da
jama'a da kungiyoyi zasu taka wajen kula da ruwa.

Kamar yadda hukumar ta WWF ta fadi shirin yekuwar zai samarwa da kogunan na Turai da tsarin kula tare da
manufofi na kwarai.

Za'a kaddamar yekuwar ne a Brussel ranar 21 ga watan Satumba, a halin yanzu kuma za a kaddamar da wani
littafi mai warka 20 a karshen watan Agusta, wanda ke da taken RAYA KOGUNAN TURAI. Tsarin sha
yanzu magani yanzu. Shirin na sha yanzu magani yanzu, zai kalubalanci kungiyar kasashen Turai, Gwanmatocin
kasashen da kananan hukumoni masana 'antu da 'yan kasuwa, masu samar da ruwa da sauran kungiyoyin da
ke da sha'awa a wannan fanin, domin daura damara wajen daukar matakan da suka dace, inji hukumar ta
WWF.
WWF

Mata da yawa ke zaman jarun a kasar Sudan 1min 53secs
Sama da mata dubu talatin ne suke zaman jaron na wa 'adi dabab-daban a Sahin Arewacin kasar Sudan inda
Musulmi ke da rinjaye, akasarin su saboda aikata kananan laifuffuka.

Wannan kuwa yafi kashi daya cikin dari na yawan al'umar kasar. Kashi casa'in da biyar cikin dari na wadan
nan matan a daure su ne saboda laifin girka barasa dakuma sayarwa, kuma kusan dukkan su sun fito ne daga
sashin kudancin kasar ta Sudan inda ba laifi bane girkawa ko saida barasa dakuma dirkan sa.

Kamar yadda rahotanin baya-bayan nan ya nuna fiye da rabin adadin Matan an sake kama su ne bayan da aka
sako su. Kayan da ake girka barasan kuwa wasu matane fittatu ne ke sayar dasu da arba ta hanyar gwanjo inji
rahotannin. Matan su kan baron gidan kason ne su je su sayi kayan girka barasan kana su cigaba da sana'ar
ta su da suka saba.

Akasarin matan dai masu juna biyu ne ko kuwa suna shayar da jarirai. Fiye da yara dari a ke haihuwar su a
kowace shekara a daya daga cikin gidajen jarun din, yayinda wani gidan akan haifi kimanin yara dari biyu
yayinda iyayen nasu ke zaman kaso. 5
5 Page 6 7
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

6
Koda shike ance gidajen Jarun na Sudan na daya daga cikin mafiya kyau a Afrika, tuni ake da kira domin sake
tsarin gidajen ta yadda za arika kula da matan da suke fama da tasku a sashin Arewacin kasar saboda al'adar
su ta saida barasa.
Newslink Africa

Sabon maganin kare jariban da iyayen su ke
fama da cutar kanjamau 1min 32secs
An samo wani sabon maganin da zai iya kare jariran da iyayen su ke dauke da cutar kanjamau, kamar yadda
binciken da wasu masana daga kasashen Amruka da Uganda suka gudanar a Kampala da Washington.

Sakamakon farko da aka bayar baya aiyukan bincike na shekaru biyu ya nuna cewar maganin zai kare jaririn
da uwar sa ke dauke da kwayoyin cutar HIV, wanda ke kaiwa ga cutar kanjamau, in har anywa uwa wannan
maganin yayinda take haihuwa dakuma shi jarinrin bayan yayi kwana uku da haijuwa.

Ana cin karfin cutar da kimanin rabin karfin ta ta hanyar amfani da wannan sabon maganin, idan aka kwantata
da maganin AZT-, wanda ke da tsada ninki 70, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Amurka tayi bayani. Wanan
bincike shine mafi muhimmanci da ingaci yazuwa yanzu kan kokarin da akeyi na kare yaduwar wannan muguyar
cutar ta kanjamau tsakanin iyaye mata da jariran su a duniya inji Dr. Anthony S. Fauci na tsangayar kula da
cututtuka masu yaduwa, wanda ta dauki nauyin tafiyar da binciken.

Haka kuma wannan sakamakon ya samu gagarumin marhabin a Kampala. Wannan bincike ya bada kwarin
gwiwar cewar akwai alamun kare jama'ar kasashen Afrika masu zuwa nan gaba daga kamuwa da ita wannan
cutar ta kajamau, inji Ministan kula da aiykan lafiya na Uganda Cripus Kiyonga.
Newslink africa

Sharhi
Kudacin Afrika na fuskantar matsalar cutar kanjamau 1min 45secs
Cutar kanjamau ta fara faskara a kudancin Afrika duk da kokarin da Gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman
kansu da sauran al'umomi keyi na wayarwa da jama'a kai game da matsalar cutar.

Daga kididdigar da aka gudanar ta nuna cewar kasashen Botsuwan, da Namibia da Swizaland dakuma Zimbabwe
sune cutar tafi muni a kudancin na Afrika. Kusan rubuin al'umar kasashen duk sunharbu da kwayoyin cutar ta
HIV ko kuwa cutar kanjamau din baki daya. Kusan rubu'in wadanda suka kamun, mutane ne da shekarun su
ya kama daga goma sha-5 zuwa arba'in da tara. 6
6 Page 7 8
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

7
Kamar yadda Mujallar TIME ta Amurka ta wallafa ma'aikatar lafiya ta Afrika ta Kudu tayi kiyansin cewa,
akalla kashi 20 cinkin dari na yawan ma'aikatan kasar ne zasu kamu da kwayoyin cutar yazuwa badi. Cinkin
shekaru uku man gaba kuma kimanin mutane dubu metan da hamsin ne za su rika mutuwa a duk shekara a
sansadiyar cutar wadda zata bar muatane dubu dari shida marayu. Haka kuma cutar zata rage yawan shkarun
da ake saran mutane za suyi da shekaru ashirin hakan zai sanya tattalin arzikin kasar ya rago da kashi biyu cikin
dari.

Cutar zatayi matukar illa ga tattalin arziki, muddin ba a bullo da kwararan matakai da shirye-shirye ba wadanda
zasu kyautata harkokin kwadago da ingantuwar aiki, kamar yadda rahoton hukumar raya kasa ta duniya
UNDP ta bayar.

Ministan lafiya na Afrika ta kudu Nkosazan Zuma yace mutanen kasar suna kamuwa da kwayoyin HIV cikin
hanzari, wanda a duk wata kimanin mutane dubu hamsin ne ke kamuwa da cutar. Wanan kuwa baban hatsari
ne ga kasar. Hakan ya nuna akwai gyara bisa damarar da kasar tayi na yaki da yaduwar cutar ta kanjamau.
Newslink Africa

Afrika na samun karbuwa kan kasuwanci 2min 45secs
Ganin demukuradiya ta kankama a Afrika, mayan kasashen duniya sai nuna sha'awa sukeyi game da zuba jari
a nahiyar. Cikin watan Oktoba, za'ayi taron kwanaki biyu a Dakar ta kasar Senegal, inda manyan kasashen
duniya da kungiyoyin raya kasa zasu hallara domin tattaunawa. Daga cikin wadanda zasu hallara su hada da
Ministoci daga kasashen Turai da manyan kamfaonin 'yan kasuwa da sugabanin Afrika da Minintocin su na
kudi. Kamar yadda mjallar Newslink Afrika ta ruwaito baki daga kasashen Turai sun hada da Ms. Clare Short
Sakatariyar kula da raya kasashe na Biritaniya, da Mr. Paul Neilson Ministan raya kasashe na Denmak.
Sauran sun hada da Mr. Kenzo Oshima babban darektan tattalin arziki da raya kasashe dake Japan da Ms.
Hilde F. Johnson Ministar raya kasa da kasa da kare hakkin dan adam na Norway.

Haka kuma Ms. Evelyn Kerfkens Ministar raya kasashe ta Netherlands da manyan jami'an kasashen Faransa
da Jamus da Finland dakuma Italiya duk zasu halarci taron. Taron na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar raya
masan'antu la duniya UNIDO, da kungiyar habaka masan'antu ta Afrika (AAI) da hukumar raya tattalin
Arzikin Afrika (ECA) da Bankin raya Afrika (ADB) dakuma kungiyar hada kan kasashen Afrika (OAU).

Daga cikin batutuwan da za a tattauna a taron su hada da tsarin bunkasa masana'antu a Afrika da yanayin
harkokin zuba jari a haniyar dakuma hadin ka yankuna da kawancen kungiyar Tuari da Afika da sha'anin
samar da kudaden kafa kananan masana'antu. 7
7 Page 8 9
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

8
Taron na Oktoba ya biyo bayan yekuwar Harare ne da akayi a shekarar 1997. Yekuwar ta sanya babban
sakataren kungiyar OAU tare da hukumar raya kasa UNIDO da babban sakataren hukumar ECA kan su
shirya taro da manyan kasashen dake bada taimako na duniya ta yadda za a samo hanyoyin samar da kudaden
aiwatar da aiyukan raya kasa na sha yanzu magani yanzu.

Masu shirya taron suna fatar taron zai gaggauta habaka masana'antu a Afrika ta hanya baiwa kasashen Afrika
damar samun sabbin abokan huldar kasauwanci ciki da wajen nahiyar ta Afrika.

Hadin kai ta fuskar fusaha shine babban jigo wajen kyautata yanayi domin zuba jari a kasashen da dama.
Haka kuma zai kara kyautata samar da masana'antu masu karfi na 'yan kasa, wadanda zasu tafi tare da
manyan masu zuba hannayen jari na kasashen duniya, inji rahoton da Newslink Afrika.
Newslink Africa

Shinkafa mai yawa da ruwa kalilan 2mins 34secs
Kokarin gaggawa da akeyi na samar da wata dabarar noman shinkafa tare da ruwa kadan kwalliya ta fara
biyan kudin sabulu. Domin kuwa an samo wata dabarar noman shinkafa mai yawa da ruwa kalilan. Kungiyar
binciken aikin gona da bayar da shawarin kwaruru ta duniya CGIAR ce ta bullo da dabarar samar da dausayi
da ingantacen iri, da kyautata filayo domin noman shinkafar.

Ita wannan sabuwar dabarar ta rage yawan muhimmancin samar da ruwa, domin samun amfani mai yawa kan
kowace dadadar gona. Saidai kuma kungiyar ta CGIAR bata bada dalla-dallar bayani kan yadda sabuwar
dabarar zatayi aiki ba. Duk da haka shugaban kungiyar Isma'il Seragendin kuma mataimakin shugaban Bankin
Duniyan kan aiyuka na musamman yace shinkafa tana bukatar ruwa ninki biyu fiye da kowace tsaba kana
sama da tan dubu biyu na ruwa ake amfam\ ni dashi domin noma tan guda na shinkafa. Wanan yanayi kuwa zai
kasance mawuyaci ganin yadda ake samun koma baya kan samar da ruwa tare da yawan bukatar samun
shinkafa a duniya.

Fiye da rabin mutanen duniya zasu dogara ne kan shinkafa, nan da shekaru 30 masu zuwa. Yankunan da ake
noma shinkafa a sashin Arewachi da Kudancin Najeriya suna fuskantar baranzanar giggina madatsun ruwa,
dakuma bukasar alkari'u watakila sabuwar dabarar ta farfado da nomar shinkafa sannu kan hankali. Ganin
yadda ake asarar filayen noma cikin hanzari, domin bunkasar garuruwa da lalacewar dausayin kasar noma
matsalar ta zama babba da ake fuskanta inji babban Darktan kungiyar ta CGIAR Ronald Cantrell dake da
cibiya a kasar Filifin. 8
8 Page 9 10
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

9
Sabuwar dabarar tana iya taimakawa wajen kyautata tattalin arzikin kasashe masu tosowa na duniya. Akasarin
kasashen dake nomar shinkafa kasashe ne masu tasowa wadanda Bankin duniya yace samun su dan kalilan
ne. Nahiyar Asia na da kasashe goma sha-7 daga cikin kasashe 25 manya dake noma shinkafa. Suna nome
fili mai fadin kashi case'in daga cikin dari na yawan filayen da ake noma shinkafa a duniya suna samar da kashi
casa'in cikin dari na shinkafar da ake nomawa a duniya. A hakikan gaskiya ma kashi daya cikin uku na
kasashen Asia dake noma shinkafa ce suke nomawa a ciki.
CGIAR

Hango barkewar zazzabi mai Tsanani ta hanyar tauraron-dan adam 2mins 7secs
Ana iya kare aukuwar barkewar kwayoyin cutar nan dake haddasa cutar dake kashe garkunan shanu masu
yawa a gabshin Afrika, wanda kuma ke janyowa jama'a shiga halin tasku. Daga binciken da aka gudanar ya
nuna cewar cutar tana da sahihiyar hanyar da take sake zagayowa. Ana iya hango sake zagayowar cutar
watani hudu kain aukuwar ta, ta hanyar yin amfani da tauraron dan adam dakuma daukar matakan lalata
kwayoyin cutar.

Masu binciken su gano cewar zagayowar cutar a ko yaushe yanayin kicibis da daminar da aka samu ruwan
sama mai yawa a yankunan masu yawa na gabashin Afrika. Sunyi nazain yanayi na shekaru hamsin, sun gano
cewar, cutar ta bulla shekaru goma sha-7 da suka wuce, wanda kuma yayi kicibis da daminar da aka samu
ruwan sama mai yawa. Daga bisani kwayoyin cutar sukan bace tsakanin bullowar ta.

Wanan kuwa cibiyar binciken kimiyar Amurka NASA da ma'aikatar kare kwayoyin cuta ta duniya dake
cibiyar bincike ta Walter a Washington DC ne suka gano.

Kamar yadda bincike ya nuna, Sauro Aedes dake yada kwayoyin cutar, suna sanya kwayoyin ne a kwayayen
su, wanda duma ke yaduwa a wuraten dake da dausayi bayan da aka samu ambaliyar ruwa. Su kuwa
kananan Sauron suna samun abincin su ne a jinkin dabbobi. Haka abin zaiyi yaduwa ba tare da la'akari ba har
sai sun yadu sosai. Dabbobin da suka ci wadan nan kwayayen Sauron su zasu kamu da cutar, wanda daga
bisa in mutane sunci naman dabbobin sai su rika kamuwa da cutar zazzabin mai tsanan. Shi kuwa irin wannan
Sauron yana yaduwa ne a locacin da aka samu damuna mai ruwa sama sosai.

Masu binciken suce wannan tauraron dan adam zai taimaka wajen hango ko hasashen barkewar annobar
cutar watani shida kafin aukuwar sa. Abin sha'awar anan shine tauraron dan adam din, zai iya yin gargadi tun
kafin barkewar annobar, kana ya gano ainihin yankunan da abin zai faru, inji wani kwararen masanin halittu
Compton Tucker, wanda yayi amfani da tauraron dan adam, wajen yin nazarin halittu a Afrika na tsawon
shekaru 20.
Environmental News Network 9
9 Page 10 11
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

10
Azabtar da yara ya zama ruwan dare a Uganda 2min 3secs
Iyaye suna yawan dukan 'ya 'yan su tare da yi musu fyade ba kuma tare da an dauki matakan shawo kan
lamarin ba. Wannan kuwa na kunshe ne cikin rahotton da jaridar Monitor da ake bugawa rana-rana a Uganda
ta 13 ga watan Yuli.

Jaridar ta ruwaito cewar wani locain anayiwa yara dukan kawo wuka a gidaje da makarantu. Wasu ma har
kashe su akeyi ta hanyar azabtarwa daga su iyayen saboda 'yan laifukan da basu taka kara su karya ba, irin su
samartakar Bera ko rashin kawowa uban su agogo cikin lokaci yayinda yake kokarin zuwa aiki. Hanyar da
akafi azabtar da yara, itace da daure hannun su da igiya, kana a rufe da ganyen ayaba ko takarda, kana a sanya
a kan wuta inji jaridar. Haka kuma jaridar ta Minitor tayi tir kan yadda akeyiwa yaran mata kanana fyade,
wasu kan dududu ba su wuce shekaru uku da haihuwa ba.

Kwanan nan ne Gwamnatin Uganda ta daga yawan shekarun yiwa 'yan mata aure daga goma sha-4 zuwa
goma sha-8, domin kare su. 'Yan kasar Uganda da abin ya dama suna kura da babbar murya kan Gwamnati
ta kara yin kuduri wajen kare yara mata. Babbar mataalar azabtar da yara, shine Gwamnati ba ta dauki batun
da muhimmanci ba inji jaridar ta Minitor, cikin sharshi ta. Baya ga kungiyoyi masu zaman kansu, Gwamnati
bata kashe kudi wajen gudanar da bincike, ko shirya taruruka na kasa ta yadda za a karfafa gwiwar shawo kan
wannan matsala ta azabtar da yara.
Africa News On Line

Zaki da bera
Zaki wanda ake dauka a matsayin sarkin dawa, saboda karfin da yake dashi yana kuma ladabtar da duk wata
dabbar da ta nemi wuce makadi da rawa. Domin haka dukkan mamun dawa suna tsoron sa kuma suna masu
biyayya gare shi, bugu da kari kuma suna bakin kakarin su na kaucewa duk wani abu da zai bata masa rai.
Dukkan dabbobi suna kokarin ganin dangantakar su da sarkin dawa Zaki ta kara kyautatatuwa.

Wata rana Zaki na barci, sai Bera cikin rashin sani ya taka bancin sa. Yayinda zaki ya tashi cikin fushi, sai ya
kama bera yana son ya kashe shi, shine bera ya roki sarkin dawa da yayi masa rai. Yace watakila wata rana
shima zai taimakawa zaki. Shine zaki yayi mamaki, har abin ya bashi dariya, ganin bera dan tsurut dashi har
yace zai iya taimakawa zaki, wanda shine sarkin dawan dabbobi. Duk da haka dai sai ya sake shi amma fa sai
da ya ja kunnen sa kan kada ya kuskura ya sake tadashi daga barci. Bera yayi godiya kana ya tafi gida. 10
10 Page 11 12
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

11
Baia dade ba da yin haka, ran nan sai zaki na yawo cikin daji, sai ya fada cikin tarkon da maharba suka kafa.
Yayinda zaki yayi ta ruri, domin neman dauki, dukkan sauran dabbobin sai sukayi biris dashi, tunda yake suna
tsoro in har sun sako shi yana iya halaki su. Daga karshe dai sai bera yaji kukan zaki, sai ya tuna da irin alhinin
da zaki yayi masa yayinda ya taka hancin sa yana barci, domin haka sai ya kuduri aniyar zuwa ya taimaka
masa.

Yayinda ya doso zaki sai ya ga ashe taron na kirtani ne. Sai bera ya fara daddatse kirtanin da hakoran sa kan
ajima sai gashi yayi katuwar kofa ta yadda zaki zai iya fita. Yayinda bera ya ceci zakin sai yace dashi, yayinda
ka ceci rai na nace dakai nima watalila wata rana zan cece ka, sai kayi dariya, kace sarkin dawa da kanka yaya
ni bera zan iya taimaka maka.
Domin haka dai aikata alheri ga kowa, ba asan gobe ba.
Character moulding Stories for Better Citizenship.

Meyasa Jamagu ke tashi da dare 1min 5secs.
Jamagu kamar sauran dabbobi basu da wata hanyar kare kansu. Domin haka dahun dare shine makarin su.
Babban abokin gabar su shine Duji, wanda ke yawo da dare domin neman abinci yayinda suma jemagu ke
barin wuraren zaman su irin su kogo ko kuwa bishiyoyi. Wasu daga cikin jemagun suna cin kwari, yayinda ba
mai ganin su. Saboda haka jemagu suna yawo ne cikin dare saboda kare kan su, dakuma samun abincin su
cikin sauki.

Daga cikin dukkan dabbobin duniya jemage ne dadai ke tashi kamar tsuntsu. Fukafukin su fata ce da ta lullube
yatsun su dakuma dogayen kafafun su har baya. Wasu mutanen suna daukar cewar jemagu basa gani. Kokadan
ba gaskiya bane Domin kuwa jemagu suna da idanu dana suna gani saari cikin dare.
Chongololo

Mummunan laifin da Kurege Kadima ya aikata 4mins 10secs
Wata kabila da ke kira Hambakush dake kudancin Afrika, sun bada labarin wani kureje da wata damisa da
'ya 'yan ta. Sun kulla yarjejeniyar cewa, kureje zai rika kula da 'yan 'yan damisar yayinda ta tafi neman abinci,
ita kuwa damisar zata rika baiwa kureje abinda ta samo daga wajen farautar ta. Sunan kureje Kadima ita
kuwa damisa suna ta Nthoo.

Ita wannan yarjejeniyar tayi ta aiki tsakanin su, har yazuwa locain da aka samu kamfar ruwa a kasar. Namun
dajin da ita Nthoo take farautowa duk su gudu zuwa yankunan dake da ruwa, domin haka damisar ta fara
fuskantar mawuyacin hali na rashin abinci tare da Kadema dakuma 'ya 'yan ta. Kwanan da kawanki Nthoo
yadda ta tafi haka take dawowa hannun ta rabbana babu abinci. Nan da nan yunwa ta fara addabar su. 11
11 Page 12 13
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

12
Wata rana Ntooo ta komo daga wajen faruta sai ta samu Kadima na cin nama, shine sai ta tambayeshi ko ina
ya samu abinci, yayinda itama da ta shiga daji domin neman abin kalce bata samu ba. Sai Kadima ye kada
baki yace, wata 'yar karamar dabba ce tazo wucewa bakin kogo, shine na kokarta na kashe. Amma gaskiyar
lamarin shine naman da Kadima ke ci naman daya daga cikin 'ya 'yan damisar ne.

Washe gari Nthoo ta fita faruta, sai Kadima ya sake kashe daya daga cikin 'ya 'ya ta biyu da suka rage ya
cinye. Yayinda damisar ta komo da marice hannun ta rabbana Kurege sarkin wayo, sai ya dauko mata dan
nata guda da ya rage, bayan ta bashi nono sai ya shigar dashi ya sake fitowa dashi yace ga na biyu, bayan ta
bashi nono sai ya shigar dashi ya sake fitowa dashi yace ga na biyu, bayan ta bashi nono ya sake komawo
dashi ya fito dashi yace ga na ukun su.

Washegari bayan da Nthoo ta fita faruta, sai kurege kadima ya sake kashe ragowara dan nata ya lakwame.
Domin kare laifin da ya aikata, sai ya karkarya rassan itatuwa yayi ta birgima a laka, yakuma shafa jar kasa a
jikin sa kamar jini, yayi kamar anyi gumurzun fada.

Yayinda Nthoo ta komo gida, sai kurege yazo gare ta yana tafiya kata-kata yana kuka ya shaida mata cewar,
wasu mutane ne suka zo suka kashe 'ya 'yan ta suka tafi dasu cikin kauye domin su cinye su. Yace yayi kokari
domin kare 'ya 'yan amma maharbar suka nada masa dan karen duka, har ma sun kusa kashe shi. Shine ya
nuna jar kasar da ya shafa a jikinn sa da cewa jinin dukan san ne.

Nan take Nthoo damisa tayi wani kugu cikin daren wanda ya girgiza jama'a. Cikin fushi ta nufi kauyen dake
kusa dasu, domin daukar fansa kan mutanen da suka kashe 'ya 'yan ta. Yayinda damisa ke kokarin auka wa
wasu yara sai taji wani tsuntsu yace Kadima ne ya kashe miki ya ya.

Sai Nthoo ta juya da baya a fusace domin aukawa Kadima kurege, amma yayinda Kadima yaji tautasuwar nan
tana fadawa Nthoo sai yace kafa me naci ban baki ba. Nthoo damisa bata samu ta kama Kadima kurege ba,
amma mutanenen Hambakush suce har yanzu Nthoo tana cigaba da neman Kadima. Shine yasa har yanzu
damisa take kaffa-kaffa kana take farauta ita kadai. Kuma shi yasa kurege yake gudu a kodayaushe domin
tsirar da ransa batare da yana waiwaye ba.
When Hippo Was Hairy 12
12 Page 13 14
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

13
Gibi Tsankanin maza da mata a makarantun Afrika 46secs
Yara maza akafi dauka a makarantun Firamare da sakadare fiye da yara mata a akasarin kasashen Afrika.
Gibin yakairabin yara mata ake dauka kan maza a kasashe 11 ciki harda Najeriya, da Ghana da Cote d'Ivoire,
da jumhuriyar Benin da jumhuriyar denijyradiyar Congo. Wannan kuwa yana kunshe cikin sanarwar da majalisar
dunkin duniya ta bayar.

Sama da kasashe 18 ne suke kokari wajen cike gibin, wadanda suka haka da Masar da Zimbabwe, da
Uganda da Habasha da Cameru dakuma Algeria. Kasashe bakwai kuma basa nuna wannan bambancin,
yayinda Afrika ta Kudu da Lesotho kuma yaran mata ne akafi dauka cikin makarantun fiye da yara maza.
United Nations

Matsalar ingantacen ruwan sha 14secs
Yanzu haka akwai kasashe 31 a duniya dake fuskantar matsalar karncin rwan sha. Yazuwa shekara ta 2025
ana kyautata Zato yawan kasashen zasu karu zuwa arba'in da tawas yazuwa shekara ta 2-50 kuma da zasuyi
fama da matsakar karancin ruwan zasu kai 55.
CGIAR

Italiya na daukar tsauraran matakai kan karya
dokokin muhalli 44secs
Yayinda take samun aiyukan cunna wuta a gandun dazuzzukan ta kowace rana yanzu kasar Italiya ta sanya
tarar dala dubu 60 ga duk wanda aka kama da laifin cinna wuta a gandun dajin kasar. Kana za a bada kyautar
wannan kudin ga duk wanda ya taimaka aka kamo wanda ya cinna wutar. Rahotanni sun nuna cewar masu
cinna irin wannan wutar a Itlaiya suna janyo ta'adi mai yawa na katako da sauran gandun dazuzzukan kasar a
duk shekara.

Kusan kowace rana sai an sami rahoton cinna wuta har sau 28 a locain bazara a shekaru biyar da suka wuce,
yayinda filaye mai fadin kadada dubu dari biyar da arba'in ne suka kone, kamar yadda rahoton hukumar kula
da halittu ta duniya tayi bayani.
WWF

Bunkasar alkari'u cikin hanzari a Afrika 21secs
Mutane sai kara baikin yankunan karkara suna zuwa birane a nahiyar Afrika fiye da kowace nahiya a duniya.
Tsakanin shekarar 1995 zuwa 2025 yawan mutanen dake alkari'un Afrika zai rubanya har sau biyu a duniya,
amma na Afrika zai rubanya sau uku a daidai wannan lokacin.
Boiling Reint 13
13 Page 14 15
Vol 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

14
Tsuntsun dake sanin locaci 59secs
Katabaji wani tsuntsu dake fadin locai? Wasu masu bincike kan halayyar tsuntsaye a kasar Indonesia sun gano
wani abin sha'awa. Su wadan nan masu binciken da ake kira Pitta Erythrogaster, sun gano wasu tsutsaye
masu launin ja a ciki suna iya sanin locacin dake ciki a duk twawon rana. Da asuba tsutsayen sukan sauka kasa
su rika yin wata irin waka. Yayinda rana ta daga sai su hau kan bishiya har sai rana ta raba tsaka. Yayinda rana
ta fara faduwa, sai tsutsayen su sauko daga rassan bishiyar har zuwa faduwar rana. Ba anan ta tsaya ba in har
tsuntsayen sun sauka kasa batare da sun hau kan bishiya ba to ranan za'ayi ruwa.
WWF

Asarar halittu 34secs
"Babbar asarar da zata auku ba wai rashin makamashi ba ko gurguncewar tattalin arziki, ko yaki da makaman
kare dangi ko cinyewa da yaki ba. Duk da irin wadan nan ta'adi ko asarar, yan baya masu zuwa suna iya
farfadowa dashi. Amma babbar asara itace wanda aka fara a shekarun 1980, wanda kuma zai dauki miliyoyi
shekaru ba a gyara ba kamar yadda wasu halittun ke bata baki daya daga doron duniya. 'Yan baya masu zuwa
bazasu gafarta mana ba muddin muka kauda wasu halittun batare da sun sansu ba.
Edward O. Wilson

Kasar Canada na da nuhimmanci kan halittu 26secs
Canada keda kashi 10 cikin dari na dazuzzukan dake akwai a duniya, wanda yakai kadada milyan 418, wanda

ya kai kimanin rabin fadin kasar baki daya. Wanan gandun dazuzzukan suan taimakawa wajen kula da kashi
20 cikin dari na ingantacen ruwan sha na duniya, wanda kuma nau'o'in dabbobi daban-daban har dibu dari da
arba'in ne ke zaune a yanki. Bugu da kari kasar itace kan gaba wajen saida albarkatun dazuzzuka a duniya irin
su katako.
WWF 14
14 Page 15
Vol. 11 No 10
September 1999 (Hausa) CHANGE Radio

15
Kalmomin Da Akayi Amfanidasu
AAI -Kungiyar kawance bunkasa masana'an ta Afrika
ADB -Bankin raya Afrika
AIDS -Cutar Kanjamau
CGIAR -Kungiyar kwararu kan binciken aikin gona
ECA -Hukumar raya tattalin arziki na Afrika
FAO -Hukumar abinci da aikin gona ta duniya
HIV -Kwayoyin cutar kanjamau
NCF -Hukumar kula da gandun daji ta Najeriya
NGO -Kungiyoyi masu zaman kansu
OAU -Kungiyar hada kan kasashen Afrika
UN -Majalisar Dukin duniya
UNDP -Hukumar raya kasa ta duniya
UNIDO -Hukumar raya masana'antu ta duniya
UNITA -Kungiyar 'yan tawayen Angola
WWF -Asunsun kula da gandun daji da halittu 15

Page Navigation Panel

1 2 3 4 5 6 7 8 9
10 11 12 13 14 15

 

© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw