Document Body Page Navigation Panel
Kungiyoyi masu zaman kansu da dama zasu cigaba da aiyukan su
Godiya ga Gidauniyar Ford.
Karin Maganar Raya Kasa 30secs 12 Manyan Afrika sun danno.
HARKOKIN MULKI
Ra'ayoyin Jama'a 'Yan Najeriya Basu Amince Da Shari'a Ba. 3min 18secs 6
Ra'ayin jama'a na farko a Najeriya kan shari'a da dama basu amince ba.
KIWON LAFIYA
Duniyar Da Ba Cutar Shan-inna. 4mins 31secs 8 Wata mace a Indiya ta
baiyana irin abinda ta sani game da allurar
rigakafin cutar shan-inna.
Kungiyar Kasa Da Kasa Zata Magance Zazzabin Cizon Sauro A Yankin Neja
Delta 1min. 17secs 5
Kungiyar agaji ta Sans Frontiere zata magance cutar dake kisa a Nija Delta.
BINCIKE
Majalisar Dinkin Duniy Ta Bukaci Kasashe Masu Tasowa Suyi Nazari Kan Abinci
Mai Rike Ciki 1min. 51secs 3
Kungi Abinci ta duniya (FAO) na karfafawa kasashen Afrika gwiwa da su
shiga sahun duniya kan abinci.
MATA
Yarinyar Da Mafarkin Ta Ya Zama Gaskiya. 3mins. 45secs 45 Sara ta
cimma burin ta duk da rasa kafar ta guda da tayi a hatsarin mota.
Unesco Ta Bukaci Mata Su Kafa Bajimta Banar 8 Ga Watan Maris 1min 37secs
4
Shirin da akayi na duniya kan bajimtar mata.
Matar Kasar Rwanda Na Rabon Maza Tsakanin Su Domin Samun Iyali. 3 mins
20secs 7
Kisan kare dangi ya sanya mata a Rwanda raba maza tsakanin su.
Yanayin Muhalli AIKIN GONA
Birrai Abokanen Manoma. 1min 16secs 4 A kyauta manyan Birrai zasu
sanya manoman koko yin arziki.
Taran Gajimare Ya Kano Sauki Ga Kauyen Dake Fama Da Fari. 2min . 56secs
6 Wani kauye ya samo dabara samun ruwa daga gajimare domin biyan
bukatar ruwa.
Kajin Swaziland Na Fuskantar Karewa. 1min. 19secs 4 Kaji 'yan
kasa a Swaziland zasu kare a duniya saboda rashin tasarin
kula da dabbobi na gari.
HAMADA
Hanyoyin Al'ada Na Taimakawa Domin Kare Hamada. 4 mins 22secs 9 Hikima
irin ta al'ada zata taimaka wajen kare hamada a Afrika. 1
1 Page 2 3
2
Vol. II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio
Maris 2000
BALA'I
Bankin Duniya Na Taimakawa Kasashe Matalauta Domin Kare Bala'o'i. 58. secs
3
Hadin gwiwar kasa da kasa na taimakawa wajen rage asarar rayuka
da dukiya kan bala'o'i.
GANDUN DAZUZZUKA
Da Mun Sare Iyace Yanzu Nuna Kulawa Gandun Dazuka. 3mins. 58secs 10 Al'umar
da ada ta dogara kan saran itatuwa, yazu ita ke kare gandum dani.
Hukumar 'Yan Gudun Hijira Ta Duniya Ta Himmatu Kan Kare Muhalli. 1min.
16 secs 9
An fara aikin tsabtace yankunan al'umar da ta karbi 'yan gudun hijira
a
sashin Arewacin Uganda.
Sabuwar Mnufar Gandun Dazuka Dake Tafe. 3mins. 7 sec 8 Sabuwar
manufa kan dazuka na majalisar dinkin duniya ta kammala.
Sashin Yara Labarin Al'umar Afrika Ta Tsakiya Kan Alfacari.
4mins. 49secs 10
Yadda Alfadari ya sami zanen sa baki-da-fari.
Yadda Pokapin Ke Kare 'Ya'yanta 5 mins 43secs 12 Yadda pokapin
ke kokarin fidda "ya'yan ta daga hatsari.
Hawainiya Na Kashe Kanta Ne Domin Haihuwa? 2 mins 11secs 11 Mutane
na kashe Hawainiya ne saboda bahaguwar fahimtar da sukayi mata.
Meyasa Kudaje Da Kekkesai Ke Rayuwa Gashi Basa Tsinanawa Mutane Komai?
58secs 12
Kudaje da kekkesai suna da amfani ga jama'a fiye da yadda ake zato.
2
2 Page 3 4
3
Vol II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio Maris 2000
Lamarai
Kungiyoyi Casa'in Na Afrika Zasu Raba Dla Miliyan 14 1min 49secs
Kusan kungiyoyi masu zaman kasu casa'in na Afrika (NGO) zasu sami taimakon
dala miliyan 14 daga
Gidauniyar Ford a watani shida na farkon shekarar bara. Dukkan kudin taimakon
suna daga ciking shirin Gidauniyar na kula da bangarori uku, wandanda suka hada
da aiyukan raya kasa, dana zaman lafiya da
adalci, dakuma harkokin ilmi dana addini.
An samar da taimakon ne tsakanin daya ga watan Fabrairu zuwa 31 ga watan Mayun
1999, wadanda suka kama daga dalar dubu dari uku zuwa dala miliyan daya kana
aka badasu cikin watani uku zuwa shekara uku.
Cibiyoyin da suka ci moriyar shirin sun fito ne daga kasashe 14 daga dukkan
nahiyoyi hudu na Afrika. Kasashen kuwa sun hada da Masar, da Ghana da Kenya
da Mozambique, da Namibia, da Najeriya, da Senegal
da Saliyo, da Afrika ta Kudu, da Tanzaniya, da Tunisiya, da Uganda da Zambia
dakuma Zimbabwe.
Daga cikin wadanda suka ci moriyar sun hada da cibiyoyin bincike, da Jami'o'i
da aiyukan kare muhalli, da kula da shara dakuma shirukan taimakawa juna, da
harkokin magunguna da wasan kwaikwayo, da kungiyoyin
dake yaki da cutar kanjamau dakiwon lafiya da kauda bambanci tsakanin maza da
mata da kare hakkin dan adam da tsarin demokuradiya da kare yara da sauran aiyukan
kare da sauran aiyukan kare tursasawa jama'a.
Haka kuma akwai kare 'yan tsiraru, da tattalin arziki dana al'adu da sake
ginakasa tare da ilmi kan harkokin na'urar internet.
An zabi wuraren da za a taimakwan ne danufin karfafa Gideuniyar ta Ford kan
karfafawa jama'a gwiwa wajen dogaro da kai na cibiyoyin duniya tare da karfafashirin
rage talauci da yin adalci da hadin kan duniya
tare da cimma manufa. Ford Foundation Report
Bankin Duniya Na Tanimakawa Kasashe Matalaita Dp Om Lare Bala'i 58secs
Bankin duniya da hadin kan Gwamnatoci sun kaddamar da shirin taimakawa kasashe
masu tasowa danufin kare bala'o' in dake faruwa daga Allah. Membobin kungiyar
da aka kira hadin gwiwar duniya sun hada da
cibiyoyi da jami'o'i da sauran kungiyoyi masu zaman kansu.
Kamar yadda Bankin duniya ya nuna bala'o'i na kashe mutane sama da dubu hamsin
tare da lalata dukiya ta sama da dala biliyan 65 a shekarar 1998 kadai. Kusan
dukkan mace-macen a kasashe masu tasowa ne inda
mutane mafi talauci suke zaune.
Shidai wannan hadin gwiwa yayi nufin samawa kasashe masu tasowa ne kayan da
zasu iya kare kansu a duk lokacin da irin wannan bala'in ya auku, irin su girgizar
kasa da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa, domin
rage yawan asarar rayuka da ta dukiya da sukeyi. Addis Tribune
Majalisar Dinkin Duniya Ta Roki Kasashe Masu Tasowa Suyi 1min 51secs Nazari
Kan Abinci.
Hukumar abinci ta duniya (FAO) ta bukaci cibiyoyin bincike a kasashe masu
tasowa da suyi nazarin hanyoyi daban-daban kan kayan abinci dangin hatsi domin
su sami sukunin takara da sauran kasashen duniya. 'Hanyar
samun karin labarai kan abinci dangin hatsi zai taimakawa jama'a a kasashe masu
tasowa su saida kayan su tare da takara a kasuwanin duniya, ' Inji Morton Satin
baban jami'in hukumar abinci ta duniya.
Ana samun staci cikin abinci irin su alkama, da dawa da shimakafa da dankali.
Daga cikin kayan da ake amfani dasu da sitaci sun hada a biredi, da sinak da
miyar taushe, da kaji, da kayan kamshi, da fauda, da madara. Haka
kuma ana yin kaya irin su takardu da masana'atun yin tufafi da kayan agwaja
irin na mata da masana'antun magunguna da na sarrafa karafa. 3
3 Page 4 5
4
Vol. II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio
Maris 2000
A yanzu haka akasarin binciken da ake yi na sitaci anayi ne a kasashen da
suka cigaba, hakan tilas a canja muddin ana bukatar gina ingantaciyar kasuwar
sitaci ta duniya daga kasashe masu tasowa inji Satin.
Hukumar FAO ta fara nazarin aiyukan kayan sitaci ne shekara daya da ta shige
yanzu tana aiki tare da cibiyoyin bincike na Italiya da Thailand kan batun.
Man gaba hukumar zata marawa aiyukan nazahiri, wadanda
suka shafi sitacin.
Satin yace sitaci kamar sauran abubuwan da ake samu bai samu cin moriya ba daga
binciken da ake bukata domin tabbatar da harkokin kasuwanci yadda ya kamata
a duniya kabi daya.
FAO
Birrai Abokan Manoma Ne. 1min 16secs. Biri abune dake da ban haushi
a duk lokacin da ya shiga gonar ayabar ka, amma binciken da aka yi kwanan
nan, ya nuna suna iya kara samun manoman Coaco ta hanyar cin wadanda basu nuna
ba.
Binciken wanda ya ta'allake kan jajayen birran ne dake tsibirin Zamzibar a kasar
Tanzaniya, Kirsten siex da Thomas Stuhsaker na Jami'ar Duke dakedurham a Arewacin
Carolina ne suka gudanar,. Sun gano birran
suna zaben Coacon ne kamar yadda mazauna tsibirin keyi suma.
"Tunda yake sunfi son wadanda basu nuna ba, lallai suna aiki ne kamar ma'aikatan
da ba abiyan su, ta hanyar kara yawan coaco akan itacen da suke cin kamar yadda
siex da Struhsaker suka fadi.
Sun gano daga itace Coaco shida wadanda basu nuna ba da birran suka ci bayan
wata guda sai guda goma sha-3 suka tsiro. Haka kuma itacen da suka cire goma
wandada basu nuna ba sai ga 17 sun fito, wannan kuwa
wata sanara ce inji su.
Manoman kamata yayi suyiwa Birran godiya bawai kashe su inji jami'an. The
Economist
Kajin Swazi Na Fuskantar Karewa 1min 19secs Wasu nau'in kajin kasar
Saziland biyu na daf da karewa a duniya. Kajin sune da wadanda basu da
gashi a wuya da masu kananan kafafu, wadanda yanzu basu da yawa. Jami'an Gwamnati
sunce wata kila ancinye su ta wajen yin miya.
Ministan gona da jam'iyun gama kai na kasar Roy fanourakis ya dora laifin
karewa kajin kan rashin bullo da dabarun zamani na kiwon kaji, da rashin kula
da dabobi dakuma rashin tsari na gari.
A halin yanzu dai wasu kungiyoyi uku na duniya, hukumar raya kasa UNDP, da hukumar
abinci (FAO) da kungiyar raya kasashen kudancin Afrika (SADC) sun kaddamar da
shirin inganta noma
da kiwon dabbobi ta yadda za a magance rashin tabuka abu kan kiwon dabbobi a
Swaziland.
Fanourakis yayi fata da wannan matakin, 'ina mai imani kan wannan tsari da muka
kaddamar zai taimaka wajen inganta harkokin noma da jama'ar mu inji shi.
PANA.
Unesco Ta Bukaci Mata Suyi Bajimta Ranar 8 Ga Watan Maris. 1min. 37secs
An roki daukacin dafofin yada labarai da su baiwa mata 'yan jarida damar
samun gindin zama a jaridar su da
labaran su a ranar mata 'yan jarida ta duniya watau 8 ga watan Maris.
Koichiro Matsuura, babban darektan hukumar UNESCO saida yayi roko tun farkon
watan Fabrairu kan dukkan kafofin yada labarai da su baiwa wannan rana 8 ga
watan Maris muhimmanci ta hanyar ganin matan
sunyi bajimta. 4
4 Page 5 6
5
Vol II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio Maris 2000
'In 'yan jarida da sauran kafofin yada labarai da suke wakilta sun basu damar
haduwa da juna domin samun nasarar shirin, zai zo daidai da tsarin jami'an tace
labaru inji ta.
Ta wannan hanyar bada dama ga kowa ne UNESCO take son jaddada samun labarai
ba tseko ta hanyar baiwa kowa dama daidai-wa-daida ta yadda zamu zama manyan
jami'an tace labarai batare da nuna bambanci
maza da mata ba ko jinsi ko addini.
La'akari da wasu kafofin yada labarai wadanda tuni mata ke shugabancin su kungiyar
ta UNESCO ta kyale su da su yanke shawara kan yadda yafi dacewa su kallamar
da shirin.
UNESCO.
Wata Kungiya Ta Duniya Zata Magance Zazzabin Cizon Sauro A Yankin Neja
Delta. 1min. 17secs
Bayan ziyara sau biyu domin tantance matsayin kiwon lafiya a yankin Neja
Delta yankin da akafi rigima ciki a Najeriya, wata kungiyar da tayi fice a duniya
kan aiyukan jinkai Sans Frontiere (MSF) ta yanke shawarar
gudanar da shirin yaki da zazzabin cizon sauro acan.
Kungiyar daga binciken da ta gudanar ta gano cutar itace ta daya wajen kisa
wanda ta kashe kimanin mutane 100,000 a yankin mai arzikin manfetur.
Aikin zaiyi sansani a Yenagoa hedkwatar jihar Bayelsa, tare da ma'aikata na
farko kwararu biyar da sauran jami'ai 'yan Najeriya su 30. za akuma bullo da
shirin tafi da gidan ka domin tabbatar da ganin aikin yakai ga
daukacin jama'ar na yankin Neja Delta.
Baya ga zazzabi da zazzabin cizon sauro, za a kuma kafa tsarin rigakafi dana
wayar da kan jama'a.
Ita dai kungiyar ta Medicine sans Frontiere tana Najeriya tun 1996 bayan da
cutar sankarau ta barke a arewacin Najeriya kana daga bisani kungiyar ta bada
taimako kan wasu manyan cutuka daga bisani. irin su
lolera da sankarau da ciwon shawara. Medecines Sans Frontiere.
Hukumar Kula Da 'Yan Gudun Hijira Ta Tsaya Kan Kula Da Tsabta 1min. 16secs
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta dukufa kan yekuwar tsabtace
sansanonin 'yan gudun hijira a sashin arewacin Uganda.
Da yake magana kwanan nan a taron karawa juna sani a Kampala ta Uganda Adera
Tsegaye mukaddashin wakilin hukumar, yace hukumar ta sami dala miliyan 42 daga
ma'aikatar tsimi da jam'iyun gama kai na Jamus
(BMZ) domin kyautata yanayin muhalli tare da rage irin abinda ke akwai ga jama'ar
da ke karbar bakwancin su 'yan gudun hijira dake arewacin Uganda. Za a kula
da matakan dake akwai ciki har da dazuka, samar da
kayan aiki da ruwan sha da shirin kula da muhalli ga 'yan gudun hijira da jama'ar
dake tare dasu. inji Tsegaye.
Wanna sabon shirin bashi ne na farko ba a yankin. An gudanar da irin wannan
a arewacin na Uganda tun daga 1996 zuwa 1999. Tsegaye.
Wannan sabon shirin bashi ne na farko ba a yankin. An gudanar da irin wannan
a arewacin na Uganda tun daga 1996 zuwa 1999. Tsegaye yace sabon aikin, za afadada
shi domin taimakawa karin kula da muhalli a
unguwanin da 'yan gudun hijirar kamar su Koboko, da ajumani dakuma Moyo, wadanda
suke da dazuzzuka. New Vision: 5
5 Page 6 7
6
Vol. II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio
Maris 2000
Sarrafa Giza? Gizaiya Kawo Sauki Ga Kauyen Dake Fama Da Fari 2mins. 56secs
Caleta Chungungo, wani kauye ne dake karkashin tsaunuka, dake fama da fari
a kasar Chile dake kudancin Amurka, wanda ya sami hanyar sarrafa giza-gizai.
Caleta na bushewa tare da karewa, har yazuwa lokacin da masana yanayi na Chile
masu bincike na Canada da sauran kungiyoyi na duniya suka tsaida shawarar yin
amfani da abinda garing yafi tamaka dashi
CHAMACHACA, watau gizagizan dake wuce ta garin kusan duk dare.
Kame giza-gizai wata dabara ce kamar sanya bakar gizo cikin kwalba. Amma mazauna
kauyen Caleta sun gano hanyar yin hakan. Sun iya yadda sukeyi domin matso ruwa
daga gizza-gizan dake bushe ta hanyar yin
amfani da raga. Suna da raga 86, wadanda akayi daga nailon, wadanda aka rue
tare da barin ramuka a inda akayi tanadin tara ruwa, wanda girman sa yayi kamar
allon da ake kafawa domin talla akan tsaunin dutse
domin tara ruwan wucewa.
Ruwan dake fadowa daga giza-gizan su ake tarawa, wanda kuma suka tanadar da
fili mai fadi domin wannnan, in har sun girma sai su rika fadowa ta wadan nan
hufin ragar zuwa inda suke taruwa daga nan sai tacewa. A
ranar da tayi kyau ana iya samun lita 700 ruwa.
Bakamar sauran makwabtan sa ba kauyen Caleta na samun sauki daga kogunan dake
kusa. Babban abin ma kauyen na nan ne kan hanyar da babu ruwa sam, inda ba a
wuce samun 7oomm a shekara. A sakamakon
haka Caleta mai mutane 350 tilas sai sun dogara kan motocin dake kawo musu ruwa
daga wasu wurare domin rayuwar su. Hakan na da tsada aikun musamman kauyawan
dake hannu baka hannu kwarya.
Amma daga wannan tsari na amfani da giza-gizai suna samun ruwa lita 300,000
a kowani wata kimanin kowani mutum na samun lita 30, kuma abinda suke kashwa
bai fi kashi uku cikin biyar na abinda suke sayen
ruwa ba.
Wannan hanya mai sauki da saukin samu na ruwa ya taimakawa manoman Caleta kamar
yadda Benjamin Quijandria wani kwarare dan lLatin Amurka a hukumar kula da aikin
gona dake Roma ya fadi. Man oman
dake kauyukan dake kusa sun fara nuna sha'awa kan wannan aiki. Suna duba yiwuwar
fadada aikin domin rage tsadar kudin nomena rani a gonakin su.
The Economist.
Rahotanni
Ra'ayin Jama'a Kan Shari'a 3min 8secs Ra'ayin jama'a da aka gudanar
kwanan nan, da kamfan in RMS yayi, ya nuna wasu 'yan Najeriya basuyi
maraba da bullo da tsarin sharia'a a da gwamnatin jihar Zamfara dake area maso
yammacin Najeriya tayi ba cikin watan Nuwamba 1999. Amfani samun rashin amincewa
bisa tsarin kabilanci dana yanki, kuma akasari
daga mabiya addinin kirista dake kudancin kasar. Haka kuma wasu daga arewacin
kasar ma sun aiyana rashin amincewar su cikin Musulmin da kiristoci. Amma duk
bai isa ya hana bullo da tsarin shari'ar ba a wasu
karin jihohin takwas ta hanyar samun rinjaye mafi kankanta daga jihohin.
Samfur daga mutane sama da 5,000 daga dukkan jihohin tarayya banda zamfara kamfanin
RMS ya gano cewa kimani rabin su basu amince da bullo da tsarin ba a jihar Zamfara,
yayinda daya bisa uku suka amince.
Yawanci 'yan kudancin kasar ne basu amince ba a jihar Lagos kusan kowa bai amince
ba, sai gabashin kasar dakuma yammacin kasar. Ba agudanar da jin ra'ayin ba
a Zamfara saboda tsaro.
Daya daga cikin mutane uku a arewacin Najeriya ne basu amince ba, yayinda
daya cikin goma suka yi tsit da bakin su. Wannan kuwa yafi wadanda aka zata
idan aka bi yadda Gwamnatocin Zamfara da Neja suka fadi
na samun amincewa baki daya game da bullo da tsarin shari'ar. Koda shike rashin
amincewa kan bullo da tsarin shari'a yayi yawa, duk da haka shirin ya sami goyon
baya a jihohi akwai akasari daga sashin arewa 6
6 Page 7 8
7
Vol II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio Maris 2000
maso yamma. Duk da haka ra'ayin ya nuna jihar Neja an sami kashi 31 cikin dari
na reshin amincewa jihar Kaduna kashi 58 cikin dari. Rashin amincewa a jihohin
Bauchi da Adamawa da Gombe da
Nasarawa, da Taraba da Pilato dakuma Kogi ya tashi ne tsakanin 34 zuwa 75 cikin
dari.
Haka kuma ra'ayoyin jama'ar sun nuna biyu daga cikin kowani mutum uku daga arewaci
da kuma daya daga ciki uku na musulmin arewa, suna ukatar gwamnatin tarayya
ta duba wannan lamari game
da hihar Zamfara, Shugaba Olusegun Obasenjo bai fito fili yaki ko ya aminced
da maganar shari'ar ba.
'Wannan rashin tsaida shawara kan batun na baiwa sauan jihohi kwarin gwiwar
cigaba da yin mahawa wajen bullo da tsarin shari'a kamar yadda binciken ya nuna.
Ikirarin da Gwamnan jihar Neja keyi na cewar yayi daidai bisa bukatar akasarin
al'umar jihar yayi daidai. Haka kuma ya nuna hujjoji da ke nuna shari'a ba ra'ayin
al'umar jihar Kaduna bane inda ake
kokarin bullo da tsarin.
Haka kuma inciken ya nuna yadda kiristoci suka nuna rashin amincewar su game
da ullo da shari'ar, ba kamar yadda wasu musulmin suka nuna amincewar su da
bullo da tsarin shari'ar kiristanci in
har akwai. R M S.
Matan Rwanda Na Raba Maza Domin Samun Iyali 3mins 20secs Rashin samun
miji Maatan kasar Rwanda wadanda suka rasa mazajen su da 'ya'yan su a sanadiyar
kisan kare dangi da ya auku a shekarar 1994, yanzu sun fara raba maza tsakanin
su danufin samun iyali. Hakan ya haifar da fargaba tsakanin ma'aikatan kiwon
lafiya, wadanda suka ruwaito kan
karuwar mutanen dake kamuwa da kwayoyin cutar kanjamau bisa wannan tsarin.
Josephine Nyananwandakusi, wanda ta rasa mijin ta da 'ya'yan ta hudu cikin biyar
a lokacin kisan kare dangin, ta matsa ainun wajen sake samo 'ya'yan da ta rasan.
Tace ashirye take ta fuskanci duk wani hatsari kan wannan.
Rayuwa a Rwanda batare da miji da 'ya'yan ba ba rayuwa bace, inji ta. Yanxu
abune mawuyaci samun miji, amma akalla zan sami 'ya'ya inji ta.
Domin samun haka ashirye take domin raba maza da wasu matan irin ta. An kashe
maza da dama, wasu kuma an saure su saboda hannun da suke dashi wajen kisan
kuma babu tabbas na mata irin ta
su sami miji. Amma ta hanyar raba mazaje Nyinawanakusi ta sanya kan ta cikin
hatsarin kamuwa da kanjamau.
Nasan akwai cutar kanjamau, amma samun iyali shine mafi muhimmanci inji ta.
Shirin raba maza, wanda ake kira kwinjira yana yaduwa a yankunan karkara na
kasar Rwanda tun lokacin kisan kare dangin. Yafi tsanani a tsakiyar kasar inda
kisan ya auku ainun. Ance kimanin
mutane 800,000 ne suka mutu a kisan na shekarar 1994. A wasu gundumomin kam
mazajen da suka rage basu fi kashi 20 cikin dari bane na yawan jama'ar.
Tuuni Rwanda na fuskantar hatsari cutar kanjamau. Kimanin kashi 11 cikin dari
na jama'ar kasar ne aka kiyasta sun kamu da kwayoyin cutar HIV, tuni jami'an
kiwon lafiya sun radawa cutar kanjamau
sunan sabuwar kisan kare dangi. Dr. Ildephonse kamali, wanda ke aiki a Asibitin
kabgayi a wajen garin Gitarama yace kashi hamsin cikin dari na wadanda aka gwada
duk suna da mutar ta kanjamau.
Darektan shirin kula da kare yaduwar cutar Innocent Ntaganira yace masu fama
da cutar kanjamau ke kwance a kashi 60 cikin dari na gadajen Asibitin, kana
fiye da mutanen Rwanda dubu metan, dubu
hamsin yara duk sun mutu a sakamakon ita wannan mugunyar cutar. 7
7 Page 8 9
8
Vol. II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio
Maris 2000
Rokon jama'ar da suka ketare rijiya da baya wajen kisan kare dangi mafi muni
tun yakin duniya na biyu na da wuya inji Ntanganira. Wadanda suka ketare rijiyar
sunce fargamar me zasuyi kuma, tunda shike cutar bata
kisa sai bayan shekaru goma. Matan sunce in har kanjami hatsari ne da zasu
fuskanta ashirye suke domin sake samun iyali.
Deseretnews.
Za'a Bullo Da Sabuwar Manufa Kan Dazuzzuka Ta Duniya. 3mins. 7secs Masu
kare dazuzzuka dakuma dangantakar su da tattalin arziki na daukar muhimman matsayi
game da bullo
da sabuwar manufa a Amurka dakuma hukumar hare gandun dazuka ta majalisar dinkin
duniya (UNDP).
Babban taron kasa da kasa kan harkokin gandun dazuka na majalisar dinkin duniya
a New YOrk daga 31 ga watan janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu, ya tattauna kan
shirin da akayi na kulawa dakuma kare dukkan
gandun dazukan da ake dasu a duniya kana a can Amurka maganar dazuka ta sami
shiga cikin kasafin kudin shugaba Bill Clinto na 2001, wanda akayiwa taken 'duniya
mai launin tsanwa', wanda za a tafiyar ta hanyar
yafewa kasashe masu talauci bashin dake kan su muddin suka amince wajen kashe
adadin kudin da ake bin su ta hanyar kula da dazuka.
Wanna babban taron na Gwamnatoci kan gandun zasukan shine na hudu kuma na
karshe shawarwarin da ya bayar na karshe za a gabatar gaban hukumar kula da
raya kasa ta majalisar dinkin duniya.
Taron ya kuma tattauna kan tsari da dokoki game da kare dukkan dazukan da ake
dasu. Haka kuma yayi nazari kan dalilai dake janyo gurbacewar dazuka, dakula
da kare dazuka da irin bukatun dasashe da basa iya
kare dazukan su yadda yakamata dakuma dazukan dake da ruwa, da matsalar wutar
daji da musaya kan fasahar dazuka tare da samar da kudaden da za a tafiyar da
aiyuka.
Ana samun gushewar dazuka a kasashe masu tasowa saboda dalilan samar da katako
dakuma samun filayen noma da sauran su inji rahoton hukumar UNEP. Yanayin duniya
a shekara ta 2000'Anyi asarar kadada
miliyan 65 na dazuzuka tsakanin 1990 zuwa 1995 daga cikin adadin kadada miliyan
3,500 na dazuka dake akwai. Kana inganci ragowar dazukan na fuskantar barazana
daga matsi daga wutar daji ambaliyar ruwa
dakuma sauran aiyuka.
Babban darektan hukumar UNEP Mr. Klaus Toepfer ya gabatar da kasida a wajen
taron wanda ke bukatar mahalarta taron da suyi nazari kan alherin dake akwai
da asuka kama daga na tattalin arziki, da masana'an tu
da al'adu dakuma zamantakewa da sauran aiyuka.
'Kula da gandun dazuka da kare yanayin muhallin mu abune dake tafe tare bisa
kokari cimma daidaito kan cigaban tattalin arziki.... tilas mi dakile abubuwan
dke janyo talauci, da kamfar ruwa da tauyewar makamashi
dakuma tauyewar dazuka'.
Mr. Toepfer yace za afara aiki da manufofin hukumar ta UNEP game da manufar
nan ta aiwatarwa, tare da bada himma wajen kara inganta tsarin hadin kai na
kasa da kasa da kungiyoyi tare kuma da yarjeniyoyi.
UNEP
Duniyar Da Ba Cutar Shan-inna: 4mins. 31secs. (Yayinda duniya ta
maida hankali kan Afrika da Asia domin kauda cutar shan-inna wata 'yar jarida
a India ta
gurgunce bayan da akayi mata allurar rigakafi, amma tace allurar itace mafi
dacewa domin kauda cutar).
Rana ta shida cikin mako a watan Oktoba 1967, na sanya kaya na dakuma takalma
ina tare da kakana, domin karbar allurar rigakafin cutar shan-inna, ina tafiya
ina wasani domin zuwa gun allurar, ban sani ba ashe wannan
shine na karshe da zanyi tafiya bisa kafafuwa na biyu. 8
8 Page 9 10
9
Vol II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio Maris 2000
Bayan da muka dawo, sai na fara jin ciwo a kafafu na, nan da nan sai zazzabi
ya rufe ni. Ba zan taba mantawa da wannan daren ba a rayuwa ta. Kakana sai ya
dauke ni zuwa bayan gida, kafata ta hagu bata tsayawa ga
kuma dan karen zafi.
'Yan kwanaki da suka biyo baya yara iri na sai zuwa sukeyi Asibiti a Jaipur
fadar jihar Rajasthan dake yammacin kasar India. Bayan mako biyu ne da aka auna
sai aka gane ashe cutar shan-inna ne ta bulla. Sauran
wata uku nayi bukin cika shekara uku da haihuwa, gashi na zama gurguwa har abada,
a shekarar 1967. Bullar annobar cutar da ta game kasashe masu arzikin masana'a
tu na kusan shekaru ashirin daga1940s zuwa 1960s
ya gurgunta dubban yara kowace shekara, saida aka sami ingantacen maganin rigakafin
sa tukuna.
Dr. Jonas Salk na Amurka shi ya bullo allurar rigakafi marasa inganci IPV a
shekarar 1955, makashi ne cutar shan-inna tilas ayi mata rigakafi. abokin mahaiyar
Dr. Salk, watau Dr. Albert Sabin, ya kirkiro da sabuwar
allurar da ake digawa a baki OPV, wanda ya kunshi mataki biyar.
A Indiya ana shigo da allurar ta OPV ne daga kasar Rasha, saidai ana bukatar
wurin anada mai sanyi domin kada maganin ya lalace, wanda babu shi a wancan
locaci a Indiya. Kuma yanzu an sami wata na'ura dake
auma ko maganin ya hadu da zafi (VVM).
wasu sunyi ikirarin cewar, allurar da akayi min tare da sauran yara dake fama
da irina ta kare aiki ne. Wasu kuma sunce an bar allurar ne a filin jirgin sama
har rana ta buga, wanda bai iya komai.
A shekarun 1960 babu wayewar kai game da allurar rigakafin cutar shan-inna
a India babu wani matakin da aka dauka, domin haka rayuwa ta gurgunce ga yara
iri na. Mahukuntan sun baiyana cewa wannan annoba ce
kafin rigakafin.
Daya daga cikin allurai miliyan uku da akeyi na OPV ake danganta ta da gurguncewar
allurar rigakafi. Saidai alfanun dake tattare da allurar rigakafin na dayawa
wanda dubban daruruwan yara ke cin moriyar sa a
kowace shekara. Hukumar lafiya ta duniya WHO ta fi bada muhimmanci ga allurar
OPV, wajen kauda cutar ta shan-inna fiye da allurar ta IPV. Ana kuma tafiyar
da shirin a kowace shekara a duniya.
Da nake rubuta wannan yanzu, shekaru 31 daga bisani, har yanzu babu maganin
warkar da cutar shan-inna. Amma akwai rigakafin ta dakuma yekuwar da akeyi a
duniya baki daya domin kauda cutar kafin karshen
wannan shekara.
Yau cutar shan-inna wanda ake kira da cutar gurgunta mutum, an kauda tita a
sassa dayawa na duniya. Wuraren da cutar ta saura sune yankin Saharar Afrika
da kudancin nahiyar Asia.
Neena Bhandari
Hanyoyin Al'adu Na Tatimakawa Wajen Kare Hamada 4mins. 22secs An
gudanar da wani safiyo da nufin tara bayanai kan hanyoyin al'adu na kula da
albarkatun kasa da manoma
keyi dakuma wadanda ke zaune a bakin iyakar saharan Afrika. An tafiyar da safiyon
ne danufin inganta harkokin samar da abinci, da rage talauci tare da karfafa
harkokin kula da aiyukan bincike.
Wanda kungiyar kasa da kasa kan aikin gona da kula da hamada dakuma bincike
ta gudanar, safiyon da aka hada ya kunshi hikima bisa al'ada, wanda ke kula
da muhalli haka kuma an gano hikimar mazauna yankunan
hamada tana bacewa cikin hanzari.
'Ka'idojin nan da tsarin dake taimakawa mazauna bakin yankunan hamada su zauna
lafiya da sauran halittu, sai dade karya su akeyi, bawi da gangan ba sai saboda
rashin wani zabi da za abi'kamar yadda safiyon yayi
bayani. an kaddamar da shirin na mazuna bakin sahara ne domin kare hikimar dake
akwai. 9
9 Page 10 11
10
Vol. II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio
Maris 2000
Al'umar Turkana dake arewa maso yammacin Kenya sukan hukunta duk wanda ya
sare itace daga gandun dajin Moro Anyache, wanda sukayi imanin cewar can ne
asalin su. Haka kuma al'umar suna kare dazukan
dake da alaka da iskokin mutuwa, kana suna da dokoki na shekara da shekaru
dake taimakawa tsirrai da itatuwa da ake samu a bakin kogi da gidaje. Magabata
ke da dazuka, amma kare dazukan alhaki ne da ya
rataye kan al'uma.
Haka kuma Burkina Faso wasu mazauna hamada suna dasa itatuwa irin su acacia
a bakin gonakin su, saboda la'akarin da sukayi na cewa irin wadan nan itacen
suna taimakawa wajen kara yawan kayan amfanin gona.
Haka kuma suna karfafa rike amfanin gona. Haka kuma al'umomin basa yarda ayi
amfanin da wasu nau'in itatuwa domin girki, domin ana cin 'ia'uan su a lokacin
rani, lokacin yunwa.
Kafin 'yan shekarun nan da makiyaya suna kiwon dabbobin su a sashin arewa
ne da damina, kana su komo kudu da rani domin samun abincin dabbobin su. Ana
shuke-shuken kayan gona, kana a barfilaye domin
inganta dausayi. Amma yanzu da jama'a sukayi yawa ba abin wannan al'ada saboda
karancin gonaki.
Yayinda maganar anayi mata lakani da fada tsakanin masu aikin yi da masu kula
da muhalli, Jungwirth, wanda ta fito daga iyayen dake sana'ar katako, tayi imanin
cewar akwai hanyoyin da suka dace wajen kula da
dazuka, wanda kuma zai inganta tattalin arzikin kananan garuruwan. 'yan raji
kare dazuka dake cikin amurka sunyi ta gwada hanyoyi domin horas da wadanda
suka daina aikin katako, domin samun sabuwar sana'a
daufin kare albarkatun dajin, wanda kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.
Wannan aikin daga bangaren ainihin babban aikin da ake kira kare dazuka daga
al'uma'wanda ke shigar da mazauna karkara danufin kula da dazukan. Kauyukan
dake samar da katako irin su Hayfork dake kokarin
rayuwa, ya zama zakaran gwajin dafi.
A shekarar 1993 Jungwith ta fara gudanar da bincike a cibiyar horaswa bisa wannan
sabon tsarin kula da dazuka domin garin su. a shekarar 1996 a sakamakon aikin
ta a Hayfork, an gaiyace ta da shiga cikin hukumar
nan ta majalisar dokokin Amurka mai kula da gandun dazuka, wanda kuma ke samun
taimako daga gidauniyar Ford.
'Sunadaukar kwamiti kan bincike, daya kan manufa daya kan ilmi'inji Jungwirth.
'Nace yaya maganar kwamiti kan al'umomi kuma? domin koda wace iri manufa kuka
yi ko kuka gano a binciken ku ko shirin ilmin ku in
babu sami goyon bayan al'uma ba ab za asami nasara ba.
Yau kwamitin al'uma, wanda take shugabanci ya game kasa baki daya, yana da kungiyoyi
300 kuma shine jigon aiki kan gandun dazuka a Amurka.
Jami'an gandun daji daga nesa kamar India, Mozambique da China sun zo Hay
fork domin koyon aiyukan cibiyoyi tare da karawa juna sani. Sauran aiyuka da
shawarwarin kwamitin yanzu haka kauyuka da garuruwa
suna gwadawa.
Jungwirth ta lura da cewar aiyukan al'uma tilas ne su hadu da sauran aiyuka,
domin haka gari irin Hayfork na iya kirkiro sassa da dama na tattalin arziki,
domin rayuwa. A kusan kowace rana tana kaffa-kaffa. Saidai
akwai aiki ja a gaban ta. Ford Foundation.
Sashin Yara
Tatsuniyar Mutanen Afrika Ta Tsakiya Kan Alfadarin Farko 4mins. 49secs
A farkon duniya, yayinda komai na sabo a doron kasa dabbobi duk iri guda
ne babu wata dabbar dake da
kaho ko launi ko wata siffa ta dabban. Amma a kusa da katon kogo dake kusa da
katon tabki, akwai kahuna iri-iri manya da kanana dakuma launuka iri-iri. 10
10 Page 11 12
11
Vol II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio Maris 2000
Dukkan dabbobin dake zaune a filin dake da ciyawa, suna kiwo, sai aka kira su
aka shaida musu cewar gobe da safe, sai kowace dabba ta shiga cikin kogon ta
zabi irin kahon da take so dakuma launin da yafi dacewa da
ita. Domin haka ko wace dabba tana Allah-Allah safiya tayi domin taje ta zabi
kaho da launin da take sha'awa.
Kowace dabba na doki, banda alfadari, wanda babban abinda ya dame shi shine
cikin sa. A gaskiya ma kowace dobba ta san halin alfadari da ci. Yayinda kowace
dabba ta kama hanya zuwa kogo da sanyin
safiya, alfadari bai tafi tare dasu ba. Yace in har zaiyi doguwan tafiya kamar
haka, to kamata yayi ya cika cikin sa tukuna, baiga wani abin doki ba da sauran
dabbobin keyi kan samun kaho da launi. Koda shike sauran
sauran dabbobin sunce dashi yazo su tafi yace dau su cigaba gashi nan tafe,
in ya karya kumallo. Ya fadi hakan ne kuwa yayida ya hambudi ciyawa. Sauran
dabbobin sukayi tafiyar su suka bar alfadari.
Bayan sa'o'i da dama sai alfadari ya ga yayi tatil da ciyawa, daga nan sai
ya kama hanya zuwa kogo yana bin burtalin da sauran dabbobin suka bi. Yayinda
alfadari ya kusa da kogi sai yaga wasu daga cikin dabbobin
suna dawowa tuni har sun zabi kaho da launin da suke da sha'awa. Giwa ta zabi
launin toka kana ta hada haure guda biyu. Zaki ya zabi launin dabbare-dabbare
mai digon baki.
Daya bayan daya, alfadari na kallon su, suna wucewa da sabbin launi da kahon
da suka zaba. Daga karshe yana dab da shiga kogon, sai alfadari yaga karkanda.
Karkanda tafi gani kurkusa, ta zabi launi masu girma
daban-mai makon ta sanya kahon a kan ta kamar sauran dabbobi, sai karkanda ta
dora kahon kan hancin ta.
Yayinda alfadari ya shiga cikin kogo sai ya tarar ba abinda ya rage sai launin
fari da baki buga da kari kahuna sun kare. Bayan doguwar tafiya gashi kuma ya
fara jin yunwa, domin haka sai yayi sauri ya dauki fari-da-bakin
da ya rage ya sanya kuma ya karbe shi amma shi bai damu ba, kuma bai damu da
rashin kahon da yayi ba. Bayan kowace dabba ta koma ne sai sukeyiwa juna murna
bisa irin zaben launi da kahunan da sukayi.
Yayinda alfadari ya komo bai damu da kowa ba sai ya cigaba da cin ciyawa abin
sa. Sauran dabbobin da suka ga irin abinda alfadari ya samu na fari da baki,
sai suka shiga yi masa ysiya da dariya.
'Dubu sarkin hadama alfadari cikin sabon launin da ya samu, kuma bai da kaho'inji
sauran dabbobin, daga bisa sauran dabbobin kuma suka shiga rera masa waka suna
yi masa shegan taka.
Shidai alfadari bai damu ba. Ba Kaho bane abun da muwa, abin damuwa shine ka
samu abinci mai yawa ka cika ciki, inji alfadari. Shine hae yanzu alfadari baida
kaho amma zaka ganshi a koshe bul-bul-bul, da zanen sa
fari da baki. When Hippo Was Hairy:
Hawainiya Na Haihuwa Ta Hanyar Kashe Kanta? 2mins. 11secs Akwai labaran
al'ajabi a gabashin Afrika na cewar kafin hawainiya ta hailhu sai ta hau kan
itace ta fado cikin
ta ya fashe 'ya'yan su fito. Koda yake wannan babu gaskiya a ciki, amma dai
shike yaduwa. Me yasa wannan al'ajabin ya samo asali? wata kila wata rana wani
ya ga hawainiya ta hau itace ta fado cikin ta ya fashe
'ya'yan ta suka tito.
Yaya hawainiya ke haihuwa? wasu nau'in hawainiyar suna haihuwa ne kan bishiya
su bar 'ya'yan can. Yayinda wasu nau'in kuma ke saka kwai a kasa, dumin kasa
ke taimakawa wajen kyankyasar kwan.
Mutane da dama suna tsoron hawainiya, don haka suke kashe ta. Wannan kuwa
saboda watakila canja launi da takeyi. Hawainiya tana iyacanja duk launin da
take so tana kuma sarrafa idanun ta ta kalli duk kusurwar
da take so a lokaci guda. Dukkan wannan abu na tsoratar da wasu mutane. Amma
sukan taimaka wajen kare su tare da sama musu kwarin da take ci.
Hawainiya tana canjawa zuwa launuka daban-daban. Daga launin kore zuwa algashi
da rawaya da baki. Tana iya maida launin sitin ko farfara, tana iya kuma kara
dabbare-dabbare domin fiddo ta sarari. Saboda
tana yin irin wannnan ne wasu mutanen dauka tana da dafi. 11
11 Page 12 13
12
Vol. II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio
Maris 2000
Amma batada shi. Hawainiya bata da hatsari ga mutum. Bakamar yadda wasu ke
zato ba mutum ba zai mutu ba ko canje launin sa in hawainiya ta cije ka. Hawainiya
tana taimakon mu ma ta wajen cin kwari
dake yi mana ta'adi a gonaki. Saboda haka ne ma ya kamada mu kyale su su cigaba
da rayuwa. Chongololo.
Meyasa Kyankeso Ke Rayuma Tunda Basa Taimakawa Mutum? 58secs Wannan
wata kykkyawar tambay ce, kuma amsar ta na da alaka kan kowace halitta tana
da rawar da zata
taka. Kyankyasai da kudaje suna daga cikin halitun da Allah Yayi dake nasaba
da kazanta. Suna cin matatun dabbobi kuma kuda na daukar ruwan furanni daga
wannnan zuwa wancan.
Kwari da dama ne ke tare da dan adam. Kudaje da kyankyasai suna samun abincin
su ta najasar da adam, da sauran datti. Abin taka ici wani sa'ilin sukan dauki
guba su saka cikin abincin mu. Hakan yakan sanya mu
ciwo, domin haka kamata yayi mu rika rue abincin mu, kana mu rika tsatace ciki
da wajen gidajen mu. In munyi haka za mu rage yawan kudaje da kyankyasai dake
damun mu.
Chogololo
Karin Maganar Raya Kasa: 30secs Kudancin Afrika na da albarkatu da
dama, kama da ma'adinai da makamashi fiye da gabashin Asia, yayinda
ita kuma take da albarkatun jama'a. Yanzu da yake Afrika ta kudu ke fage, mun
fara magance raunin mu na albarkatun jama'a. Nayi imanin zuwa tsakiyar karni
na 21 zamu bugi kirjin cewar Afrika ta kudu ta kawo
karfi irin na gabashin Asia. Christon Tembo, Vice President of Zambia/ The
Courier
Yadda Pokapin Ke Kare 'Ya'yanta 5mins. 43secs Pakara ta cika son 'ya'yan
ta, sai ta birkice. Sai ta fara sa ido domin ko akwai abinda zai nuna mata yadda
'ya'yan nata sukayi. Tana dubawa sai taga takun sawun muzurun dawa. Wannan tsinanen
barawon inji palara. Sai na kama shi. Tayi ta bin sawun har zuwa wata katuwar
bishiya. Inda ta tabbastar da cewa nan
'ya'yan ta suke domin taji kukan su.
Tana cikin wannnan hali sai wani tsoho yazo. Yaga irin halin da take ciki, sai
ya tambaye ta abinda ya faru. Tace dashi 'ya'ya nane muzurun dawa ya ace ya
buya dasu kan wannnan bishiyar.
Kada ki damu inji tsohon, zan karbo miki su. Sai ya fara saran bishiyar daga
tushe har sai da ta fadi kasa. Paakara tayi sauri ta dauko 'ya'yan ta, yayinda
muzurun dawa ya diro ya sheka a guje cikin daji, tsohon kuma
ya bishi a guje.
Yayinda sukayi da gudu cikin sunkuru, sai kurege ya hade dasu, tsohon baiga
hadewar su ba sai yayi ta bin su da gudu yana zaton muzurun dawa yake bi kadai.
Abokin na ka faye gudu inji kurege, ya tambayi muzurun
dawa me ya faru ne ma? Wannan tsohon ne ke bi na na saboda na sace 'ya'yan pakara
inji muzurun dawa. Karkadamu inji kurege saboda kai aboki na ne zan taimake
ka. Washegari kurege ya nemi pakara inda suka
fara tai. Ya gai sheta Nhungu naji ance muzurun dawa ya sace miki 'ya'ya jiya.
Abinda kike bukata shine wuri mai tsaro domin ajiye su. Kuma gashi ina da wuri
mai kyau cikin rami na, inda zaki iya ajiye su batare da
fargaba ba, in kina bukata.
Nagode sosai kurege, domin pakara tajidadin wannan taimako, sai ta kwashi 'ya'yan
ta zuwa ramin kurege ta ajiye su,. Amma yayinda kurege da pakara suka bar ramin
kowa ya kama gaban sa, sai taji kurege na
shaidawa muzurun dawa zo da quri. Pakara ta zuba 'ya'yan ta a rami na. Ashe
pakara na ji, ai ta ganed yaudara ne nan da nan takoma bakin rami inda 'ya'yan
ta suke tayi likimo. Da muzurun dawa ya iso sai yaga
pakara yace kurega ya yaudare shi ya kyale pakara da 'ya'yan ta.
Bisa fushin abinda kurege yayi mata sai pakara ta sami sarkin dawa zaki Khala.
Ta kwashi labari ta gaya masa abinda ya faru tsakanin ta da kurege, kana ta
nemi taimakon zaki domin koyawa kurege darsin da ba zai
manta ba a rayuwar sa. Zaki yayi murna da samun wannan damar, domin kuwa akwai
jikakiya tsakanin su. 12
12 Page 13
13
Vol II Lamba 15 (Hausa) CHANGE Radio Maris 2000
Yayinda sukayi tozali da kurege, zaki yayi gurnani mai tsanani, amma kurege
bai firgita ba, yace meme tsakain ka da 'ya'yan pakara?
Sai ya rika ja da baya kadan kadan yanayiwa zaki bayani. Yace watakila an gayama
karya, abinda ya faru dai ina kare 'ya'yan pakara ne cikin rami na zo ma in
nuna maka zurin. Sai suka juya cikin daji. Zaki yayi gunaki,
sai kurege yayi tsalle ya fada cikin ramin sa domin tsirar da ran sa.
A daidai lokacin kuma an fara cida da tsawa, zaki bai son jika, sai ya tube
kashin jikin sa, ya ajiye a bakin ramin kurege ya nemi wurin fake ruwa cikin
daji. Yayinda aka fara ruwa sai gashin zaki na fadawa cikin ramin
kurege, shi kuwa kurege yana zato har yanzu zaki ne ke tsaye bakin ramin sa.
Amma daga bisani da ya dauki gashin sai ya iske ashe zaki bai bakin remin, sai
ya fashe da dariya. Yace wannan gashin manyan dawa ne, ba
abin tsoro bane, shine kurege yafito daga rami ya sheka a guje cikin daki. Shangani
Folktale.
Yarinyar Da Mafarkin Ta Ya Zama Gaskiya: 3mins. 45secs (Wannan labarin
hakika gaskiya ne ya faru, bayan hatsarin da ta samu lokacin tana yarinya amma
ta cimma
burin ta). A watan Mayun 1985, Sarah Doherty Kellet ta hau dutsen McKinley dake
Alska ta kasar Amurka, amma ba wannan ne ainihim labarin ba na game da hawa
kolouwar ddutse.
Lokacin da take yarinya Sarah tana sha'awar zama 'yar wasanin motsa jiki.
Tayi ta samun horo sosai kan ninkaya dakuma tseren keke, haka kuma tana da sha'awar
hawa dutse. Tana 'yar shekara 13 a 1973 ta sami
hatsarin mota, wanda ta kusan mutuwa. Ba kamar yadda likitoci suka zata ba,
Sarah ta rayu tayiu aiki tukuru inda ta sake samun lafiyar ta. Sarah ta fara
shiga cikin gasar wasanin motsa jiki kadan kadan har ta fara
samun kyautakan bajimta cikin gasar musakai. Haka kuma sha'awar ta na hawa dutse
sai karuwa takeyi. Samun kan hankali ta fara da hawa kananan duwatsu, yayinda
ta fara kwarewa game da hawa dutse. Yayinda
ta fara kwarewa da sanin makaman hawa dutsen burin ta na karuwa. Sai ta fara
rayawa a zuciyar ta game da hawa dutsen McKinley, wanda shine mafi tsawo a arewacin
kasar Amurka, yana da tsawon mita dubu shida
da 194 ga kuma tsananin sanyi can kololuwa.
Damar ta ta hawa dutsen McKinley tazo ne a shekarar 1985, lokacin da aka gayyace
ta zuwa wajen gwajin kayan hawa duwatsu. An gayace ta ne saboda kudurin ta da
karfin halin da take nunawa. Sarah anyi mata
kayan hawa dutsen ne na musamman saboda nakasar ta, wanda take yi bisa kujerar
guragu.
Ranar 29 ga watan Afrilu 1985 suka fara hawa dutsen. Ga Sarah ta fara ne lokacin
da ta hau dutsen dake da daskararen kankare kimanin mita 4,900. Koda yake ga
masu kafa ba abune mai tsayi ba, amma ga ita dake
kan kejar guragu, tayi ta kokartawa dai. Sarah tayi ta hawa dutsen tare da sauran
mutanen. Tawagar ta kafa sansani wajen nisan mita 5,243 kan dutse, sunko zauna
nan har na kwananki uku, saboda guguwar da ta taso
lokacin.
Ranar 19 ga watan Mayu, sararin samaniya ya wartsake, kana su ka cigaba da hawa.
Sarah ta cigaba da yin duk abinda saura masu lafiya keyi. Bayan sa'o' 12 ne
tawagar ta kai kiloluwa. Sarah burin ta ya cika tayi
abin tarihi.
Kamar Sarah rayuwa tun mutum na karami ba koyaushe ke da dadi ba, amma duk da
haka ba zai hana mutum more rayuwar sa ba muddin akwai kuduri. Muddin dai muka
kuduri aniyar cika burin mu to kuwa
zamuyi nasara komai rauni. AHI/ Growing. Up. 13
© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw