Document Body Page Navigation Panel
'yan sandan Najeriya basa iya tsare masu keta haddin mata da yara.
ILMI:
JUMHURIYAR NIJAR TA SAMO HANYAR SAKE TSUGUNAR DA M WADANDA SUKA KARE KARATU
3 Min 18 Sec.
Wata kasar Afrika ta yamma ta fara daukar matakin dakile matasa masu zaman
kashe wando. KARA GINA GIDAJEN YARA MAZA DA MATA MARASA GALIHU. 26 Sec.
Akasarin kasashen duniya yanzu sun fara gina gidajen marayu.
MAKAMASHI: GIDAJE SUNE KE KAN GABA WAJEN AMFANI DA MAKAMASHI A NAJERIYA:
1 Min
53 Sec.
Akasarin makamashin da ake samu a Najeriya na tafiya ne wajen girkegirke
da tafsa ruwa.
ABINCI:
YAKIN BASASA YA HAIFAR DA MATSALOLIN SMAR DA ABINCI A GABASHIN
AFRIKA: 4Mins 17 Sec. Kasashen Afrika sha-5 ne suka shiga shekara ta 2000
inda miliyoyin mutanen su basu da abincin da zasu
ci.
KIWON LAFIYA:
SHEKARA TA 2000 maiyiwuwa ta zama karshen cutar shan-inna 2Mins 42 Sec. Maiyiwuwa
yekuwar majalisar dinkin duniya na shekara 12 domin kauda cutar shan-inn kwalliya
zata biya
kudin sabulu. SABBIN NAZZARI YA BAIYANA HATSARIN DAKE TATTARE DA AMFANI DA
TABA
SIGARI. 3 Mins 38 Sec.
Ana kyautata masu mutuwa a sakamakon sukar taba sigari su karu cikin 'yan
shekarun nan. MAJALISAR DINKIN DUNIYA TACE CUTAR KANJAMAU NA BARAZANA GA
ZAMAN
LAFIYA a AFRIKA. 4 Min 30 Sec.
Cutar kanjamau yanzu ta zama matsalar tsaro ga Gwamnatocin Afrika.
SADARWA:
FINAI 2 DAGA TASHAR TVE SUN SAMI KYAUTAR YABO. 2 Min 7 Sec.
An baiyana matalosin da Afrika ke fuskanta cikin fina-fainai biyu da suka
samu lamba.
MUHALLI: 1
1 Page 2 3
2
Febrairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio
WANI KAUYE A KASAR GHANA YA BULLO DA AMFANI DA TAKIN GARGAJIYA KAN
NOMA.
5 Mins 34 Sec.
Kauyen da ya daina amfanin gona dazika a farkon damina domin shuka yanzu
ya fara cin moriyar shirin.
YANAYIN MUHALLI:
BURATANIYA TA KASAFTA DALA NILIYAN 34 DOMIN SU A AFRIKA: 2 Mins 27 Sec.
Burataniya ta dauki matakin farko domin gyara harkar su a Afrika.
TEKUN CIKIN KASA MAFI GIRMA A DUNIYA: 24 Sec. Nahiyoyi uku sunyiwa tekun
kasa da'ira mafi girma a duniya.
SARE GANDUN DAJI:
RAWAR TABA SIGARI KAN SARE GANDUN DAJI. 1 Min 7 Sec Masu taba sigari sun
yarda kan suna gurbata dazuzuka baya ga janyo mutuwar mutane masu shan tabar
da
suke yi.
KASAR SIN TA HARAMTA SARE ITATUWA, AMMA TANA SAYO KATAKO. 25 Sec.
Kasashen dake makwabtaka da Sin suna sare itatuwan su domin saida mata da
katako.
HAMADA MAFI GIRMA A DUNIYA: Kasashe takwas masu girman Nageriya ne
zasu iya shiga cikin hamada mafi girma a duniya.
SARAN ITACEN KATAKO
Daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ceto daji ya zama kakakin ma'aikatai
sarrafa katako. Wani wanda na daya daga cikin 'yan kungiyar kare muhalli, ya
fda aikin samun kudi saidai kuma ba annuri
a fuskar sa.
YAWON BUDE IDO:
TSUNTSUN DAKE KULA DA MASAN'ANTA. 1 Min 1 Sec. Hanya mafi dacewa wajen habaka
aikin tsuntsun dake duba masana'anta.
SASHIN YARA:
JAKI DA DORINA. 4 Mins 14 Sec. Hadamar jaki da ramuwar gayyar dorina.
DALILIN DA YASA GUNDURI BAIDA JELA 3 Mins 55 Sec. Sanyi jiki da rashin
biyayya ya sanya gunguri ya rasa jelar sa
KARIN MAGANAR YANAYIN MUHALLI. 47 Sec. Al'umar duniya na iya zaman lafiya
da yanayin muhalli? 2
2 Page 3 4
3
CHANGE Radio Febrairu 2000 (Hausa)
WACE DABBACE TAFI HADARI. YANKIN Amsoshi uku kafin ka karanta
littafin.
LABARU:
GIDAJE NE SUKA FI AMFANI DA MAKAMASHI A NAJERIYA. 1Min 53 Sec.
Masu gidaje sune suka fi yin amfani da makamashin da ake samarwa a Najeriya
musamman yankunan alkari'u. Sashin shike amfani da kusan dukkan makamashi dake
samarwa kano itacen da fetur da kalanzir
Sashin ke amfani da kashi uku cikin hudu na kalanzir din da ake samarwa a
kasar. Kamar yadda wani bincike da aka gudanar ya nuna daga shekarun 1992 da
1995 dakuma 1997 kashi goma cikin dari na lantarkin da
ake samarwa dun sun tafi ne kan aiyuka a gidaje dakuma gas. Binciken ya nuna
duk wadan nan makamashi ana amfani da su ne wajen girke-girke da kuma dumama
ruwa.
Dumin matsalar karancin mai da ake samu daga lokaci zuwa lokaci yana shafar
mazauna birane na kasar fiye da masu motoci da sauran jama'a dake amfani da
ababan hawa, ba kamar yadda ake zato ba. Akasarin
makamashin da ake amfani dasu a kasar ana samu ne daga albarkatun manfetur.
Haka kuma an sami karuwar amfani da albarkatun manfetur her ninki goma a shekaru
1970, kuma mazauna birane suke kan gaba wajen amfani dashi.
Yawan karuwar jama'a ha haifar da karuwar mazauna birane, da karuwar masana'antu
dakuma habakar tattalin arziki dakuma kokarin rata yankunan karkara suna daga
cikin yawan karuwa da amfani da
makamashi.
Kamar yadda masu bincike daga jami'ar tunawa da Ladoke Akintola a Najeriya suka
fadi, yawan karuwar
amfani da makamashin albarkatun manfetur a birane wata alamace na cigaban tattalin
arziki. Sai dai bai kai ga raguwar amfani da shi makamashin ba irin su itacen
wuta koda a biranen. Wannan kuwa saboda
makamashin da akafi dashi a gidaje irin su kalanzir da gas da gawayi har yanzu
bai daidaita ba kuma babu tabbas.
BOILING POINT:
SHEKAR TA 2000 WATA KILA KARSHEN CUTAR SHAN-INNA. 2 Min 42 Sec.
Akwai kyakkyawar zato a majalisar dinku duniya a wannan shekara game da
samun nasara kan cutar da
ta addabi duniya, watau cutar shan-inna. Yaki da cutar da aka kaddamar a 1988
domin kauda cutar a duniya kafin shekata ta 2000, yanzu yana matakin karshe.
Yawan bullar cutar ya ragu ainum daga dubu 350 a 1988
zuwa dubu 5 da metan a shekarar 1999 a duniya baki daya.
Muna daf da kafa tarihi kan nasarar kiwon lafiya, na kauda cutar shan-inna,
cutar da ta sanya duniya cikin
jafa'i inda miliyoyin yara suka nakasa, inji darektajanar ta hukumar kiwon lafiya
ta duniya WHO Gro Herlem Brundtland cikin watan janairu.
Ms. Brundtland da Gro Bellamy babban darektan hukumar yara ta duniya (UNICEF)
sun rubutawa shugabanin kasashen duniya akalla 30 a Africa da Asia inda nan
ne cutar tafi kamari,. Sun bukaci shugabanin 3
3 Page 4 5
4
Febrairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio
da su taimaka wajen shirin allurars tare da samar da duk abinda ya kamata
musamman a ranakun da ake domin kaddamar da allurar rigakafin na kasa domin
kwalliya ta biya kudin sabulu.
Matka dai akwai yaro daya dake dauke da wannan cuta yara a ko ina suna cikin
kasadar kamuwa da ita kenan inji Bellamy kwanan nan a New York.
Yunkurin duniya na kauda cutaar karfin karshen shekara ta 2000 karkashin jagorancin
hukumomin WHO da UNICEF dakuma Rotary na duniya. India ke da kashi saba'in cikin
dari na masu fama da cutar a duniya.
Kokarin kauda cutar a karshen shekarar ya dogara ne kan kokarin da India keyi
a halin yanzu.
A shekara ta 2000 shekarar dake saran kauda cutar, muina da dama domin cin nasara
kan outar har abada'inji Dr. Brundtland a wajen kaddamar da matakin darshe na
kauda outar ta shan-inna a fadar kasar
India, inda wakilai sama da 300 ciki harda jakadoji suka halarta daga Afrika
da kudancin Asia.
Tundaga kaddamar da yaki da cutar a 1988 aka samu raguwar bullar cutar ainun.
Tawan yaran dake zaune
a yankunan da cutar tafi yawa a duniya ya ragu daga kashi 90 cikin dari zuwa
rabin hakan, kana an kauda cutar a yankunan Amurka da Turai da yammacin Pacific
da akasarin gabas ta tsakiya da akasarin arewaci
da kudancin Afrika.
UNITED NATIONS:
BIRRITANIYA TA KASAFTA DALA MILIYAN 34 DOMIN SU A AFRIKA: 2 Mins 27 Sec.
Kasar Ingila zata bullo da wata sabuwar hanyar kula da tattalin arziki,
domin kare tabarbarewar harkar kamun kifi a Afrika. Kwanan nan ne ma ta bada
sanarwar kebe dala miliyan 34 domin tallafawa kimanin
masinta miliyan 24 marasa karfi dake kasashen Afrika, wadanda sukafi tagayyara.
Wannan shirin ya gaza ainun kan yekuwar da kungiyar kare muhalli ta duniya keyi
na tabbatar datuntubar juna tsakani Afrika da
Turai kan yarjejeniyar kamun kifi yadda ya haifar da kamun kamun kifi fiye da
yadda aka kayyade da hanzarin tabarbarewar harkar su da Turai keyi a Afrika.
Kungiyoyin kula da muhalli sun bukaci sabon tsari karkashin taron Lome, wanda
zai yanke tallafin da Gwamnatoci ke bayarwa kan harkar hamun kifi, da rage yawan
jirager kamun kifi da inganta kimiyar
su, danufin kyale kamun kifi ya hada da komai da koma daga tekun Atlantika.
Sabuwar yarjejeniyar zata kuma tanadi sa ido domin tabbatar da ganin ana bin
tsarin da aka shimfida dakuma kudin ka'ida da ake biya
ga Gtocin Afrika da ake kamun kifi a farfajiyar ruwayen su.
Dala miliyan 34 na taimakawa shirin su na Biritaniya (SFL) zai taimakawa fiye
da masinta miliyan biyar marasa karfi a kasashen da abin ya shafa, wadanda suke
gudanar da su kai tsaye
Shirin zai karfafa tsarin su mai dorewa, da muhimmancin kamun kifi ga masu
karamin karfi, da masu sana'ar
kifi. Haka kuma zai taimakawa kasashen da shirin ya shafa domin magance wasu
daga cikin matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya.
Sun kuwa hada da yawan gurbata ruwa domin su lalata tsarin su da gurbata yanayin
muhalli, da asarar dakuma rashin jituwa tsakanin masinta dakuma kifayen da basu
ake bukatar kamawa ba.
Wadan nan kasashen sune shirin zai shafa, Angola, da jumhuriyar Benin, da Burkina
Faso, da Camerou, da Cape Verde, da Chadi, da Congo, da Cote d'Ivore, da jumhuriyar
decokuradiyar Congo, da Equatorial 4
4 Page 5 6
5
CHANGE Radio Febrairu 2000 (Hausa)
Guinea, da Gabon, da Gambia, da Ghana da Guinea Bissau, da Liberia,
da Mali da Mauritaniya, da jumhuriyar Nijar, da Najeriya da Sao Tome da Principe,
da Senegal, da Saliyo dakuma Togo.
Hukumar abinci da aikin gona ta duniya da hukumar raya kasa da kasa ta Biritaniya
dakuma kasashen Afrika ne zasu tafiyar da shirin.
FAO/ OBASI OGBONNAYA.
FINA? FINAN AFRIKA BIYU NA TASHAR TVE KAN MUHALLI SUN SAMI KYAUTAR YABO
2 Min 7 Sec. Suniyar da tayi zuwa wata dakuma yayinda mutane na gari suka
kasa yin wani abu sune fina-finai biyu kan
abin takaici ga afrika na karnin da ya shige da hukumar talabijin na TVE ta
shirya da kuma suka sami kyautar yabo a wannan karnin.
Daya daga cikin su, watau Saniyar da tayi tsalle zuwa wata ya samu kyautar
Prix wajen bukin fina-finai na duniya da akayi. Fin da Chris Walker ya shirya
ya biyo yadda fulani makiyaya a Afrika ta yamma dake tafiya
daga wannan wuri zuwa wancan yakka suke fama da abubuwa iri-iri domin samun
abincin shanun su. Fi din ya nuna yadda fulanin ke kokari wajen samun abincin
dabbobin su da dan ciyayin dake akwai kana yake
dushewa. Sai taimko yazo daga bisani daga inda basa tsammani, yadda ilmin kimiya
ke taimakawa wajen
rayuwar hanyoyin al'adu.
An fara nuna wannan fin ne a cibiyar Margaret Mead a New York wajen bukin
baje kolin fina-finai. An kuma zabe shi domin gasar fina-finai na Washington
DC kan muhalli cikin watan Maris 2000.
Fin na biyu In mutane na gari suka kasa yin komai' ya sami kyautar 1999 domin
bincike na duniya. Kungiyar 'yan jaridu masu bincike ta duniya (ICL) ce ta bada
kyautar a Turai Steven Bradshaw da Mike Robinson
ne suka dauki fin din inda suka maida hankali kan hatsarin dake akwai game da
kisan kiyesin da akayi a kasashen rwanda inda aka kashe kabilar Tutsi kimanin
miliyan guda a shekara 10 da ta shige a karni na
ashirin. Fin din yayi tambayoyi, Meyasa kasashen Yammaci suka kassyin wani abu
domin hana aukuwar
wannan jafa'i?. Alkalan da suka bada kyautar sun bukaci da a nuna wanna fin
ga dalibai a duniya baki daya, domin nuna yada ragwantakar siyasa takai ga kisan
kare dangi ya sake komowa cikin al'umar duniya.
ONE WORLD ORG:
SHARFHI:
YAKIN BASASA YA HAIFAR DA MATSALAR ABINCI AGABASHIN AFRIKA 4 Mins 17 Sec.
Kimanin kasashen Afrika 15 suka shiga sabon karnin nan tare da fuskantar
matsanancin karancin abinci.
Kasashen Angola da Burundi da jumhuriyar Demokuradiyar Congo, da Eritria da
Habasha da Guinea Bissau da kenya da Liberia da Liberia da Rwanda da Sliyo da
Somaliya, da Sudan da Tanzaniya dakuma Uganda
duk suna fama da yakin basasa. Da yakin basasa na dogon lokaci dakuma kamfar
ruwa sun shafi aikin noma a dukkan wadan nan kasashe.
Da take gargadi kan mumuna yanayi a Sudan hukamar abinci ta duniya game da
Sudan cikin rahoton ta na 5
5 Page 6 7
6
Febrairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio
baya-bayan nan tace mi kimanin mutane miliyan biyu ne yakin basasa da
kamfar ruwa ta hanawa sukunin samun abincin taimako kana mutane sun fara mutuwa
saboda yunwa.
Kamfar ruwa tare da yakin basasar sun kai ga hanawa akasrin iyalai zuwa gonaki.
Haka kuma fadan ya gurgunta harkokin noma tare da samar da kayan jinkan dan
adam dake bukata. Yaduwar tashe-tashen
hankula ya dakile aikin rabon kayan jinkai an kuma bada rahotani mutuwar mutane
da dama dake da nasaba da yunwa.
Rahoton kungiyar watsa labarai da hukumar FAO ce ta shirya. Wani babban jami'in
tsimi Mr. Mwita Rukandema yace ' kamfar ruwa na tsawon lokaci tare da yakin
basasar da ya raba mutane da gidajen su, da
kwarin dake lalata kayan abinci, sun sanya al'umar Somaliya cikin bala'in karancin
abinci. '
A wau sassa na gabashin Afrika, rashin ruwan sama ya sanya ba a iya noman hatsi
a kasashe irin su Kenya da Uganda da Tanzaniya dakuma Habasha, wanda ya sanya
jama'a da dama ke dogaro kan abincin da ake
kawowa na taimako. a Eritria mutane rabin miliyan da yaki ya tagiyara ne suke
fuskantar karancin
abinci, yayinda a Sudan duk da yanayi na kwarai mutane miliyan biyu ke dogaro
da abincin taimako a sashin kudancin kasar saboda yaki.
Rahoton ya kara da cewar yankin tabkin gabashin Afrika har yanzu yana fama
da matsalar karancin abinci saboda tashe-tashen hankula dake cigaba a sassa
daban-daban na yankin.
Ga misali ana samu matukar wahala wajen samr da abinci a Burundi saboda sake
kazancewarfada a wasu sasan kasar, wanda ya haifar da gujewar mutane dega gidajen
su, tare da tilastawa kungiyoyin kasa da kasa
dakatar da bayar da agaji ga mutane kimanin miliyan daya a sansanonin 'yan gudun
hijira. Yanayin zama a wadan nan sansanonin bakyaun gani, babu ruwan sha mai
kyau babu kuma wurin zagayawa
inji rahoton.
Ana kyautata zato matslar zata kara kazanjewa cikin 'yan watani nan gaba.
A jumhruriyar demokuradiyar Congo rahoton yace yakin basasa ya jefa mutane miliyan
goma cikin rashin tabbas kan abinda zasu ci, yayinda a makwanciyar ta Congo
yaki ya gurgunta aikin gona da harkokin
kasuwanci. Koda shike a Rwanda an sami karuwar kayan abinci a shekarar da ta
gabata har yazu tana bukatar taimako, domin ciyar da 'yan gudun hijira dake
komawa gida su dubu dari tara. Angola da
Madagascar ana samun matsala wajen samar da abinci saboda yakin basasa tare
da farin dango.
'Duk wanda yaga wannan kididdigar zai nuna damuwa 'inji shugaban kungiyar
ta AHA Lyni Smaha. Shan taba na cin kudi kimanin dala miliyan dubu 30 kowace
shekara kan aikin samar da magani a Amurka kadasi.
Wannan kuwa ya hada da kudaden kula da mata masu juna biyu dake zukar taba,
wanda ke haddasa haifar jariran da basu da nauyi.
Rahoton na kungiyar AHA ya baiyana wasu illolin shan taba. Kamar yadda hukumar
ta WHO ta baiyana mai shan taba na iya rage yawan bunkasuwar zuciyar sa cikin
shekara guda da fara shan taba sigari. Wani
tsohon mai shan taba da ya daina shekaru 15 zai fice daga kasadar mutuwa daga
cutukan dake da nasaba da shan tabar.
Masu bincike yanzu sun dukufa kan hanyoyin da suka fi dacewa na karfafawa
yara gwiwa domin su dawo 6
6 Page 7 8
7
CHANGE Radio Febrairu 2000 (Hausa)
daga rakiyar shan taba. Wannan kokari na bisa bincike da ya nuna cewa
akasarin mutanen dake shan taba sun fara ne tun kafin su cika shekara 18 a duniya.
Nazarin da aka gudanar kwanan nan a Amurka ya nuna cewa tsara shirukan da zasu
sanya yara gujewa shan taba yafi tasiri kan yi musu laccoci game da kasadar
dake akwai na shan taba. Kamar yadda jami'in nazarin
Rich Petosa, inda yace matsi daga abokai shine ke sanya yara shan taba mai makon
ra'ayin su.
Da yakeyiwa yaran lacca kan kasadar dake tattare da shan taba bai hana musu
shan tabar ba. Shirukan zaman takewa tsokaci kan abinda yake damun matasa inji
Petosa. Shirukan da sukayi nasara sune wadanda
ke matsawa matasa lamba kan su guji duk wani abinda zai sasu bada kai. Sauran
masu binciken sun gano cewa irin wadan nan shiruka zasu dakile yadda matasa
ke shan bada gudunmawa ciki harda hukumar ta
WHO, da cibiyar shawo kan cutuka da kungiyar bincike. ENN.
KANJAMAU NA BARAZANAR ZAMAN LAFIYA A AFRIKA INJI UN. 4 Mins 30 Sec.
Yake-yaken Afrika tun-tuni sune ke cikin ajandar kwamitin sulhun majalisar
dinkin duniya. Amma ba a taba duba maganar cutar kanjamau dakeyiwa zaman lafiya
barazana ba a nahiyar Afrika.
Watan jiya ake saran zaunanun wakilan kwamitin su biyar da sauran goma nadadu
zasu tattauna kan kiwon
lafiya a karo na farko, wanda mataimakin shugaban Amurka Al Gore aka shirya
zaiyi jawabi ga wannan taro mai dimbin tarihi. Amma kuma Rasha da Sin biyu daga
cikin kasashe biyar dake da kujerar dindindin suka
ki yarda da ayi taron.
Jakadan Amurka a majalisar Richard Holbrook ya shaidawa manema labarai cewa
dalilin taron shine
fadakar da duniya kan yadda cutar kanjamau ke lakume rayuka a Afrika da yunkurin
rage yaduwar cutar tare da sake duba manufar kwamitin sulhun bayan karewar yakin
cacar baki. Yakin cacar baki dai kalma
ce da ake amfani da ita lokacin da ake zaman doya da manja ta na gabashin
Turai da sukayi ta tara makamai.
A matsayin sa na shugaban kwamitin sulhun a watan Janairu, Holbrook an shirya
zai bude taron, shine ya
gayyaci Al Gore, domin gabatar da kasida kan manyan manufofin Amurka ta yadda
suka shafi cutar kanjamau. Mataimakin shugaban na Amurka zai kuma bada sanarwa
game da sabbin kudurorin Amurka
inji Holbrook.
Kafin taron ne Al Gore ya baiyana abinda ke akwai.
Ana saran mutane da dama ne zasu mutu a farkon shekaru goma na wannan sabon
karni a sakamakon cutar kanjamau fiye da wadanda suka mutu a sakamakon yaki
a karnin da ya gabata ya fadi cikin jawabin sa ta
gidan talabijin a Amurka.
Kanjamau ya gurgunta tattalin arziki da zamantakewar al'umar Afrika, bayan kantar
talauci da rashin tsarin kiwon lafiya, cutar na hanawa kasashen amfani da mutanen
su masu jini a jika, kana yara sama da miliyan 10
ne suka zama marayu a sakamakon cutar.
A 1998 yakeyake yayi sanadiyar mutuwar mutane miliyan biyu. Sashin gabashi da
kudancin Afrika nan cutar
tafi yin ta'adi. Afrika mai kimanin kashi biyar cikin dari na yawan mutanen
duniya fiye da rabin mutanen ta miliyan 16 da dubu dari uku sun rasa rayukan
su a sakamakon cutar kanjamau inji majalisar dinkin duniya. 7
7 Page 8 9
8
Febrairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio Akwai mace da dama tsakanin
masu hali na Afrika a sanadiyar cutar, ciki harda ma'aikata, wanda ke barazana
ga
ingantuwar aiyukan Gwamnati na wasu kasashen. Babban sakataren majalisar dinkin
duniya Kofi Anan ya fadi cikin kasidar da ya shirya ga majalisar. Yaduwar cutar
tsakanin sojoji da 'yan sanda ya sanya kasashen Afrika basu da jaruman
da zasu kula da harkokin tsaro inji shi.
A yanayin dake kwan-gaba-kwan baya, wannan mugunyar cutar zata kara dagula al'amari'
inji Kofi Anan, tashe-tashen hankula kuwa zai bada damar kara yaduwar cutar,
domin harkokin kiwon lafiya zasu ruguje haka na ilmi, babu kuma
damar kai kayan agaji gudun jama'a dakuma yaduwar cutar tsakanin sojoji. Kamar
sauran rukunonin jama'a daka zurga-zurga duk wannan zai kara taimakawa wajen
yaduwar mugunyar cutar ta
kanjamau cikin hazari.
A watan jiya ne Anan ya gai yaci wakilai daga Afrika da hukumomin majalisar
dinkin duniya do Gwamnatocin dake bada gudunmawa da kungiyoyin su da 'yan kasuwa
hanshakai da su tsara wani jadawali da zai rage yawan yaduwar cutar na
akalla rubu'i na matasan dake tsakanin shekaru 15 zuwa 24 kafin shekara ta 2005.
Ya bukaci samun karin bayani da yakar cutar ta hanyar samar da allurar rigakafi
da sauki samu domin Afrika dakuma sake kuduri daga kasashe masu arziki, domin
zuba kudin su kan sikin yaki da cutar a Afrika.
Annan yayi fatar kwamitin sulhun zai kasance abokin aiki a kokarin da akeyi
na ganin yake-yake bai taimaka wajen yaduwar cutar ba kanjamau ba ko hanawa
majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin ta shiga shirin shawo kan cutar
ba, inji kakakin majalisar Fred Eckhard..
DESERETNEWS.
S A S H I N Y A R A .
JAKI DA DORINA: 4 Mins 14 Secs.
Shekaru da dama da suka shude jaki da dorina abokan juna ne, sun saba zuwa
kiwo tare a bakin fafi. Wata rana lokacin da rafi ya ja da baya, sai jaki ya
hangi ketaren kogi yaga tsirrai kore sharr. Kafin dorina ta zo a wannan ranar
sai jaki ya
ketara ta inda babu zurfi, ya shiga cikin shukar dake ketaren rafin yaci ya
cika cikin sa. Yayinda ya komo da maraice, sai dorina taga cikin jaki ya cika
til, sai ta tambaye shi ko ina ya sami abinci?
Jaki yace na ketara rafi ne inda na tarar da abinci iri-iri mai dadi. Meyasa
ba zaki bini gobe muje can ba?
Ah zamuje mana inji dorina.
Da gari ya waye sai jaki da dorina suka kama hanya, suka ketara rafi. Yayinda
suke tafiya sai jaki ya shawarci dorina cewar, gonar fa akwai mai gadi, dake
gadin shukin dare da rana amma kadi ki damu zan rika duba hanya yayinda ki kecin
shukar. Zanyi kuka in naga mai gadin na zuwa sai ki san yadda zakiyi wajen fita
daga cikin gonar.
Dorina tayi jaki godiya bisa wannan alheri, dorina tayi ta cin tsirrai cikin
hanzari har lokacin da taji jaki yayi kuka sai ta fito da gudu gonar ta ketara
rafi tako inda take gani ta tsira, inda mai gadi bai ganin ta.
Haka sukayi washe gari, dakuma sauran kwanakin har saida dorina ta gane cewar
jaki bai biyo ta lokacin da take fita
daga gonar, ko lokacin da yayi kuka. Dorina ta gane cewar dai jaki tsoratata
yakeyi, shi yana tsayawa a baya yayi yaci shuki yadda yake so har sai yaji yayi
kat. Yanayin haka ne kuwa, domin kada dorina taci ta cika cikin ta babu mai
gadin
dake kula ka gonar.
Dorina batace uffan ba suka cigaba da haka har lokacin da damina ta fadi, rafi
ya cika makil da ruwa.
Jaki bai iya ketarawa yanzu saboda ruwa ya kawo kogi yayi zurfi. Domin haka
bai iya yin nitso cikin ruwa sai ya cigaba 8
8 Page 9 10
9
CHANGE Radio Febrairu 2000 (Hausa) Ita kuwa dorina sai kara kiba
takeyi domin kullum sai ta ketara taje tayi ta cin tsiran gonar tana komowa
da maraice.
Kamata yayi ka koma ga gonar nan inji dorina, sai jaki yace naso hakan amma
ba kisan ban iya ruwa ba. Dorina tace
dubi sai ramewa kakeyi, ga kuma abinci makil a ketaren rafi. Bari zan taimaka
maka na haye da kai gobe inji dorina.
Jaki ya hau bayan dorina suka fara ketara ruwa. Komai lafiya har sai da suka
kai tsakiyar kogi, sai dorina tace nan da zurfi kafafuna basa taba kasa, sai
ta nutse cikin ruwa tare da jaki, dorina sai kara kasa takeyi cikin ruwa tare
da jaki, shi
kuwa jaki da baya iya numfashi cikin ruwa, sai shan ruwa yakeyi cikin kogi.
Shine har kwanan gobe abota tsakanin jaki da dorina bai sake ingantuwa ba.
SHANGANI FOLKTALE.
IN KUNNE YAJI: 47 Secs.
'Mun gaji duniya daya ce in mutane sunyi munafurcin lalata bishiyoyi tare
da ruwa ko gurbata muhalli takai har ya canja yanayin muhallin, domin haka abinda
zai biyo baya shine wahalolin da mutum zai fuskanta wanda ba karama ba. Domin
kuwa ciwo ne kan ciwo bi bisa wahalolin da dan adam ke fama dasu. Tilas ne mu
dauko daga salsala, sannan mu sake
halaiyar mu game da halittu domin rage kantar talauci tun kafin lokaci ya kure
man.
Tilas ne mu zama masu kare muhalli, domin cigaba da rayuwar al'umar duniya
cikin kwanciyar hankali da lumana tare da sauran halittu.
HIS HIGHNESS PRINCE SADRUDDIN AGA KHAN (1985).
ABINDA YA HANA GUNDURI JELA 3 Mins 55 Secs.
A zamani da can tu kafin baiyanan dan adam, zaki shine sarkin dawa na sauran
dabbobi kuma shine kadi ke da jela.
Har yanzu koda shike yana alfahari da irin baiwar da Allah Yayi masa, yana gani
kamata yayi sauran dabbobi talakawan sa ma su sami jela, domin amfanin dake
akwai gare ta, kana shi zakin ba zai zama daban cikin sauran dabobin ba. Domin
haka ya kuduri aniyar yin jela da kan sa domin baiwa sauran talakawan sa.
Daga nan sai ya fara aikin yin jela iri-iri daidai da kowace dabba dakuma launin
ta Yayinda ya kammala sai ya shaidawa gunduri da ya kira sauran dabbobi gaba
daya domin kowa ya zabi irin jelar da zata dace da ita. An kuma shaidawa gunduri
da ya tara dabbobin duk a majalisar zaki, kana ya tabbatar bai manta da kowa
ba.
Yayinda ya kammala cikin dawa kiran sauran dabobi wadanda ke nesa da kusa har
dare yayi, kana dabobi suka fara
hallara a majalisar zaki dake cikin duwatsu, saidai gunduri malalaci ne kadai
bai zo ba. Yana gani tafiyar da nisa kuma ya shaidawa wasu daga cikin dabbobin
dake tafiya majalisar cewa su shaidawa sarkin dawa baijin sukunin zuwa amma
duk abinda sarki zai bayar sai a karbar masa nasa. Gunduri yayi imanin cewar
sakon sa zai kai ga sarki ya cigaba da gyangyadi.
Sarkin dawa ya baiwa dukkan dabbobin da suka hallara jela kowa ta zabi irin
wanda zai dace da jikin ta. Amma zaki yayi kuskure saboda idanun sa na gardama,
shine ma yasa kurege ya dauki jelar da tafi karfin jikin sa, yayinda Giwa ta
dauki jela dan kari, wanda bai dace da girman jikin ta ba. Yayinda dukkan jelar
aka baiwa dabbobi, sai zaki ya lura cewa, gunduri bai zo ba.
Sauran dabbobi sai taya juna murna sukeyi da samun jela, yayinda birrai suka
gama murnan su sai suka tuna ashe gunduri
yayi musu sako wajen sarki, sai suka shaidawa zaki sakon gunduri. Sarkin dawa
yayi fushi saboda ganin gunduri ya ki bin umurnin sa shine ya dauki 'yar karamar
jela ya baiwa birrai su kai masa, su kuwa a kan hanya sai suka hada da nasu
jelar. Sukace kamata yayi su koyawa gunduri darasi, domin su a ganin su bai
cancanci samun kyautar sarki ba, sai suka hada
da nasu jelar. Dayin haka sai suka tashi da jela mai tsayi kuma suka jidadin
hakan. 9
9 Page 10 11
10
Febrairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio Da suka shiga inda gunduri
yake sai suka nuna masa kyautar da sarki yayi musu ta jela, kuma suka shaida
masa abinda
sukayi da jelar da sarki ya basu su kawo masa domin koya masa darasi. Nan gaba
suka ce masa tilas ne gunduri ya bi
umurnin da sarkin dawa ya bayar kana ya daina kashe jikin sa.
Gunduri yayi bakin ciki asinun, amma rago ba abinda zai iya yi, saboda haka
ne har yau gunduri baida jela kamar sauran dabbobi.
WHEN HIPPO WAS HAIRY.
WACE DABBA CE TA HATSARI A DUNIYA. 1Min 35 Secs.
Amsar wannan tambaya zata baka mamaki, zakace meyasa ma banyi tunanin haka
ba. Wannan dabba kuwa itace dan
adam. Ada munyi zaton cewa halittu basa aiki, anyi sune dai kawai domin muyi
amfani dasu kamar yadda muke bukata. Munga kuma muna da ikon canja duk abin
da muka ga dama ko mu lalata su haka ne kuwa mukayi, wanda har yanzu
wasu mutane keyi.
Wani kwarare kan muhalli Gerald Durrel ya baiyana lalata muhalli kamar haka:
-'
Duniya abuce mai rauni kamar sakar tautau in kataba zare daya sai sauran su
lalace. Bawai kawai taba zaren mukeyi bama yanzu hudawa mukeyi baki daya'.
Ga wasu hanyoyin da zamu bi domin yin gyara, hanya ta farko da zamu dauka
itace koyon sanin yadda halittu suke. Koyon
zai taimaka mana fahimtar su. In munfahimce su ne zamu iya sanin yadda zamu
kula dasu da sauran abubuwan dake raye ciki harda mu kanmu. Wata kila mune zamu
gyara zaren tautau da ya lalace. '
Kanajin cewa zamu yi hakan? Munyi imani za mu yi.
CHONGOLOLO.
HUJJOJI MASU AMFANI CIKIN HANZARI: 1 Min 47 Secs. MA'AIKATAR KALLON TSUNTSAYE:
A ina ne a Afrika za kasami daukaci ma'aikatar da ta himmatu wajen kula da
tsuntsaye Sai a karamar kasar nan watau Gambia. Saboda wadan nan abubuwa ya
maida ita aljannar kallon tsuntsaye.
* Tsuntsaye iri-iri har 550 da suka taru a fili mai fadin dubu 11 da 300 murabba'i.
* Yankin dube ido da aka tanadar tare da dukkan kayan da ake bukata, domin masu
sha'awar y a w o n dube ido ko shakatawar hutu.
* Wurin dake da lafiya kuma ga yanayin muhalli mai kyau.
* Kasa kenan a duk fadin Afrika ta yamma, inda kallon tsuntsaye ya zama wurin
hutu mai makon k a i ziyarar aiki.
Hanya mafi sauki a Afrika ta yamma domin samun tsuntsayen yankin da kuma,
* Sanin inda za ka sami duk irin tsuntsun da kake da sha'awa. Kana iya zuwa
Abuko inda halittu ke nan yadda suke na ainihi domin ganin tsuntsaye cikin sauki
ko ka tafi Tanji inda sansanin tsuntsaye suke iri-daban daban inda zaka sami
tsuntsaye har iri dari uku a bakin teku mai tsawo kilomita biyar, ko kaje sansanin
Tendaba na tafiya cikin kurmin domin sanin yadda tsuntsaye suke.
Amma ba a Afrika ne kadai tsuntsayen suke ba. Karamar kasar Costa Rica dake
tsakiyar Amurka, wanda tayi girman 10
10 Page 11
11
CHANGE Radio Febrairu 2000 (Hausa) Gambia sau biyar, ita ma tana
da masana'antar kallon tsuntsa Tana da tsuntsaye iri-iri har 8 50, ga kwaciyar
hankalin siyasa, saukin rayuwa kayan marmari daban-daban. Wani mai yawon bude
ito da ya ziyarci kasar yace yaga irin tsuntsaye
har 460 cikin makwan uku kacal.
AFRICAN BIRD AND BIRDING
HAMAKDA MAFI GIRMA A DUNIYA: 22 Secs.
Mai fadin kilomita miliyan 8 da dubu dari hudu Hamadar Sahara itace mafi
girma a duniya baki daya kuma tana dada
karuwa. Wannan yakai kusan dukkan hamadar da ake dasu a duniya in an hadasu
wuri guda, kuma ya kai girman Najeriya har sau takwas.
ABOVITAE.
SIN TA HARAMTA SARAN KATAKO, AMMA TA KARA YAWAN WANDA TAKE SHIGOWA DASHI 25
Secs.
Yanzu kasar sin tana sayo katako daga ketare kimanin mita miliyan hudu murabba'i
daga farkon shekarar 1999, bayan da ta haramta sare itacen katako a cikin kasar
sabod saboda ambaliyar da ta auku. Shigo da katako ya karu da kimanin
kashi daya cikin 3.
Masana muhalli sunce haramta saran katako a Sin ya kara saran katakon a kasashen
dake makwabtaka da ita.
arbovitae.
MATSAYIN TABA KAN DUSHEWAR GANDUN DAJI: 1 Min 7 Secs.
An kiyasta ana asarar guma-gumai dubu metan a duk shekara a sakamakon noman
taba wanda yakai kashi biyu cikin dari na dazukan duniya kamar yadda binciken
da aka gudanar ya nuna, wanda kuma aka buga a mujalla da akayiwa lakani
shawo kan taba.
Anfi yin asarar dazuka ainun a kasashen dake noman taba musamman a kasashe masu
tasowa dake kudancin Afrika, da sassan gabas ta tsakiya da kudancin Amurka da
Asia.
Tsakanin 1990 da 1995 anyi amfani da tan miliyan 11 da dubu dari hudu na guma-gumai
wajen yin taba sigari.
Koda shike wasu kasashen suna karfafawa manoman su gwiwa domin noman guma-gumai
domin amfani dasu, amma har yazu wadanda aka rasa ba asamo su ba.
Sunyi imanin cewar gushewar dazuka kan taba baida muhimmanci ko illa kamar
yadda mawallafin mujallar Helmut Geist ya fadi.
arbovitae.
WANDA YA KAFA KUNGIYAR KARE DAZUKA YA ZAMA KAKAKIN KAMFANIN KATAKO: 1 Min
1 Sec.
Dr. Patrick More, wanda yana daya daga cikin wadanda kafa kungiyar kare dazuka
da sauran halittu, tuni ya sami wata sana'ar da daya daga cikin kungiyoyin da
suke gaba da juna. Yazu yana aiki da kamfanin nan mai suna kawancen
Biritaniya da Colombia kan gandun daji, kawance manyan kamfanonin dake tu'amalin
saida ka tako, wanda ake zargi da karfafa gwiwar sare itatuwan katako.
Koda shike bai sha da dadi daga kungiyar sa ta farko, domin kuwa yayinda a wani
taro ya fara jawabi kan shirin canje-canjen
aiyukan katako, sai wani ya harbe shi da gurasa. A sakamakon nuna bacin rai
kan yadda More din ya bada kai game da yunkurin da suka fara tun farko.
Amma shima cikin fushi sau ya dauki gurasar ya rama harbin da akayi masa kana ya fice daga zauren taron da bacin rai. agitpro. 11
© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw