Go Back
Communicating for Change

Document Body Page Navigation Panel

Pages 1--14


Page 1 2
1
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

Raya Kasa ABINCI MAI JIKI

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Ta Hade Madagascar Da Vietnam Kan Aikin Abinci 1min. 51secs. 9
Madagasca da Vietnam sun Hade ta Fuskan Hadin kan Kudancin Duniya
Donin aikin Samar Da Abinci
Masifun da dan Adam Kejanyow: Babbar Hanyar Auruwar Yunwa 48 Sec. 13 Hujjoji daga hukumar abinci da aikin gona ta duniya (FAO)

Matan Afrika Sun Samo Sabuwar Dabarar Yaki Da Yunwa 3mins 13sec. 6 Mata a Kenya sun kasance sahun gaba kan aikin gona.

KIWON LAFIYA
Tsohon Ministan Lafiyar Naheriya Ya Bukaci Cigaba Da Yaki Da
Cutar Kanjamau 5min. 4sec. 6
Tsohon Ministan lafiya ya bukaci shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

da ya ja damarar yaki da cutar kanjamau.
Dalar Miliyan 750 Domin Yallafawa Asusun Yaki Da Cututukan Yara 2mins. 15sec. 3 Kungiyar Bill Gates ta bada kudi kan aikin binciken allurai da aiwatarwa

domin yaki da cututukan yara kanana.
Yara Sun Bada Gudumawa Kann Yaki Da Cutar Kanjamau 2mins 18sec. 4 Yara sun sami damar baiyana ra'ayin su kan cutar kanjamau

MUTANE
Yawan Yara Marayu Saikaruwa Yakeyi A Afrika 1min 4sec. 12 Yaran Afrika marayu sun karu yanzu haka five da dacan.

Majalisar Dinkin Duniya Na Karfafa Hakkin Nakasasu 42sec. 12 Akwai nakasasu miliyan dari biyar a duniya.

KWADAGO
Kenya Ta Yi Niyar Saida Jarin Tashar Jiragen Ruwan Ta Daya Tilo 1min 2sec. 11 Gwamnati Kenya tana tunanin saida jarin tashar jiragen ruwan ta daya saboda

yawan cin hanci da rashawa.

CINIKAYYA
Kofi Anan Yayi Magana Kan Rashin Adalicinkan Dangatakar Cinkayyar Duniya 1min. 58sec. 4

An ja kunnen kasashe masu arziki da cewa kaanan kasashe zasu ki aminciwa game
da sabon tsarin cinikayya na duniya muddin ba an inganta shi ba.

Yanayin Muhalli KASUWANCI
Kanfanin Kasar Ingila Zai Sayi Jarin Kamfanin Ruwa Na AfrikaTa Kudu 2min 40sec. 5
Wani babban kamfanin kasar Ingila dake tace ruwa zai sayi wani kamfanin ruwa
na kasar Afrika ta kudu domin fadada aiyukan sa a duniya.
1
1 Page 2 3
2
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

GANDUN DAZUZUKA
Ansa Sami Sabon Yankin Gado A Afrika Ta Kudu 2min 37sec. 9 Wani gandun daji a yankin Kwa Zulu ya zama yankin gado na duniya.

Wani Shirin Doka Na Barazana Ga Wani Kurmi Mafi Girma a Duniya 1min 48sec 4 Kamun kafar da manoma keyi na barazana ga wani makeken kurmi a kasar Brazil.

MASIFA
Wani Bal'iya Aukawa Kasarindiya 44sec. 12 Jihar Orissa dake gabar teku a kasar India ta fada bala'in guguwa.

YANAYI
Kamfani Sarrafa Shara Ya Fara Samu Riba Daban-daban 8mins 22sec. 7 Bincike a kasashe takwas da aka gudanar ya nuna cewa shigar jama'a cikin aiyukan

sarrafa shara a birane kwalliya na biyan kudin sabulu ga rayuwar jama'ar

DABBOBIN DAWA
Dan Kasar Japan Da Aka Daure A Thailand Ya Karfafa Cinikin Malam-Bude Littafi a Ghana 1min 43sec. 10

'Yan kasar Ghana sun koyi cinikin Malam-Bude Littafi dake da riba.
Cututtuka Na Barazana Ga Zakunan Afrika Ta Kudu 2mins 21sec. 3 Gandun dajin kruger a Afrika ta kudu na fama da cutar fuka na dabbobi.

Dabban Dawan Afrika Dake Fuskan tar Hatsari Yazu Ya Sami Sauki 1min 19sec. 5 Mugun dawan Habasha yanzu ya sami sararin rayuwa.
Abubuwan Ban Sha'wa Da Zakayi, Ka Gani Kuma Ka Sani 2mins 16sec. 13 Takaitacen yawo da aikace-aikacen dabbar dawa.

Sashen Yara
Kuregeda 'Ya'yan Zakanya 7mins 56sec. 11 Zakanya dake girmama kurege.
Babu Kifi Ga Dorina 2mins 1sec. 10 Dorina ta kulla yarjejeniya domin ta kasance cikin kogi
Yaya Maciji Kehawa Bishiya amma Bai Da Kafa 29sec. 10 Wani lokaci ciki na zama tamkar kafa.
Karin Maganar Gandun Dazuka 36secs. 10 Duniya zata tumbatse in yawan mutane yayi mata yawa
Dalilin Da Yasa Damisa Ke Boye abincin Ta A Kan Itace. 1min 55sec. 12 Haihuwa daya....... 2
2 Page 3 4
3
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

LABARU
Dalar Miliyan 750 Domin Taimakawa Yaki Da Cutukan Yara 2mins 15sec.
Za afara karfafa yaki da cutukan dake addabar yara kanana, da kungiyar kawance kan samarwa da yiwa yara allura ta duniya (GAVI) da za afara ranar 31 cia watan janairun nan bisa karin kudin cia aka samu. Asusun tallafawa shirin na Bill

Gate dalkuma Melinda Gate ne sukayi tanadin shekaru biyar na daba taimakon dalar miliyan 150 wanda ya hada jimillar dalar mihyan 750 ga kungiyar ta GAVI a ranar 24 ga watan Nuwamba. Bisa samun wannan taimako, kungiyar
ta GaVI ta kuduri aniyar aiwatar da shirin sha yanzu magani yanzu daga ranar 31 ga watan na Janairu. Manya daga
cikin shirye-shiryen sun hada da: -* kokari cikin hanzari domin samar da sabbin allurai da sauran magungunan da ake bukata domin inganta

kiwon laf iyar yara a kasashe masu tasowa. * hanzarta samar da sabbin allurai.
* fadada dukkan kokarin da akeyi yanzu na samar da alluran.
* inganta hanyoyin tabbatar da cigaba da shirin aiyukan. * dakuma maida aikin allurar a matsayin mizanin auna cigaban kokarin kasa da kasa.

Kungiyar ta GAVI ta kunshi wakilai da suka dukufa wajen karf afa gwiwar fadada shirin amfani da hanyoyin gargajiya da na bature a kasashe masu tasowa. Membobin ta sun hada da asusun kula da yara UNICEF, da hukumar lafiya ta
duniya WHO da Bankin duniya, da asusu Bill Gate da na Melinda Gate da asusun Rockefeller da ma'aikatar dake samar da allurai da sauran kungiyoyin dake da alaka da irin wannan Shirin. Da take baiyana shirin kungiyar na GAVI
kan aikin allurar hukumar UNICEF tace shirin an tsara ta yadda za ayi tsimin kudi dakuma rigakafin cutukan yaran. Bawai kawai rage kudin Asibiti dana magani ba, harma da samar da abinci mai gina jiki da kiwon laf iya tare da kyautata
rayuwa yara tun suna kankana inji hukumar ta majalisar dunkin duniya. Da cikin cututtukan dake saurin kashe yara da
shirin zaiyi yaki dasu sun hada da gudawa, da tandau, da cutar shan-inna da bakon-dauro dakuma tarin-fuka. Tuni an samar da kudaden samar da wurare da kayan aikin da za a tafiyar da shirin alluran, inji hukumar ta UNICEF. Kungiyar

ta GAVI zata kuma taimakawa kokarin kasashe masu tasowa dake nuna zumma kan yakar wadan nan cutukan ciki harda cutar shawara.
UNICEF.

Cutar Dake Barazana Ga Zakuna A Afrika Ta Kudu 2mins 21secs. Daukacin zakunan dake gandun dajin Kruger dake Afrika ta kudu suna fuskantan barazanar kamuwa da cutar fuka da
yanzu haka take yaduwa tsakanin dabbobin dake can. Ckutar ta shigo gandun dajin ne ta hanyar shanun da suka ratsa gandun dajin a shekarun 1960s, wadanda suka shafi baunan dake sashin kudancin gandun dajin inda kimanin zakuna
dubu biyu da zama. Yawan zakuna da sauran dabbobin dawa da suka kamu da wannan cutar ba asan iyakan su ba. Amma bauna ce ke saurin yada cutar ta hanyar tari da sukeyiwa juna a fuska inji Dr. Micheal Woodford shugaban
kungiyar kwararu kan cutukan dabbobi ta duniya.
Basafai ne zakuna ke yada cutar ga sauran dabbobi ko 'yan uwan su ba. saidai sukan yi kiwo cikin garke inda da yawa
daga cikin su ke kamuwa da cutar in sunci baunar da ta kamu da cutar fukar, inji Dr. Woodford. Ana kyautata zato zakuna ne suka fi kamuwa da cutar. Gwajin da aka gudanar kwanan nan ga zakuna 30 kimanin kashi 90 cikin dari duk

sun kami da cutar. Babu maganin da aka samu kawo yanzu, kana babu wata allurar rigakafi. Jamiár gandgandun dajin suna duba yiwuwar raba tsakanin dabbobin da suka kamu da cutar da wadanda suke da lafiya ta hanyar kafa shinge a
sashin kudancin gandun dajin. Su baunan da aka killace za a kashe su ne domin kauda cutar a yankin. Su kuwa
wadanda basu kamu da cutar ba daga bisani za ayi amfani dasu ta yadda zasu hayayyafa domin maye gurbin wadanda suka mutun. Za akuma gudanar da bincike domin tantance tsawon lokacin da zai dauka domin tabbatar da cewar cutar

ta kare kwata-kwata bayan an kauda wadanda suka kamu da cutar. Ko kuwa za a yanka daukacin baunar dake 3
3 Page 4 5
4
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

wannan gandun dajin na Kruger. Da yake gargadi game da fargabar dake akwai darektan kungiyar kula a dabbobi ta Afrika Kark R. Stanley Price yace bisa rashin kwarin gwiwa cutar za a iya tsammanin ta kan wata annoba ce da ta

aukawa dabbobin. Amma saboda yawan dabbobin dakuma yadda ba aiya shawo kansu game da cututtuka shine ya sanya abin yayi tsanani.

Wata Sabuwar Doka Da a Ke Son Kafawa Na Barazana Ga Gandun Daji Mafi Girma a Duniya 1min. 48sec.
Gwamnatin Brazil ta bullo da wata sabuwar doka dake son bada dama wajen yin amfani da makeken dajin nan na Amazon kan aikin gona inji masu kula da muhalli. Sabuwar dokar zata bada dama wajen maida irin wadan nan
dazuzuka zuwa gonaki bakuma tare da wani la'akari ba daga Gwamnati. Haka kuma dokar zata bada kwarin gwiwa wajen maida dazuzukan gargajiya su koma wadanda ake sarrafa su. Haka kuma zata bada damar lalata sauran wrare
dake bakin koguna. Masu hangen abinda kaje yazo sunce dokar zata sanya yankunan da ake tinkaho dasu a Brazil
cikin hatsari. Wani yace ainin dazuka na asali suna Brazil, amma yanzu Brazil tayi asarar rabin irin wadan nan dazuzuka.

In har wannan doka ta sami shiga zata canja daukacin tsarin dkokin muhalli inji Darektan kula da muhalli na Brazil Bobert Buschbacher, bugu da kari dokar zata sanya sauran dazukan kasar su kasance gonaki. Ita wanna dokar ta biyo
bayan kamun kafa mai tsanani da majalisar manoman kasar keyi ne. Wanda kuma tayi ta yadda ya baiwa kowa
mamaki, hartta ita hukumar kula da muhalli ta Brazil (CONAMA) ba a tuntube ta ba wajen gabatar da dokar. Shima Ministan kula da muhalli Sarney Filho bai shiga cikin tattaunawar ba kana yace baya goyon bayan ita dokar. Ma Abuta

muhalli suma suna kamun kafa, domin ganin dokar bata samu shiga ba amma kuma ana gani sun makaro. WWF.

Kofi Anan Yayi Magana Kan Rashin Adalci a Dangatakar Cinikayyar Duniya 1min 58sec. Babban sakataren majalisar dinkin duniya kofi Anan ya bukaci kasashe masu arzikin masana' antu da su kauda duk
shingen dake hana ruwa gudu kana su bude kofofin kasuwanin su domin hajojin kasashe masu tasowa, domin kuwa inji shi duk wani tarnaki ga kasashe masu tasows, bazata sabu ba. Cikin jawabin da ya shirga gabatarwa taron kungiyar
cinikayya ta duniya WTO a Seatle cikin watan Nuwamban da ya shige, babban sakataren ya baiyana fater cewa taron
zai kasance wurin da za kafa harsashin adalci kan cinikayya ta duniya.

Muddin ba mum tabbatarwa da kasashe masu tasoua ba na bude kofofin kasuwanin mu ta yadda zasu amfana to kuwa ba zasu amince ba. Hakan kuwa na iya zama mai muni ga su kasashe masu har ma da duniya baki daya. Anan wanda
aka hanwa gabatar da jawabin bayan da masu zanga-zanga sukayi kokarin hana taron ya zargi kasashe masu arazikin
masana'antu kan yadda suke cigaba da maida kasashe masu tasowa saiyar ware a kasuwanin su. Wasu kasashe masu arazikin suna zargin kasashe masu tasowa da laifin maida su jujin zuba hajojin su.

Amma a kashin gaskiya sune suka maida kasashe masu tasowa jujin baje kolin hajojin su ta hanyar rangwami kan farashin kayayyakin kayayyakin nasu wanda hakan ya jefa miliyoyin manoma cikin haki kakanikayi inji babban sakataren
majalisar. Ganin cewa ciniki yafi bada taimako Mr. Anan yayi kira ga samun rangwami kan kudin fito da sauran tarnaki da ake sanyawa kasashe masu tasowa. Kaseshen da sukafi talauci kuwaa sai a dauke musu kudaden da suke biya
domin shigar da hajojin su a irin wadan nan kasuwanin duniya inji shi. Da yake gargadi kan babakere kan harkar cinikayyar game da manufofi da gazawa, Mr. Anan ya bukaci kasashe masu arzikin masana'antu da suguji warware
nasu matsalolin ta yadda zasu karawa kasashe masu tasowa matsaloli. UNO 4
4 Page 5 6
5
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

Yara Sun Bada Gudunmawa Kan Yaki Da Cutar Kanjamau 2mins 18sec.
Anyi buki na 12 na ranar yaki da cutar kanjamau. Wani fin da akayiwa taken YANKIN SASHIN SAHEL' wanda yara suka rubuts na farko cikin jerin finunuka 30 an gabatar a tasoshin talabijin na kasashe akalla goma na Afrika ciki

harda Najeeriya. Fin din yayi magana ne kan irin illar dake akwai ga cutar kanjamau kan yadda yara suka gani. Fin din yana dauke da wasu sassa uku na wasu wadanda sukayi na ukun farko da suka rubuta a gasar insha'i da akayi na yara
daga ko ina a duniya. YANAYIN SAHEL an shirya shi ne ta yadda ya kula da irin matsalolin cutar a Afrika inji jami'an
hukumar TVE de suka shirya fin din. An kuma shirya fin din ne cikin harsunan da mutanen ke ji domin ya dac da al'adin jama'ar.

Hukumar talabijin na TVE ne ta shirya gasar domin yayi kicibis da ranar yaki da cutar ta kanjamau, wanda akayiwa lakani 'YARA DA MATASA KU JI KU KOYA DOMIN KU RAYU, '. Fiye da labarai 2,000 ne aka samu da ga
yaran, wanda hakan ya nuna cewa yaran suna saneda ita wannan mugunyar cutar. An zabi wadanda sukayi nasara su 30 daga yankuna dabandaban na duniya, wadanda za a maida labaran da suka gabatar cikin hotunan silma. Haka
kuma tashar ta TVE zatayi amfani da dukkan labarai 2,000 da yaran suka gabatar ta hanyoyi daban-daban.
Babu daya da za a yar a kwandon shara, wadanda ba ayi silma dasu za a adana a rumbun adana takardun tarihi domin
yin amfani da shawarwari da yaran suka bayar a kokarin da akeyi na yakar cutar ta kanjamau, inji kungiyar mai zaman kanta. Kamar yadda TVE tace wannan aiki ya sami goyon baya da kuma sanya hannu daga muhimman 'yan Afrika

dake wasan kwaikwayo. Za akuma samar da kukkan finafinan 30 bayan am kammala su a faife kana za a rarraba ga kungiyoyin dake yaki da cutar kanjamau dakuma kare kamuwa da ita. TVE na shirya finafinai domin wayar da kan
jama'a kan muhalli da sauran aiyukan cigaban kasa tare da rarraba wadan nan finafinan a kasashen duniya ta hannun
wasu manyan hukumomi irin su CFC da TVE ga wakilan su a Najeriya. TVE.

Kamfanin Kasar Ingila Ya Sayi Jari a Kasuwar Afrika Ta Kudu 2mins 40sec. Enving Holdings wani kamfanin tace ruwa dake Afrika ta kudu an saida jarin sa ga kanfanin Weir Westgarth dake
Glasgow a kasar Scotland a Ingila kan kudi fam miliyan uku da dubu dari bakwai. Kamfanin Weir na kasar Ingila ya kware kan sha'anin tace ruwan teku mai gishiri, domin amfani a gidaje da masana'antu. Kamfanin na Weir yace ya sayi
kamfanin na Enving ne dake birnin Cape Town wanda kuma ke da of is a Johannesburg da Botsuwana domin inganta aiyukan sa, wanda yanzu za a rika kira ga Weir Envang domin hade kan kwararu na kamfan on in wuri guda.

Wani kakakin kamfanin yace bisa wannan sabon tsarin hedkwatar kamfanin zai kasance a Glasgow, wanda zai rika samar da tsarin aiyukan tace ruwa, domin bukatar dinbin jama'a da masana'antu. Tsarin zai hada da fasahar Envang da
sauran kayayyakin da yake sarrafawa. Paul Capell manajan darektan kamfanin Weir wanda kuma shine shugaban sabon kamfanin Weir Envang yace sayen kamfanin ya basu damar samun fasahar da suke bukata domin fuskantar
karwar bukatar kayan su a kasuwani da masana'anru kan ruwa.
Haka kuma zai basu damar taka rawar da suke bukata a kasuwar. Zai kuma kara samar da dama dake akwai a kamfanin Weir tare da fadada Envang ga duniya baki daya. Haka kuma zai basu damar taka rawar da suke bukata a
kasuwar. Zai kuma kara samar da dama dake akwai a kamfanin Weir tare da fadada Envang ga duniya baki daya. Amfani da fasahohin dake akwai somin tabi ne'amma kuma yayinda aiki ya kankana babu sauran rufa-rufa musamman
in anyi la'akari da kokarin da duniya keyi na kare muhalli tare da adana ruwan da ake dasu sosai. Kamfanin yace haka kuma yarjejeniyar cinikin ta sanya kamfanonin biyu zasuyi aiki kafada-da-kafada wajen samr da tatacen ruwa a kasuwanin
Afrika ta hanyar amfani fasahar Weir na tace ruwan gishiri dana taku wanda akafi sani da fasahar tatacen ruwa (MSF). 5
5 Page 6 7
6
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

Kamfanin Envang wanda ke da dimbin basira wajen yin tsimin ruwa tare da magance matsalolin ruwa wanda shima ke samar da nasa rukunin ruwan tuni ya fara aiki da sabon kamfanin na Ingila. Kamfanonin biyu sunyi aiki na tsawon

shekaru biyu kuma sun samar da tatacen ruwa a tashar Tukuta a Eskom, da tashar wutar lantarki ta Afrika ta kudu.
Kamfanonin na samar da cubic 12,500 na ruwa kowace rana. London Press Service

Dodon-Dawan Afrika Dake Fuskantar Bacewa Yanzu Ya Bullo 1min 19sec. Dodon-dawan kasar Habasha, wanda shine dodon-dawa na hakika yanzu an sake gano su. Ganowar kwanan nan da
akayi na irin wadan nan dabbobi a yankunan dutsen wollo dake sashin arewacin kasar Habasha ya sanya an sami kwarin gwiwar sake farfado da kokarin da akeyi na wanzar da dabbobin tare da kasancewar, wadanda ake zato da
basu wuce tsakanin dari hudu zuwa dari biyar ba yanzu sunkai 650. Hakan yakara inganta damar kare su a gandun daji. Kamar yadda masana kimiya suka baiyana su dacewa sune na kwarai kuma 'yan kalilan dodon-dawan na
Habasha sune kuma karen dawan Afrika. An fara ganin su ne a farkon karni na 19 a tsaununan Siemens inda dududu
basu shige 50 ba. An sami mafiyawan su kimanin 180 a yankin duwatsun Bale na gandun dajin dake kudu maso gabashin kasar. Wannan ganowar na baya ya sanya yankin Wallo na biyu a wurare mafi muhimmanci kan dodon-dawa

baya ga Bale, inji Dr. claude Sillero-Zubiri na jami'ar Oxford, wanda ya ja goranci tawagar da ta tabbatar da kasancewar dabbobin a yankin na Wallo. Wannan kuwa ya kara inganta matsayin gandun daji na irin wadan nan dabbobin.
AWF.
Sharhi

Maran Afrika Sun Bullo Da Sabuwar Dabarar Yaki Da Yunwa 3mins 13sec.
Wata kungiyar mata a kasar Kenya, wanda ake kira da harshen kasarIvuso ya Mayatta ta zama zakara gwajin dafi wajen bullo da fasahar noma ga yankunan dake fama da talauci. Ivuso, wanda ke nufin kokarin hadin kai tayi nasarar

karfafa inganta irin gujiya domin samar da abinci mai gina jiki. Matan kungiyar Ivuso sun fara jin labarin shirin inganta noman gujiya ne daga masana kimiya dake aiki a cibiyar binciken aikin gona dake yankin Arid (ICRISAT) dakuma
cibiyar binciken aikin gona ta Kenya KIRI) ,wadanda suka dukufa kan aikin inganta noman gujiya a sashin gabashi da
kudancin Afrika wanda Bankin duniya ke tallafawa. Sun fahimci cewar na samar da kayan gina jiki da ake bukata kamar su bitamin da kitse da sauran su, domin amfanin su a yankin na Arid. An kiyasta kimanin kashi 30 cikin dari na

yaran dake kasa da shekaru biyar basu da nauyin da ya dace dasu, saboda rashin isashen abinci mai gina jiki. Irin wadan nan yara zasu ci moriyar cin gujiya wanda ke kunshe da kayan gina jiki ninki goma fiye da gujiyar da ba a inganta
ta ba kuma ninki biyar kan bitanin A kuma ninki uku na bitamin C. Haka kuma gujiya tafi nama arha wajen samun abinci
mai gina jiki. Bisa wannan sabuwar dabara, Ivuso tayi aiki domin inganta wanna abincin ta hanyar kara yawan amfani da gujiya tsakanin al 'umomin dake zaune a karkara. Matan suna toya kosai da biskit da sauran su da akayi da garin

gujiya, da aka gauraya da alkama da garin gero da maiwa.
Mun inganta irin abincin da ake ci a nan'inji Diana Nzomo'wanda ta kafa kugiyar. Cibiyar ICRISAT ta inganta hanyoyin
fasahar samar da abinci da noma shi musamman mata a India, da Kenya da Malawi da Tanzaniya dakuma Uganda domin kyautata amfani da shi. Haka kuma gujiya abune da ake nomawa domin samun kudi, musamman dayake sai kara

fahimtar ta akeyi. aka kuma ana saida ita a kasashen Asia, da Arewacin Amurka dakuma Turai, akwai alamar cewar bukatar gujiya ta ninka abinda Kenya ke samarwa. Kusan kowani sashi na gujiya na da amfani. Ainihin jikin ta na bada
kariya ga dan adam yayinda bawon ta dabbobi na ci, ganyen ta kuma na amfani. Haka kuma gujiya na jurewa yanayi
tare da inganta dausayin kasa. Kowace kadada ta gujiya na samar da kimanin kilo 40 na taki. Haka kuma jijiyoyin ta dake shiga kasa na taimakawa wajen hana zaizayar kasa. Babban abin muhimanci shine gujiya bata bukatar ruwa mai

yawa domin girma. domin tana iya girma koda anyi kamfar ruwa. Saboda amfanin ta masana kimiya sunyi ikirarin babu wani tsiro da yakai gujiya samar da abubuwa da dama kamar nata musamman a yankunan dake fama da karancin
ruwan sama. CGIAR: 6
6 Page 7 8
7
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

Tsohon Ministan Najeriya Ya Bukaci Cigaba Da Yaki Da Cutar Kanjamau 5mins 4sec
An bukaci Gwamnatin Najeriya da ta kuduri aniyar kauda cutar kanjamu watau AIDS, ta hanyar cigaba da samar da kudaden da ake bukata, wajen wayarwa da jama'a kai tare da karfafawa masu fama da cutar gwiwa. Farfesa Olikoye

Ransom Kuti tsohon Ministan Lafiya ne ya bukaci haka yayinda yake gabatar da kasida a cibiyar nazarin harkokin waje (NIIA) cikin watan Disamba. Da yake magana kan cigaba da matsalar cutar ta kanjamau a Najeriya dakuma
Afrika farfesa Ranson Kuti ya tabo tarihin cutar ta AIDS da shirin shawo kan ta a Najeriya inda yace kudin da ake
samarwa a duk shekara ya tashi daga naira miliyan daya zuwa miliyan biyar tsakanin 1986 zuwa 1992. Ya kuma fadi daga shekarar 1993 wanda yakai mafi kankanta naira dubu dari uku a shekarar 1999.

A halin yanzu kuma yawan mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya tashi daga kashi biyu cikin dari na yawan jama'ar kasar zuwa kusan kashi shida cikin dari a 1999. Senegal ta fara samun cutar ne a 1986 shekara guda da
Najeriya, amma yanzu tana da kasa da kashi daya cikin dari na yawan mutanen ta da suka kamu da cutar. Ransom Kuti yace saboda tashi tsayen da shugaba Abdou Diof da kuma shugabanin addini da suka taimaka domin kare yaduwar
cutar bisa alwashin da shugaban kasar yayi a Najeriya. shugaba Olusegun Obasenjo kwanan nan ya ware naira miliyan 50 domin yakar cutar. Wanna ya hada da mata masu juna biyu. Majalisar dokokin kasa ta kara kudin zuwa naira
miliyan 100, wanda ya nuna kudurin da shugaban yake dashi na yaki da cutar.
Ransom kuti yace daga wuraren da za afi bada fifiko sun hada da mata masu juna biyu da ke dauke da kwayoyin cutar HIV/ AIDS, da yaki da cin hanci ga masu sayowa da raba magunguna, da yaki da karuwancin yara kanana dakuma
kauda jahilci kan cutar. Kusan dukkan yaran da aka haifa tare da kwayoyin cutar daga Afrika ne a duniya. Koda yake afrika kimanin kashi daya ne cikin dari na al'umar duniya, yawan matan dake da junabiyu ke dauke da cutar yakai kashi
biyu cikin dari a Nageriya a 1992 zuwa kashi shida cikin dari a 1999. Otukpo ke da mata mafi yawa da suka harbu da cutar a jihar Binuwai. Sai kuma Geidam a jihar Yobe dake da mafi kankantan matan da suka harbu da cutar. Wannan
kuwa ya nuna ana haihuwan yara da dama tare da kwayoyin cutar. Kusan duk irin wadan nan yaran suna mutuwa kafin sukai shekaru biyar a duniya. Yawan su kuwa zai karu domin kowace uku daga cikin mata hudu basu da sukunin
samun kula da kiwon lafiya, inji Farfesa Ransom Kuti. Cutar tana kama 'yammata wadanda ba a haifesu da ita ba ta
hanyar karuwanci saboda talauci. Wannan kuwa inji Ransom Kuti ruwan dare ne gama duniya,. Akwai kimanin yara miliyan 30 zuwa miliyan 170 dake gararamba a hayoyi a duniya saboda matsalolin rayuwa Kimanin kashi 80 cikin dari

na yaran suna amfani da miyagun kwayoyi. Wani bincike da aka gudanar a Lagos, irin wadan nan yaran daya daga cikin kowani hudu na dauke da kwayoyin cutar ta kanjamau. Wanna kuwa shine na biyu baya ga karuwanci.

Matsalar cutar kanjamau ta kara kamari saboda yadda jama'a ke daukar masu fama da cutar. Wadanda suka kamun suna jin kunyar fitowa fili suce suna dauke da ita cutar. Haka kuma 'yan uwan wadanda suka mutu a sanadiyar cutar
sukan roki likita da kada ya rubuta cewar sun mutu ne a sanadiyar cutar ta kanjamau. Wata sa'ar akan bar masu fama da cutar ba mai kulawa dasu har su mutu. Irin wanna yakan sanya mai fama da cutar ya ja bakin sa ya tsuke duk da
cewa yana fama da cutar saboda gudun abin kunya. Cikin jawabin nasa Ransom Kuti ya zargi gwamnatocin Afrika
dake karkatar da kudin da aka tanadar domin yaki da munguyar cutar.

Kashe kudi ta hanyar da ta kamata shine a'ala ga masu fama da cutar kanjamau a Afrika domin ta haka ne za a iya ceto masu fama da cutar inji shi. Haka kuma ya tabo nazarin da majalisar dinkin duniya tayi, wanda ya nuna dalar 12 ne kacal
ke isa ga mara lafiya dake fama da cutar daga cikin dalar 100 da ake warewa mai cutar a Afrika. Yaki da mugunyar
cutar da wannan gwamati ta fara, ne da tallace-tallace da sanarwa ta kafofin yada labarai domin kira ga 'yan Nageriya da su taimakawa masu fama da cutar domin samun sa'ida, wanda wasun su sun kamu ne ba bisa laifin su ba.

Obasi Ogbonnaya 7
7 Page 8 9
8
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

Shirin Sarrafa Shara Na Al'uma Amfara Samun Amfani Dabban-daban 8mins 22sec
Binciken da aka gudanar kan aikin kula da sarrafa shara a biranen wasu kasashe masu tasowa da jama'a ke shiga, ya nuna cewar am fara samun amfani a fuskoki iri-iri ciki harda kiwon lafiya da zamantakewa kamar su: -*

tara shara sosai a kwandunan shara a wajen gidaje: * raguwar sharar da ake zubarwa cikin koguna da hanyoyi ko konawa
* raguwar dattin dake barbazuwa tsakanin makwabci-da-makwabci.
Sauran amfanin da ake samu sun hada da shigar mazauna biranen cikin aiyukan sarrafa shara gadan-gadan, da raguwar cututukan dake addabar yara, karuwar amfani da bahaya dakuma reguwar yaran dake bin bola suna tsince-tsince.

Binciken ya gudana ne a Afrika ta yamma da Asia da wani kamfani dake Netherlands mai suna shirin kula da birane na kwararu (UWEP), wanda hukumar tallafawa ta kasar Netherlands (NEDA) ta samar da kudin tare da ma'aikatar
harkokin waje. Shirin ya tara bayanai kan shigar al'umomi da kananan kamfanoni kan aikin sarrafa shara tare da
taimakawa wajen kula da sharar a kasashe masu tasowa.

Shigan al'umomi cikin aikin sarrafa shara na nufin shigar manyan cibiyoyi kan aikin irin su kananan kamafanoni (MSE) da kwamitocin gundumomi, da kungiyoyi masu zamon kansu (NGO) da kananan hukumomi da kungiyoyin mata 'yan
kasuwa. Sauran sun hada da sarakunaan gargajiya, dashugabanin addini da malaman makaren tu da 'yan siyasa daku
ma matasa. Al'umomin da aka gudanar da aikin sune irin wuraren nana na share wuri zauja dake da mutane tsakanin 1500 zuwa 5,000. Sune kuwa gundumar Djicoromi Para dake Bamako na kasar Maali: da gudumar Gueule Tapee

a Dakar, Senegal: dagundumar Medina Fass a Thies Senegal:. Da wata gunduma a Ouagadougou a Burkina Faso Dakuma gundumar Siddharathara a Colombie Sri Lanka. Sauran sune gundumamin kasashen Napal, da Pakistan da
Filifins dakuma Indiya.
Bullo da shirin sarrafa shara na al'umomi ya karfafa hadin kai tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu (NGOS), da kungiyoyin al'umomi (CBOS) da sauran kananan kamfanoni. Haka kuma kuma yekuwar tsabtace muhalli ya sami
karbuwa ga shirin hukumomin kula da birance tare da goyon baya wajen kafa dokoin kula da muhalli. Matsalolin kula da aikin sarrafa shara, irin su yawan karuwar jama'a, karancin ma'aikata kin shigar al'umomi, rashin kayan aiki ga
hukumomin kula da birane da kudin aiwatar da manufofi da shirye-shiryen aikin. Da kuma rashin yarda tsakanin masu tafiyar da qannan aikin. A sakamakon haka sai jama'a su fara zubar da shara a hanyoyi da koguna, sanu kan hankali
sai shara ta fara taruwa inji rahoton. Domin haka sai hukumomi su kasa shawo kan sharar.
Al'umomin sai su zama basu da zabi, domin anyi watsi dasu basu da ruwan sha ba hanyoyi ba magudanu ruwa ga
yawan jama'a a unguwanin su. A gida daya za a tarar da mutane kamar 30 a gundumar Guele Tapee na Dakar da Karachi, rabin mazauna Ghosia kuma suna cunkushe ne. A canja tsarin kula da shara na birane a Afrika ta yamma. A

shigar da kananan kamfanon da kungiyoyin matasa dana makwabta wajen tara shara. A Kyale kananan hukumomi suji da nauyin sauran matsalolin dake akwai na harkokin birane. A Dakar da Bamako kimanin kananan kamfanoni metan
ne suka shiga cikin shirin kula da shara, kana suka hada kansu domin kare bukatun su. A biranen Bamako da Cebu
kungiyoyin mata ne suka ja damara kan aikin tsabtace muhalli dakuma kiwon lafiya.

'Fahimtar aikin tare da hanyar da za abi wajen aiwatarwa yakan kafafawa masu shiga giwa'inji rahoton. Yadda aka wayarwa da jamaá kai kan wannan aiki a gundumar Ghosia ya sanya mutane suka himmatu wajen shiga aikin tsabtace
muhallin. Yekuwar tayi bayani kan yadda jama'a zasu shiga tare da karfafa musu gwiwa kan yadda zasuyi mahawara
gamw da shirin. Haka ma a Ougaodougou irin wannan hanyar akayi amfani da ita. Haka ma tsarin demokuradiya yakan taimaka wajen tafiyar da aikin kula da sarrafa shara, a biranen. Rahoton na WASTE ya nuna cewa: 'shigan aikin

tare da baiwa jamaá dama ya dogara ne kan yadda ake mahawara tare da baiyana ra'ayoyi tsakanin hama'ar. Haka kuma yace rashin cigaba da tsarin gwamnati da rashin tsarin demokuradiya wajen tafiyar da aikin dakuma canje-canje
na sanya rashin amincewa juna ga al'umonin domin aikin. 8
8 Page 9 10
9
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

Talauci da rashin samun gidajen da ya kamata sune muhimmai kan ka'idojin shigar jama'a cikin aikin. Babu wata kwakkwarar hujja na hadewar su domin yakar abinda ke damun su illabarazanar da suke fuskanta na tada su, da

bukatar samun fili nasu dakuma ace su mazauna birini ne. Babban darasin da aka koya dai shine mutane na shiga cikin
shirin sarrafa shara na birane ne in har haken ya zo daidai da bukatar su. Mutane da dama sun nuna sh'awar su ne bayan da suka ga cewar za a dauke su aiki a matsayin masu yin shawa ko direbobin motocin kwashe shara. Sha'wawar

su na fita kan aikin da zarar sun ga dukkan gurabun aikin sun cike kamar yadda ya baiyana a Ougadougou da Patan da Senegal dakuma Mali. Aikin sarrafa shara ba zaiyi nasara ba in har masu gidaje ba zasu biya kudin sharar da ake
Kwashe musu ba. Haka kuma za a fuskanci matsaloli in har masana 'antu kungiyoyi da sauran mutane suka kasa yin: -*
Kula da aiki sarrafa sharar da suka kafa: * Ki sanya mutanen dake zaune a yankin tunda farko:

* baiwa kowa irin rawar da zai taka cikin aikin. * sasanta rikici tsakanin direbobin motar shara da sauran ma'aikata:
* tabbatar da tuntubar juna tsakanin al'umomin: ko
* tabbatar da ganin direbobin motocin shara da masu shara aii bayiy musu yawa ba ko kuwa kudin da ake biyan su baiyi kadan ba.

Ana bukatar hanyoyi masu karfi domin tabbatar da dorewar shirin sarrafa shara a kasashe masu tasowa. Kwakkwarar hanya itace wadda ta hada shirin sarrafa shara da zamantakewar jama'a wuri guda, tare da aiki na gari, tare da fadakar
da jama'a kan muhimmancin shirin. Baya ga wannan akwai kuma: -*
hade kungiyoyin hukumomi da masu zaman kansu dake cikin shirin domin baiwa kowa irin aikin da zaiyi. * bullo da sabbin fasahohi domin samar da aikin yi dakuma kudin shiga.
* sanya mutanen da hukumomi sukayi watsi dasu, cikin shirin, da wadanda basa da abubuwan more rayuwa. UWEP.

Sabon Yankin Al'ada A Afrika Ta Kudu 2mins 37sec. Gandun dajin St. Lucia dake yankin Kwa-Zulu-Natal a Afrika ta kudu yanzu ya zama yankin al'ada na duniya, inji
hukumar kula da muhalli (NCS). Shine yankin farko a Afrika ta kudu da ya samu wannan matsayi na duniya. Domin
haka yanzu gandun dajin zai sami cikakkiyar kariya na zai kara janyo hankalin masu yawon bude ido ganin irin matsayin sa yanzu a duniya. 'Munyi matukar farin ciki da murna da wannan sanarwa'inji Dr. Hans Grobler mukadashin shugaan

hukumar. 'Alwao 'yan Afrika ta kudu da dama da sauran jama'ar duniya dake matukar sha'ar gandun dajin St. Lucia, wadanda kuma suka goya mana baya a kokarin mu na kare wannan gandun dajin gargajiyar'in ji shi.

Ministan gona da muhalli na Kwa-Zulu Natal Mr. Narend Singh ya baiyana jindadin sa da wannan sanarwa. Yace zai samar da kyakkyawar dama da masu yawon bude ido zuwa lardin kana yankin Kwa-Zulu Natal zai sami amfani sosai
ta hanyar samar da aikin yi ta hanyar raya aiyukan yawon bude ido. Kalubalen ne nan gaba shine inganta kayan da ake dasu a gandun dajin ta yadda masu yawon bude ido zasu mori abinda ke gandun dajin na St. Lucia, saidai kuma za a
inganta su ne ta yadda ba zasu lalata ainihin abubuwan dake akwai ba ya kara da cewa. Gandun dajin mai fadin
kadada 250,000 ya hada da yankuna daban-daban kamar su bakin babeji, ba a taba su ba. Haka kuma akwai yankin dake da ruwan gishiri da ruwa mai kyau da yankin dake da tabo da sanran su. Yankin wurin zaman dorina ne dake

kudancin kasar da kadoji 1,000 da tsuntsaye iri-iri Daga cikin abubuwan da akeyi a gandun dajin sun hada da kamun kifi, da shawagin jiragen Kwalw-Kwale da ninkaya da sansanoni. Wadan nan duk suna bada damar daukar hotuna
masu kayatarwa. Ramsar 9
9 Page 10 11
10
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Ta Hade Madagascar Da Vietnam Kan Aikin Gona 1min 51sec.

Bisa kudurin hadin kan kudancin duniya, da marigayi tsohon shugaban Tanzania Julius Nyerere ya jagoranta, gwamnatocin
Madagascar da Vietnam sun amince domin yin aiki tare wajen raya aikin gona domin tattalin arzikin Madagascar. Kwanan nan nekasashen biyu suka sanya hannu kan yarjejeniya tare da hukumar gona da abinci ta duniya (FAO),

domin tura kwararun Vietnam kan aikin gona zuwa sashin gona na Medagascar. Aikin zai kauda duk wani tarnaki, domin tabbatar da cigaban aikin samar da abinci a kasar. Gwamatocin kasashen biyu tare da hukumar ta FAO sun
zasu taimaka.
Cikin sanarwar da hukumar ta FAO tabayar tayi bayanin cewar hadin irin wannan na samar da damar karfafa hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa da FOA. Zaiyi aiki ne bisa tsarin aiyukan FAO na musamman domin samar da abinci
(SPFS) na taimakawa kasashe domin cin moriyar basirar juna musamman kasashen da suka cigaba. Dr. Jacques Diof ne ya bullo da wannan shirin a shekarar 1977. Shirin musamman domin samar da abinci na aiki a kasashe 51, kasashe
30 daga Afrika goma sha-2 Asia kasashe 6 gabas ta kusa, dakuma kasashe 2 a Turai daya a Oceania wadanda ke wakiltan sama da kashi 60 cikin 100 na kasashe mafi talauci a duniya.
FOO/ ORG.
Dan Japan Da Aka Daure a Thailand Ya Sanya Cinikin Bude Littafi a Ghana 1min 43sec.
Ma'aikatar gandun daji na Ghana ta dukufa kan yekuwardaukaka cinikin malam budelittafi dake nan dayawa a yankunan dake da tsaunuka. Kimanin bude littafi iri-iri har 20 ne ake dasu a Ghana wadanda kuma suna da yawan da za a iya

sayarwa. Sudai irin wadan nan bude littafin sunan maya da kanana dakuma masu launi daban-daban dakuma irin na Afrika ta yamma, wanda akan iya sayarwa har kudi dalar 100. Sauran irin bude littafin kuwa zasu kai kimanin dalar 2
kowane daya. Wannan kuwa kudi ne mai yawa idan aka kwatanta da kudin Ghana Cedi.
Cinikin bude littafi a duniya yakai dala miliyan 100. Ma'aikatar dangun dajin Ghana tayi imanin cewar zata sami dalar 150,000 kowace shekara tacinikin bude littafi. Wannan sililin ya biyo bayan sanrwar da wata tasher rediyo mai zaman
kanta ta ruwaito ne cewar an tsare wani dan kasar Japan a Thailand, wanda ke cinikin bude-litafi wanda jami'an kula da dabbobi na Thailand ne suka kama. Mr. Nick Ankudey jami'in kula da dabobin dawa na Ghana ya ilmantar da
jama'ar kasar kan irin muhimmacin dake akwai na kare kwari da dabobi. Najeriya na daya daga cikin kasashen Afrika dake da arzikin bude-littafi wandaa take dasu iri-iri. Tana da bude littafi kimanin kala-kala har 1000, kuma ana samun
su ne akasari a saahin kudu maso gabashin kasar. Edward Ameyibor

Sashen Yara
Babu Kifi Ga Dorina 2mins 1sec. (Wannan Labari Ne Kan Yadda Dorina Ya Tarwatsa Yankin Sa Labarin Nanan Tsakanin Kabilun Afrika Ko Da Yake Ya Fara
Ne Da Kabilar Bushman)
Yayinda aka baiwa dabbobi filayen su a duniya sai wasu dorina biyu suka nemi da a basu dama su zauna cikin ruwa mai sanyi wanda suke matukar so. Da dama sunyi shakku wajen barin su su zauna cikin ruwa, bakin kato hakuran

su dogaye da kaifi, kuma gasu katti, domin sauran dabbobin suna ganin zasu cinye dukkan kifayen dake ruwa. Domin kuwa baya ga su dorinan an baiwa wasu dabbobin ma damar zamar zama a ruwa kamar kada. Domin
sunce bai dace ba abar dabobi masu kama da juna cikin ruwa infi dabbobin domin yunwa zata kashe su. Domin
haka sai aka ce dorinan ba zasu zauna a ruwa ba saidai a sarari cikin ciyayi. Bisa wannan labarin sai dorinan suka fara kuka inda suke ta ihu da karfi, sukay ta roko har saida aka amince musu kan bukatar su. Amma saida aka ce

su dorinan su dauki alkawari in har an kyale su zama a cikin ruwa to ba zasu taba kifi ba. Saidai sufito su ci ciyayi. Dorinan sukayi alkawari suka fada ruwa cikin farin ciki. 10
10 Page 11 12
11
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

Shine har rana wata yau dorina bata yiwa kifi komai, kuma take tone bakin kogi a duk inda take domin nunawa sauran dabobi cewar bata ci kifi ba. Kuma zaka rika jinsu suna dariya harda shewa wai don an kyale su su zauna

cikin ruwa. When Hippo Was Hairy

Yadda Macoko Ke Hawa Zita Tace Bashi Da Kafa 29sec. Macijin dake hawa itace nada wani abu mai karfi a karkashin cikin sa. Wannan abu kuwa ana kiran sa da turanci
'VENTRAL'. Shi wannan magandisun shike sanya macihin ya rike jikin itace mai kaushi yayi ta ja kan itace.
Dukkan macizai suna da karfin hakarkari, wanda ke basu damar jan jiki. Yayinda karfin hakarkarin ke jan su shi kuwa maganadisun na rike jikin itace, wanda ke taimakawa macizai tafiya.

Chongololo
Karin Magana 36sec.
Duniyar da muke ciki abune kamar jirgi kato. Amma abubuwan dake ciki sun sha bambam. Abin nufi girman jirgin ba Zai karu ba haka kuma abinda ke cikin jirgin na da iyaka. In har dan adam bai kula da karuwar yawan jama'a

ba tare da lalata albarkatun dake akwai shi wannan jirgin da dukkan mutanen dake cikin sa zasu hakaka baki daya cikin iska., wanda ke nufi karshen duniya ke nan. '
Ryolichi Sasakawa, Japanese Philantroph\ ist

Kurege Da 'Ya 'Yan Zakanya 7mins 56sec. Zakanya mai 'ya'ya biyar, wadanda suka fara neman nama amma sunyi kankanta da fita domin binta zuwa farauta,
domin haka sai ta yanke shawarar sama musu mai reno. Wata rana tana yawo tana kallon yadda sauran dabbobi ke kiwo. Sai tazo ta shige kunkuru batare da ce masa uffan ba. Shi kuwa kunkure sai saibi yakeyi ta yadda zai
kule duk mai hakuri. Sai ta gamu da kura, kura ta durkusa ta gaishe ta, amma zakanyar bata kula da ita ba. Domin kura bazata iya kulawa da 'ya ýanta ba domin haka sai ta kyale ta. Cikin zakuwa, zakanyar tayi ta zura ido a daji ko
zata ga wanda ya dace da renon ya 'yan ta. Can sai taga wani abu ya gilma gaban ta, sai tayi sauri ta duba tace aha kurege. Tsaya ko kana sauri ne inji zakanya, domin ; yan kwanankin nan ko gaishe ni bakayi. Barka da hantsi
manyan dawa'inji kure ge cikin ladabi. Yaya kike tare da 'ya'yan ki su biyar? Akan su ne ma nake son yi maka
magane inji zakanya, wani nake son girmamawa kan aikin renon su yayinda na tafi farauta. Wace irin girmamawa ne wannan ya samu inji kurege:

I kai ne' inji zakanya. Domin nasanka da dabara domin haka so ka nuua dabarar ka ta hanyar kula da 'ya' ya na. Zan rika kawo maka nama a duk rana, sai karika raba musu daidai-wa-daida. Zan rika zuwa lokaci-lokaci ina duba koshin
lafiyar su. Domin haka aikin ka ya fara daga yanzu sai ka fara kulawa dasu. Zakanya ta juya ta shiga daji domin yin farauta. Kurege ya fada matsala, ya karci kasa cikin fushi yayi gunaguni tga ciki. Yace to yan ko kumallo ba zan samu ba kenan
domin fara wannan aiki. Domin sai ya sami wani rami kebabe ya sanya 'ya' yan zakayyar ciki shi kuwa yayi ta yawo yana tunani kan yadda zai bullowa wannan al' amari. Can sai ya tsaida shawara yace wacece zakanya da zanyi mata aikin
banza? Kowace rana in zakanya ta kawo masa nama domin baiwa 'ya' yan ta sai kurege ya dauki dan kadan ya basu
sauran kuma ya cinye. In ta tambaye shi yaya suke suke sai yace suna cikin koshin lafiya. Wata rana ta zakanya ta zo sai tace son taga 'ya' yan ta, sai kurege ya mika hannu a rami ya kamo da daya ta kunne ya nuna mata, ya maida ya sake

dauko daya ya nuna mata har sau biyar. A halin yanzu dai kurege sai amfani yakayi da naman da zakanya ke kawowa, su kuwa 'ya' yan ta suka fara mutuwa saboda rashin abinci. Daga karshe dai 'ya' ya hudu suka mutu saura daya. Zakanya
ta zo tace tana so taga 'ya' yan ta, sai kurege ya mika hannu a rami ya fida sauran dayan ya nuna mata, ya mai dashi ciki
ya sake sa hannu ya dauko shi ya nuna mata ya maide shi ya sake sa hannu ya dako shi. 11
11 Page 12 13
12
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

Haka dai har zakanya ta dauka cewar 'ya' yanta biyar suna nan. Daga karshe shime sauran dayan ya mutu. Sanin abinda zai biyo baya, in har zakanya ta gane 'ya' yanta sun mutu, sai kurege yaje yayi ta birgima cikin kaya da ciyayi yayi futu-futu

ya komo bakin ramin ya kwanta yana nishi kamar rai-kwakwai-mutu-kwakwai. zakanya da tazo ta same shi cikin
wannan yanayi tace ne yasame ka? Ina 'ya' ya na. Yace oh ranki dade, yayinda nake kula da su sai wasu kattin birrai suka zo suka kawo mana farmaki suka cinye 'ya' yanki duka nima dakyar na tsira dai ganin yadda nake. Zakanyar har

ta kusa yarda da abinda kurege yace da ita. Amma sai tanemi hujja da zata tabbater da labarin sa. Sai kurege yace mugina rami mu sa ciyaye a bakin inda zaki buya sai mu zuba gyada abin ramin zakiji irin abinda suke fadi na game da cinye 'ya'
yan ki da sukayi. In har kinji abinda suke fada sai ki dirar musu, kiyi ta kashe su kina yanke jelar su. Duk wanda kika
kasha sai ki yanke jelar sa. Zakanya ta yarda suka gina karamin rami suka sanya ciyayi tare da gyada, can sai ga goggon birai sun zo suka ga gyada sai suka zauna suka fara ci. sai kurege ya dauki tsinkiye ya kada ya fara cewar 'ya' yan zakanya

da mukaci ba abinda y same mu. Birrai da kwaikwayon abinda suka ji sai madugun sa ya kwaikwayi abinda yaji kurege na fadi, 'ya' yan zakanya da mukaci ba abinda ya same mu. Sai sauran birran suma suka fara kwaikwayon madugun su
na cewar 'ya' yan zakanya da muka ci ba abinda ya same mu. Zakanya bata ji wanda kurege ya fara fada ba saidai na
birrai, sai kuwa tayi kukan kura ta auka musu tana kashewa tana yanke jelar su. Shi kuwa kurege yana binta a baya sani ba yana dauker jelar yana tarawa. Saida zakanyar ta kasha wadanda sukayi sa' a suka tsira ta koma gefe daya tana haki

bisa irin aikin da tayi. Sai kurege ya same ta yace gudanawa kika kashe, ni kin ga birran da na kashe domin fansa ga 'ya' yanki da suka cinye. Ita kuwa zakanya ba jela a hannun ta ko daya domin dama tana yanke jelar ne ta yar.
Shangani Folktales

Kenya Ta A Yiniyar Saida Tasharf Jiragen Ruwan Ta Daya Tilo 1min. 2secs Gwamnatin kasar Kenya tayi niyar saida jarin tashar jiragen ruwan ta daya tilo kilindimi wanda akafi sani da tashar jirage
ta Mombasa, saboda yawan cin hanci a hukumar tashar jiragen. Akwai dai shiri tuntuni da gwamnati tayi na saida jarin tashar a matsayi hanya kadai mafita domin kauda kauda cin hanci da ya zama ruwan dare. Cikin sanarwar da hukumar
ta bayar anyi tir da rashin iya tafiyar da aiki ga hukumar, inda suke. kyale kaya na shigewa batare da biyan haraji ba, da bacewar kaya tare da satar kaya kafin yin gwanjon su. Amma manyan jami' an hukumar sun shure shirin saida jarin tashar,
Yan siyasar dake sashin kudancin kasar da ma' aikatan hukumar da sauran kananan hukumomiin yanki sun ki amince da maganar saida jarin, duk da cewar ashirye suke domin karbar takardar sallama daga aiki bayan saida jarin jukumar.
Newslink Afrika

Yara Marayuna Karuwa A Afrika 1min 4secs Yawan yaran dake zama marayu a Afrika a sanadiyar cutar kanjamau sai karuwa yakeyi, kafin karshe wannan shekara
za a sami yara miliyan 13 a duniya da zasu rasa iyayan su a sanadiyar cutar kamar yadda rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna ranar yaki da cutar cikin watan Dismba. Rahoton da akayiwa taken' YARA MARAYU KAN KANJAMAU'
an hada ne daga sashin gabashi zuwa kudancin Afrika, wanda UNICEF ta tara tare da hukumomin majalisar dinkin duniya dake yaki cutar ta AIDS. kafin karshen wannan shekara duniya zata sami sama da yara miliyan 11 da zasu rasa iyaye
ta hanyar cutar, kashi 95 cikin dari zasu fito ne yankin saharar Afrika. Yaran marayun shige minsheri inji hukumar UNICEF,. Darektan shawo kan cutar Carol Bellamy yace kafin bullar yara kalilan ne ke zama marayu a sasashe masu
tasowa. Amma yanzu sama da yaro daya daga cikin yara goma maraya ne. UN News

Majalisar Dinkin Duniya Na Karfafa Hakkin Na Kasasu 42secs. Kasan cewar akwai kimanin nakasasu miliyan 500 a duniya yau din nan?, wanda hakan yasanya sune na biyar mafi yawa
a duniya. Domin haka majalisar dinkin duniya yasanya sune na biyar mafi yawa a duniya. Domin haka majalisar dinkin
duniya tayi kira da a tattauna kan manufofi domin tabbatar da daidaito ga nakasasu kan aiyukan si siyasa da zamantakewa a duniya. 

UN News 12
12 Page 13 14
13
CHANGE Radio
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa)

Abinda Ya Sa Damisa Ke Ajiye Ta Kan Itace 1min. 55secs
Mutanen Afrika na shaidawa 'ya' yan su labaran tstsuniya da can akwai wasu abokai uku, watau damisa, da karen dawa dakuma kura. Ko ina zasu tare suke zuwa. Duk lokacin da damisa ta kashe dabba koda yaci sai ya regewa sauran abokan

nan nasa watau kura da karen dawa don suma su ci. Wata rana sai damisa tayi rashin lafiya sai tace da karen dawa don Allah yau sai kaje kayi mana farauta kaga ni banda lafiya, sai karen dawa saboda lalaci yace shi ba zai iya ba saidai ya
gayawa kura. Domin haka sai damisa ta gayawa kura kan taje tayi musu farau yan, domin batada lafiya. Ita ma kura sai
ta ki bisa hujjar cewa kafar ta na ciwo. Daga nan sai damisa tayi kuki cikin fushi, tace' koda yake ku kawaye an ne amma kawayen banza ne malalata. Daga yanzu ba zan sake baku naman da na farauto ba. Daga wannan rana zan tabbatar da

hakan. Zan dauki ragowar naman da naci bayan na koshi na dora itace. Domin haka babu daya daga cikin ku da zai samu. Damisa sai ta tabbatar da ikirarin ta, tundaga wannan lokaci har zuwa yanzu in damisa ta rage naman kashe sai t dora
kan reshen itace can kololuwa ta yadda karen dawa da kura ba zasu iya kaiwa ba. Daga wannan lokaci karen dawa da
kura basa samun nama sai abinda sauran namun dawa suka ci suka rage. Daga nan kuma sukayi bakin cikin rabuwa da kawar su damisa.

When Hippo Was Hairy
Hujjojimasu Amfani

Bala'i ya Aukawa Watahiha A Kasar India 44secs. Kusan mutane 8,000 ne suka rasa rayukan su kwanan nan a sakamakon wata mahaukaciyar guguwa da ta ratsa same
da kauyuka 18,000 a gundumomin dake bakin taku a kasr India. kamar yadda hukumar UNICEF tayi kiyasi gidaje
miliyan ukn ne guguwar ta shafa kuma same da mutgane miliyan 10 suka raga gidajen su. Haka kuma dukkan gonakin dake gabar takun ruwa ya wanke su. Hukumar UNICEF da sauran kungiyoyin agaji na duniya sun aika da kayan agaji

ga wdanga suka tagayyara. Hukumar ta shirya kasancewa a jihar ta Orissa inda bala' in ya har shekara ta 2,002, wanda a wannan lokaci ake saran sake gyara da tsugunar da wadanda suka tagayyara.
UNICEF.

Tabbasadaga Hukumar Abinci Da Aikin Gona 48sec. Rahotani biyu kwanan nan da hukumar abinci da aikin gona ta bayar, ya nuna cewa karanci abinci a duniya na aukuwa
ne saboda dalilai na mutane bawai daga kudura ba. Akaro farko da dan adam ya haddass bala 'o' i kamar yakin basasa da matsalolin tattalin arziki, wadanda sukayi kan samar da abinci fiye da masifofin kudura. Rahoton hukumar ya kara
da cewa. Kimanin mutane miliyan 10 a yankin san sahara na Afrika ke bukatar taimakon kayan abinci yanzu haka. A somalia kadai fiye da mutane 400,000 ke fuskantar yunwa. Dr. Jacques Diouf na Senegal a sake sake zabe a karo na
biyu domin wa' adi shekaru shida a matssyin babban darektan hukumar abinci da aikin gona ta duniya, wanda zai fara daga watan Janairun 2000.
FAO ORG.

Abinsha'awada Ya Kama Ta Ka Sani, Kaji Ka Gani 2mins 16sec. * Wata sabuwar hanyar wasani da ta bullo a duniya, wanda ke tsakanin masu rajin kare dabbobi da halittu dakuma
mafarauta. Kana iya biya a kaurar da dabbobi daga wannan wuri zuwa wancan mai makon a kashe su kamar yadda maharba keyi. Kuma ana iya kulawa da su dabbobin. Saidai fa wannan yana da hatsari domin dabbobin da masu
farautar su duk suna iya shiga cikin hatsari.
* GANDUN. DAJIN BWINDI: Gandun dajin da yayi suna kan irin goggon birai dake ciki gandun dajin na Uganda wanda yana daya daga cikin gandun dazuka mafi yalwa a Afrika saboda yawan bishiyoyi iri-iri har 200, da tsuntsaye
iri-iri 350 dakuma sauran dabobi kala-kala har 100. Mafiyawa daga cikin hallitun wannan gandun daji, sune bude
littafi suna suke iri-iri har 350 ga kuma tsuntsaye da sauran birrai. Birran dajin Bindi suna da wani abu na musamman watakila saboda yadda Allah Ya halitta su ne, da siffa mai tsorataswa dakuma shirin fada yayinda akayi gaba-da-gaba

dasu. 13
13 Page 14
14
Vol II No. 14
Janairu 2000 (Hausa) CHANGE Radio

* JEMAGU DA AIKIN SU: Jemagu wanda suke da muni a ido dakuma irin tarihin su da yadda ake lakanta su da camfe-camfe, jama' a basu fahimci ainihin abubuwan da sukeyi ba.

Nazarin da akayi kan jemagu game da cin kwari da 'ya' yan itace ya nuna cewa:
-In badon jemagu ba auratayyar furani da watsuwar tsirrai a dazuzuka zai ragu ainm. -In badon jemagu ba sake sabanta manyan dazuzuka ta hanyar tsirrai ba zaiyi wu ba.

-In badon cin 'ya' yan itace da jemagu keyi kan itacen kuka ba, aurataiyar furani daga wannan itace zuwa wancan, da baiyiwu ba duk da girman itacen kuka.
-Ana iya ganin jemagu 6,000 cikin minti 10 da maraice, wadanda zasu iya cinyr kwari masu nauyin kilo 23-wannan
kuwa ba karamin aiki bane wajen shawo kan kwari masu ta' adi kuma ba tare da yayiwa dan adam lahani ba, ko lalata muhalli.

Afrika Env

CHANGE Radio (ISSNIII9-6211) mujalla ce dake fitowa duk wata, wanda ake bugawa cikin harsunan Turanci da Hausa da Igbo da Faransanci dakuma Yarbanci daga hukumar canji ta fuskar sadarwa (Da WWF) dake lamba % kan
titin Adeyemo Alakija Victoria Island, P. O. Box 56283 Falomo Ikoyi Lagos Nejeriya. Tarho (234)-1-262-0602. Ko kuwa a aiko da duk sakonni ga Edita Change Radio. Tsuntsun dake shafi farko an dauko ne daga jihar Borno. Babbar
Edita: Sandra Mbanefo Obiago, Edita/ Marubuci Obasi Ogbonnaya. 14

Page Navigation Panel

1 2 3 4 5 6 7 8 9
10 11 12 13 14

 

© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw