Document Body Page Navigation Panel
Ana haka sai Maciji ya fito. Ya dauki kansa ya dora bisa gana ketu. Yin haka
keda wuya sai ketu ya bude idanunsa. Ya Juya kansa domin yaga abinda ke faruwa
sai macijin yayi awon gaba cikin ciyawa. ketu yaji
macijin na cewa "masu binciken banza ! Dama haka suke ! Basu barin mutun ya
rike asiri ! ketu ya barke da dariya, Tsohon mutumen nan ya sunkuya kusa da
ketu ya tambaishi "Me kakewa dariya, ketu? maigari yayi
sauri yace da tsoho "Karka kuma tambayarsa". Nyaloti kuwa sai tace "Ci gaba
da dariya ka ketu. Ba zan kuma damuwa ba."
Nantake sai sauran Jama'a suka barke da dariya. Dariyar data tsorata yarinyar
ta tashi daga baci. Ana dariya kuma anajin kukan yarinyar daga sama-sama, KE-YAA,
KE-YAA, KE-YAA !
Retold by Verna Aardema
Abubuwan Karshe
Ga wadansu abubuwa da muka kalato bayan kammala taron ADF a shekara
ta 2000: -A wannan zamani na fasaha yada Labarai, mu rike WWW a matsayin Jagora.
Muddin muka rike
tare da kula da WWW, ba shakka zamuyi nasara!
Kenneth Kaunda, tsohon shugaban kasar Zambia, yana bada gwarin gwiwa ga "yan
Afrika a yunkurin da sukeyi na yaki da cutar kanJamau.
Zai yiwu a karbi bashi ba taimako ba amma kasashen dake bada taimkon ba zasu
so haka ba. Micheal Kelly, daya daga cikin mahalarta taron ADF 2000, yana Jawabi
akan batun yafewa kasashen
afrika bashi.
Matasa sun nuna bacin ransu a gameda fatara, bashi, cin hanci da kuma rashin
gaskiya
Genevieve -daya daga cikin "yankungiyar matasa ta duniya daya halaci taron ADF
2000
Ga kuma kadan daga cikin hikimomin tsoffin Afrika
Duk wanda yaki neman ilmi zai mutu cikin Jahilci
Maji shawara aikinsa ba zai baci ba Ghana
Shawara mai kyau itace za kaba wani ita Uganda
More African Proverbs
CFC na fata ta gari ga dimbin Jama'ar dake karatun wannan muJalla wato
Change Radio a wannan sabon Lokaci. Barka da sabuwar shekara.
1
1 Page 2 3
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
16
kwanta akan wani karamin gado kusa da bango a cikin bukkar. Nan take su kaji
sauro na kuka a kusa da bakin ko fa yana neman shigowa. Ketu sai yaji auron
na cewa " suna ciki, mutane masu kiba ga kuma dadi !
Amma gashi ba wata kafa mai girma da zan shiga ! " Ketu najin hakas ai ya barke
da dariya harma da mirginawa, ya fado daga kan gado-guf ! Nyaloti tayi wata
irin kara tana mai tambayar sa me kakewa dariya,
ketu ? ketu ya kada baki yace "ba komai" ! ya koma ya kwanta. baice da ita komai
ba.
Can bayan wani dan lokaci saiga wani bera ana kokarin shiga ta kofa. Yayi-yayi
ya kasa. Sai ya zagaya ya samu wata kofa karkashin rufin bukka ya shiga. Yana
tafiya sannu a hankali, yakai ya kawo kan daben dakin.
Can sai ketu yaji yace" ina mamakin inda matan nan ta ajiye kitsen nan!" ketu
ya kuma barkewa da dariya, kye, kye, kye, ! Dariyarsa sai ta tsorata beran.
yayi tsalle ya fada kan gadon Nyaloti -tim ! Nyatoli tayi kara
tace " A-a-a-a". Taimakeni bera" Beran nan take ya kama bango ya sulale ya "gudu.
Nyalti ta tashi ta zauna kan gado. Tace "ketu, ina tsammanin dariyar kace tasa
beran na ya fada kai na ! Me ka kewa dariya? Ketu yace" Ba ko mai
Gari na waye ketu ya kamo wata saniyarsa ya daure jikin wata itaciya domin
Nyaloti ta tatsi nono. Can sai ya hango Nyaloti na zuwa rike da kwarya. Itama
saniyar ta hankalta da zuwan nyaloti, sai ketu yaji tace "ka
gantanan tazo ta sace mani nono ! Wannan karo kuwa ba zata samu komai ba. Domin
kuwa "yata ma na bukatar Nono daza ta sha" Ketu najin haka sai ya barke da dariya,
ke, ke-ke-ke ! abinda ya tsorata saniyar ta
gudu. Nyaloti saita ajiye kwayar kasa domin tayiwa minjinta tsawa. Tace dashi
"me ke baka dariya ne, ketu ? Gashi yanzu ka tsorata saniyar ta gudu wannan
dariyar banzar taka ! koni ka kewa dariya ? "ketu yace" A'a"
ya kama hanya yayi gaba. "ba komai " Gashi kuma saniyar taki samar da Nono.
Nyaloti bata samu ko digo
daya ba a kwaryarta. Amma gashi "yar saniya ta samu nonon da tasha ta shake
cikinta.
Tamkar tasan da wani karin magana dake cewa "Da aci a raga abinci mai dadi,
kwara ciki ya fashe". Marece nayi kuma sandiyar taki samar da Nono. Nyaloti
ta kira ketu, tace dashi" kaga fa ba Nono. "yarmu ga tanan
ba tadalafiya sanadiyar rashin Nonon nan. Ba shakka karamar saniyar nan nason
ta halaka muna yarinya!".
Saniyar saita kada kai ta kalli Nyaloti. Kuma sai ketu yaji tace" Me "yata zata
kashe mata "ya" Ketu yayi
kokarin toshe bakinsa kada yayi dariya. Amma inai sai da tafito ta tsakanin
yatsunsa, gug, gug, gug, saniyar ta tsorata, tasa kafa ta ture kwaryar Nonon,
a cikin wani kazamin wuri. Nyaloti ta kada baki tace dashi "Kalli
abinda ka Jawo!" "kai da wannan banzar dariyar taka" sai na fadawa mai gari.
Nyaloti takai kara wurin mai gari. Maigari ya aika kira ketu da sauran Jama'arsa
a wajen wata bishiya da ake shara'a a tsakiyar gari. Itama
Nyaloti tazo dauke da yarinya a cikin wani abu mai kama da kwando a kanta. Kuma
Jama'a da dama suka
hallara domin jin yadda zata kaya. Maigari, ya bude baki yace ketu, matarka
ta fadaman cewa ka kanyi dariya koma ba wani abin dariya ko gaskiya ya ne ?
ketu cikin mamaki yace "Ban taba yin dariya ba babu wani
dalili. Amma bazan iya fadin wannan dalili ba. In kuma na fadi, zan mutu."
"Maganar banza" Inji maigari. "Magana bata taba kashe wani ba" nyalobi tace
"Ni yakewa dariya. Saboda ni kadai ce a wurin" ketu "a'a ba
haka bane!"
"Inhar ba matarka ka kewa dariya ba, to me ka kewa dariya?" magari ya tambai
shi. Can wani ya daka mai tsawa yace" fada muna. Muma muna son muyi dariya !
"Maigari yace" ketu, idan har bazaka fada ba, to
matarka zata dauki yarinyar ta koma gidansu ta zauna da iyayenta. "Ketu ya
sunkuyar da kansa. Yasa yatsansa karkashi kafarsa dake cikin yashi. Ya kasa
sanin yadda zaiyi. Ana cikin haka sai "yarsa ta fara kuka, ke-yan,
ke-yaa, ke-keyan! Ketu ya kalli Nyaloti tana kokarin sauke kwandon domin ta
ciro yarinyar dake ciki. Ya
kuma ga yadda abinda yayiwa yarinyar na Lallashi yana reto a jikin hannun ta;
Nan take ya fusata yace lalle duk abinda zaifaru, ba zaisa ya kyale matarsa
ba da "yarsa. Don haka sai ya bada labarin maciji, kyauta da
yayi mashi ta asiri da kuma abinda ke bashi dariya a game da dabbobi.
Nan take ya fadi ! Ba rai ! wani tsoho ya kara yace "kalli" irin wannan abu.
"mun tilasa masa yin abinda bai kamata yayi ba. Gashi nan yayi ya mutu !" Nyaloti
da sauran matan da ke nan sai suka fara kuka, wolu, wolu,
wolu, ! Mai gari kuwa yaso ke kai kasa cikin bacin rai. 2
2 Page 3 4
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
-da
aka gabatar, ta nuna cewa cin hanci matsalace mai wuyar bayyanawa kokuma a
fadi ma'anarta a cikin kalma daya, amma duk da haka a iya cewa wata babbar matsalace
da kanyi illa ga ayukan raya kasa kuma ta
zama al'ada a ko ina. Kuma abinda kowa ya sani ne fatara ita ke kawa cin hanci.
Kan haka ne, taron ya goyi bayan a kyautata albashin ma'aikata tare da biyansu
cikin lokacin daya kamata, su kuwa Jamian gwaunati da
aka zaba masu rike da mukamai su rika yin bayani ga Mazabunsu, domin su kuwa
su ilmantar kan ka'idoji tare da yadda ake gudanar da harkokin mulkin dimukuradiya.
A cikin wata takadar bayan taron mai shafi 30 an
bukaci kugiyoyin da bana gwauntiba da su Ja akalar yaki da cin hanci kai ya
kuma kasance NGOS suma su rika yin bayani a game da abinda akeciki.
CFC
Lambobi
An Tsoma Baki Kan Cin Zarafin Da Akewa Mata 3mins. 10secs. A
ranar 25ga watan Nuwamba shekarar ta 2000, Jama'a da dama a ko ina cikin duniya
sunbi sahun "yan
uwansu wajen gudanar da bukukuwa kamarsu bukin Annie Lennox, dawn French,
Ainsley Harriott da kuma
Gab Roslin tare da bugawaga Jaridu domin sanar da ranar da za'ayi bukin white
Ribbon na shekarar ta 2000 domin nuna kin amincewa da cin zarafin da akewa mata.
Ga kuma yadda bayyanan al'kalumma suke:
Mace daya daga cikin mata hudu an taba kuntatamata agida can a wani lokaci
na rayurwata. British Medical Association 1998
A fadin duniya gaba dya, rikicin maza yakan Janyo Mutuwa tare da nakasa
wadansu daga ciki
mata "yan kasa da shekaru 44, fiye da ciwon daji, zazzabi ko kuma yaki kansa.
World Bank discussion paper 255
A Biritaniya ana bugawa Jami'an "yansanda waya tarho 1,300 a kowace rana:
kuma kashi 81 daga cikin 100 na wayar da ake bugawar daga matane wadanda maza
suka kai musu farmaki.
Violence Research Programme, University of London, 2000
Wannan yekuyar da akeyi dangane da cin zarafin mata ba shakka da akwai wani
abu da zata iya aro daga yekuwar yaki da cutar kanjamau ta maJalisar dunkin
duniya. Itama wata matsalace wadda maza kan iya nuna
bambanci ! CFC
Sashin Yara
Meke Baka dariya, Ketu? Tatsunniyartabuwa 21mins. A Afrika, kusa
da tsaunuka da suka tabo wata da akwai wani mazauni wurin da ake kira ketu.
Mutun ne mai
annashuwa Ga kuma wayan dariya. Amma hakan shiya Jefa shi cikin hatsari. Ga
yadda abin ya kasance...........
Wata rana ketu yaji karensa na haushi a bayan bukka. Yana dubawa kuwa sai ya
samu karen na damuwar wani karamin maciji da ba ruwansa. Ketu yayi masa tsawa
ya koreshi daga wurin. Macijin saiya daga kai yace
dashi, "Na gode, Mallam. Da wannan kirki da kayi mani. Bari na sakama da wata
"yar kyauta. Ketu ya kalli maciji , sai ya barke da dariya, ha, ha, ha! yace
"wane irin abune karamar halitta irinka zai bani"? Maciji yace
dashi "Wani asiri ne? Yace "daga yanzu zaka rika jin maganar dabbobi. Amma ka
da ka fadawa kowa, in kuma ka fadawa wani zaka mutu.
Ketu dai baiyi na'an da wannan kyauta ba ballantana ya ce nagode. Don haka
sai ya nemi nuna kin amincewarsa da wannan kyauta. Amma ina ! maciji ya bata.
A daren wannan ranar ne, matar ketu mai suna Nyaloti, ta dauki Jaririn da suka
haifa ta saka a cikin wani karamin gado. Ta sa mashi wani abu a baki domin ta
lallashe shi da wani karamin abu mai kamar gora. Taci
gaba da rarrashinsa domin yayi barci. Tana cikin hakane sai maigidanta ketu
ya bude kofa ya shigo. suka 3
3 Page 4 5
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
14
tayi fice kan a'lamuran kiwon lafiya da kare hakkin bil'adama domin samun wannan
kyauta ta Jonathan Mann. kofa a bude take ga kowa da kowa kama ga na kasa zuwa
manya dake aiki a tarayya ko kuma kasa da kasa.
Kyautar dai ta zunzurutun kudi ne, da ake baiwa wadanda sukayi nasara domin
basu kwarin gwiwa nasu ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Jonthan
Mann wanda aka lakabawa kyautar sunansa wani
mutum ne daya taka rawar gani a karnin na 20 wajen yaki da fatara da kuma cututuka.
Haka kuma jigo ne wajen yekuwa a game da cutar kanJamau da kare hakkin dan Adam.
Ya mutu a cikin wani hatsarin jirgin
samkirar swiss mai lauba 111 a shekarar 1998. Domin tunawa da wannan dan taliki
da kuma ayyukan da yayi wadansu kugiyoyi da suka hada da kungiyar Franccois
xavier Bagnoud, kugiyar likitocita duniya da MaJalisar
kiwon lafiya ta duniya da iyalansa suka shirka bayar da wannan kayauta da sunansa
wato Jonathan Mann wadda ake bayarwa ga wadanda suka taka rawar gani a fannin
kiwon lafiya da kare hakkin dan Adam a duniya.
Kyauta ta uku ta Jonathan Mann za'a bayar da itane a ranar 31 ga watan mayu
a wajen taron majalisar kiwon lafiya
karo na 28 da akanyi shekara-shekara daga 29 na watan mayu zuwa 1 ga watan yuni
a Washington, D. C. Amurka. CFC
Afrika Ta Kudu Zata Dauki Bakunci Taro Na Kasa A Shekara Ta 2002 6mins.
22secs. Ma'aikatar kula da al'amurran muhalli da yawon shakatawa ta Afrika
ta ku1du ta bayyana cewa kwamitin
kula da Muhalli da tabbatar da raya kasashe na maJalisar dunkin duniya ya zabi
Afrika ta kudu a matsayin
kasarda zata dauki bakuncin taro na kasa da za'ayi a shekara ta 2002.
A cikin Jawabinta data gabatar, mukaddashin Ministan kula da al'amurran muhalli
da yawon shakatawa, Re-joice Mabudafhasi, ta furta cewa Afrika ta kudu tayi
marhabin da wannan shawara da aka yanke na gudanar
da wanna taro a nahliyar Afrika. Za'a gudanar da wannan taron ne a birnin Johannesburg
na Afrika ta kudu.
Mabudafhasi, ta kara tana mai cewa "kawo wannan taro na kasa a Afrika ta kudu
wani babban abune ga Afrika a matsayinsa na wani babban taro na ayyukan raya
kasa da zaai gudanar a doron kasarmu wanda zai
tabo matsaloli tare da yin mahawori dake ciki wannan ajenda. watan a cikin
febraiun ne, shugaban kasar Mr, Thabo Mbeki ya roki maJalisar dunkin duniya
data bashi damar daukar bakuncin wannan taron karo na goma
da aka yiwalakabi da taro na kasa a shekara ta 2002 -Yace "yanada amfani a gudanar
da irin wannan taro a
kasashe masu tasowa na duniya" .
Anasaran halartar shugabannin kasashe da dama a wajen wannan taro da akesa
ran yawan mahalarta taron yakai 40,000. Sama da shugabanni 130 ne suka samu
halartar taron da akayi irin wannan a shekarar 1992 tare
dasa ran mafiyawan kasashe membobin maJalisar dunkin duniya 188 dasu tura wakilansu
a wajen taron na
shekara ta 2002 -Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 15,000 ne suka tura wakilansu
a taron da aka gudanar a shekarar 1992.
A cikin wani labari makamancin wannan, hedikwatar maJalisar dunkin duniya
ta sanar da wadannda bayanai wadanda aka tattauna a wajen babban taron maJalisar
kamar haka; cewa taron da Riot + 10 za'a yimai take
da "Taron duniya kan taimakon ayyukan raya kasa". An kuma kafa kwamitoci hudu
domin gudanar da shirye-shiryen gudanar dashi, za ya kunshi kungiyoyin da ba
gwaunatiba da wadansu manyan kungiyoyi da suka
hada da masu hannayen saka Jari da dama domin tattauna wa. Haka kuma za'a bada
dama ga sabbin kungiyoyin daba na gwaunati ba dasu aiko do nasu taimako ga Rio
+ 10.
CFC
An dorawa Kungiyoyin Daba Na Gwaunatiba Hakkin Yaki Dacin Hanci 4mins.
A kwanan nan ne wata tawagar kungiyoyin daba na gwaunati ba suka gudanar
da wani taro na kwana biyu kan
"matsalolin cin hanci da sha'anin mulki. A matsayin Jandar NGOs kan yaki da
cin hanci". Taron ya samu halartar manyan "yan Nijeriya da dama da suka hada
da marubucin nan daya samu kyautar Lambar Nobel
Laurete Wole Soyinka da farfesa Ransome kuti da "yankasuwa da masana. A cikin
wata takardar bayan taro 4
4 Page 5 6
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
akwai jami'an Jinya II, likita daya, da kuma wani jami'i mai kula da asibitin
guda daya... haka kuma da akwai jami'an jinya biyu da wani likita daya a kwance
sanadi yar wanna cuta. Cutar dai nana kamuwa da itane ta
hanyar shigar ji ni. Cutar takan kawo tsi yaye war jini, amma kuma wadansu sukan
haye ta han jinin shiga jikinsu. Associated Press
"Yan Mata Sun Nemi A Dakatarn Da Yiwa Mata Kaciya 2mins. 8secs. Wadansu
"yan mata biyu a kasar kenya sun samo izni daga kotu na hana mahaifinsu tursasa
musa da ayi musu
kaciya. Kotun ta hana Mahiaifin wadannan yara mai suna, pius kandie, wanda manomi
ne a kyauyen simotwo
dakecikin arewacin gundumar keiyo dake kenya, mai tazarar kimanin mil 312 a
arewa maso yammacin Nai-robi, daga dauka "yanmatan zuwa wajen bukin yin kaciya
na gargajiya da aka shiry a ciki watan disambar
shekarar ta 2000. Alkalin kotun majilistare ta keiyo Daniel Ochenja, shine
ya hana kandic da "yankanzaginsa na kai wadannan "yan mata Edna Jebet kandic
mai shekaru 17 da haifuwa da Beatrice mai shekaru 15 dake
karartu a makarantar sakandare yi masu kaciya har sai bayan da aka zauna sauraron
karar da kuma hukeunci
da kotu ta yanke "yanmatan sun kai karane ta hannum wani Lauya, Nixon sifuna,
wanda yayi Musn cewa mahaifin yaran bai nemi ra'ayinsu ba ko suna so kaciyar
ba ko ko kuma ya samu izni daga kotun gargajiya ta
keiyo kamin ya yanke shawarar kaisu wajen yin kaciyar. M, kandie yayi barazanar
kin biyawa wdannan "yanmata biyu kudin makaranta muddin sukaki amincewa da ayi
musu kacuiyar.
Panafrican News Agency
Bow You Must: Kira Na'a Dauki Mataki 5mins. Gwagwarmayar da akeyi domin
hana nuna banbancin jinsi ta samu karbuwa a ranar 2 ga watonNuwamba
shekara ta 2000. Hakan ya faru ne a wajen bukin kaddamar da wani Littafi da
wata mata mai suna Ada Okere Agbasimalo ta rubuta mai suna "Bow You Must". Bukin
ya samu halartar manyan mutane da dama daga
wurare daban-dabanna kasar wadanda keg anin cewa ya kamata a kyautata matsayin
mata. A scikin wannan littafin wanda yake Jami'ar shirye-shirye ce ta hada basirar
dake gareta data Jami'ar John Hopkins wuri guda
in da ta rubuta wani sahihin labari a game da halin da mata ke shiga a kasashe
masu tasowa naduniya. A cikin littafin an bayyana a cikin hanya mai sauki yadda
ake cin zarafin mata dangane da al'amurran da suka shafi
matsalarJama'i, nuna bambanci" hana gado cin zarafin mata matan da mazansu suka
mutuda dai sauransu.
"Bow You Must" wani littafi ne mai dauke da labarinwata mata maisuna meriye,
wadda take uwace mai kwazon aiki, mata, kuma shugabar kungiyar mata wadda duk
da irin mawuyacin halin da ata samu kanta ta
bijirewa yin biyayyar dole ta bukaci yin aiki dominkawo sauyi. A maimakon
ta rubuta abubuwan dake cikin wannan lamari, sai ya kasance littafin yafi maida
hankali ne kan kawo sauyi, sauyin da kungiyar mata ke
Jagoranci .
Wannan Juyin juyajhali shine ya tasimaka wajen fadakar da al'umma a game da:
kyakkyawar rayuwa ga maza mata da kuma kananan yara, da kuma al'ummar da ya
kyautu ta kasance ba tashin haukali, cin rashawa, nuna
kabilauci, gaskiya da halayya mai kyau.
A cikin wannan litafi "Bow You Must' Mawallafiyar littafin Agbasimalo ta kalublanci
al'umma dasu taimakadomin inganta matsanyin mata tare dayin la'akari da irin
abindahakan zai haifar a cikin al'umma. Wannan kira ne na
daukar mataki, kuma kira ne ga daukacin al'umma, kirandaya sabawa tambayar
nan ta ko zakayi biyayyar dole?
CFC
Dandano Jiran Rabo
Kira Kan Nade-Nade 4mins. 50secs.
MaJalisar kula da kiwon lafiya ta duniya na kira ga Jama'a dasu gabatar
da sunayen wadanda suka cancanci a basu kyautar Joathan Mann dangane da rawar
da suka taka wajen kiwon lafiaya d kare hakkin bil'adama a
duniya. Wannan wata babbar dama ce a gareku naku nada wani Jarumi ko kuma
Jarumar kungiyar wadda 5
5 Page 6 7
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
12
marasa rinJaye ba ne suka kunshi Jama'ar da ake ganin ra'ayoyinsu bana zamani
ba ne. mafi yawancin irin wadannan marasa rinJaye wasu mutane ne "yantsiraru
, dakan fake da kabilanci , wariyar launin fata, al'adu ko
kuma addini.
Muddin kuwa aka kafa Jam'iyu kan wannan tafarki, wanda duk yayi nasara ba zai
kula da sauran ba. Kan hakane su marasa rinJaye dake kan mulki ba zasu yadda
ya kubuce masa ba, su kuwa wadanda basu samuba
basuda wata madafa.
Dimukuradiyana yiwuwa ne inhar Jama'a suka shiga ciki, tare da nuna cewa abin
nasu ne. Wannan shi zai tabbatar da cewa ko ta yaya anayi da marasa rinJaye
a cikisha'anin mulki. A wadansu wuraren a kanyi
hakane ta hanyar rarraba harkokin mulki, ta yadda marasarinJaye za'a dama
dasu a cikin sha'anin muliki, a yankunan da sukeda r inJaye. A wasu wuraren
kuwa akanyi hakanne ta hanyar bada dama ga marasa rinJaye
nasu zabi wakilai da zasu wakilcesu a maJalisar tarayya, koma shugabannin zatarwa
ko kuma biyun gaba daya. Abu mafi mahimmanci anan shine bawai hanyoyin da akayi
amfani dasu ba, amma meye sakamako.
Abune mai sauki na shata irin wadannan ka'idoji, amma yanada wuya ayi amfani
dasu, musammanma a kasar
da bata ji ma dafita daga kangin yaki ba, ko kuma a kasar da Jamar ta ke fama
da fatara da kuma yunwa ba. Jama'ar da suka samu kansu a cikin wadannan matsalolisa
iya bada wuya nan take ga wadanda sukayi Juyin
mulki, suna masu nuni da cewa "yanci abune da ya kamata kowa ya samu da kanyi
wuya a kasar dake fama da fatara. So nawa mu kasha jin irin wadannan kalamai
cewa "dimukuradiya na farawa da karin kumallo "ko"
cikin da kejin yunwa kunnensa tosasshe ne".
Amma munsha gani musammamma a Afrika shugabanni basa yin wani abu domin talakawa
musammamma wadanda sukaki bin ra'ayinsu. Munji cewa dimukuradiya na farawa da
karin kumallo, to ya kyautu
a rarraba sha'anin Mulki tun daga gida, a tsakanin uwargidada maigida daga
nan kuma haura ya zuwa koli, tare
da kasancewa haka harya zuwa kasa da kasa.
Zallunci baya maganin fatara. Ba kuma wani ci gaba da ya wuce "yanci. Fatara
da zalunci abokan Juna ne, yayinda raya kasa kan gaskiya zai fitar dakai daga
garesu. Jama'ar mu dake Afrika sun san da haka cewa ba
wata kasa da za'a kirata mai gudanar da mulkin dimukuradiya muddin Jama'ar
ta na cikin fatara, ba kuma wata kasar da zata ci gaba muddin aka batse wasu
daga cikin harkokin mulki.
Raya kasashen Afrika wani abu ne na gwagwarmaya da fatara, ciwo da kuma fada.
Kan hakane ya zamo ba
wani abu bane na mamaki idan har mulkin dimu kuradiya ya samu tangarda a Afrika.
Abin nema dai, shine dimukuradiya kamar yadda Mutanen Afrika suka nuna, mafi
ya wancin kasashe basu damu da kuntatwar da
gwaunatoci keyi ba, ko nasarar da suka samu ba , abinda suke so shine gwaunatic
mai adalci. Mutanen mu sun cimma gurinsu na samun "yancin mulkin kai, amma kuma
tsaida dimukuradiya ya faskara. Godiya ta tabbata ga
Allah daya kawomu wannan lokaci na sake ganin yadda mulkin dimukuradiya ya samu
karbuwa a Afrika a
yau, ya kuma zauna da gindinsa. UN secretary General , Kofi A. Annan, Ghana
Mail
Abin La'akari Yawan Mutanen Da Suka Kamu Da Cutar Ebola Sun
Kai 400 4mins. 5secs.
Yawan Jama'ar da suka kamu da kwayoyin cutar Ebola mai kisa nan ake sunkai
mutane 400 a cikin watan disambar daya gabata, dagacikinsu kuwa mutane 160 ne
suka mutu sanadiyar kamuwa da wannan cuta, inji
wani Jami'in kiwon lafiya. Mutane biyu ne suka mutu a Arewacin birnin Gulu,
yayinda wadansu suka mutu a
masindi mai tazarar mil 125 a Arewa masu yamma da Kampala. In ji Dr. Alex Opio
Wanda mukaddashin darekta ne a cibiyar kula da yaduwar cututka ta kasa. A locaci
daya ne opio ya kuma bayyana cewa wasu
mutane bakwai sun kamu da cutar a Gulu, wadda yake cibiyace ta hana yaduwar
wannan cuta. Yanzu haka dai an tabbatar da cewa cutar ta bayyana a garu ruwan
Gulu, masindi da kuma kyauyen mbararra.
Cutar bata tsaya nan ba domin kuwa ta kama wadansu Jami'an kiyon lafiya a
Gulu. "Yanzu haka dai cutar ta kama kimanin jami'an kiwon lafiya guda 26" inji
opio. "Daga cikin mutane 13 da suka mutu a Gulu Kuwa 6
6 Page 7 8
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
tattauna amfanin yin kawance na kasa da kasa domin yakar kanJamau tare da
bayyana hanyoyin daya kamata abi domin aiwatar dasu: Da suka hada da shigar
da al'umma sanar da Juna, taimakawa wadanda suka kamu da
cutar ta kanJamau (PLWA), kula da mata da kuma al'ummomi domin tabbatar da cewa
abubuwa na gudana kamar yadda ya kamata, kulawar da taimako su hada da samun
magunguna ga wadanda suka kamu da
kanJamau.
Anci gaba da Jaddadawa a wajen taron bukatar dake akwai ta mantawa daduk wani
abu na daban a komakan daukar mataki na hakika. An kuma yi kira ga wadanda suka
saka hannunJari dasu tashi tsaye kan wannan
annoba ta HIV/ Aids. An dai samu kyakkyawan ci gaba a cikin kasa da sauran
kasashen waje tun lokacin da aka kulla kawance na kasa da kasa domin yakar HIV/
Aids a cikin watan Janairun shekarar 1999. Babban ci
gaban da aka samu na kasa ya hada da samun karbuwa ga shugabanni. Misali an
taba tada batun kanJamau a wajen taron kwamitin sasantawa na majalisar dunkin
duniya, kuma sakatare Janar ya kaddamar da kawance
a cikin watan satunmba a shekarar 1999.
An kuma samu karin taimako ga masu hannuJari na kasa da kasa. A cikin kasashe
kuwa kawancen na kasa da kasa kan yakar HIV/ Aids ya haifar da kara sa hannu
shugabani tare da gudamarwa kara daukar matakai,
rarraba ayyukan daga hakimi ya zuwa ga al'umma, tare da raba kudade. CFC
Ra'ayoyi
Kishirwar Siyasa a Afrika 13mins. Da akwai wani karin magana
da mutanen mu keyi a Ghana cewa "kai daya baya isa yanke shawara" . Kullum
na kan tuna da haka a duk lokacin da naji wani yayi kalamincewa "mulkim dimu
kuradiya sabo ne a Afrika, ko kuma cewa mutanen Afrika basu shiryawa dimukuradiya
ba". A zahiri al'ummomin Afrika tun daga
kyauye zuwa birni suna gudanar da abubwansu ne a gargajiyance ta hanyar tattaunawa
a bayyane, tare dajin ra'ayin kowa kamin a cimma matsaya kan wani abu.
Kenan da akwai abubuwa da dama da mutanen Afrika zasu koya daga cikin al'amurransu
na gargajiya, harma su koyawa wasu manufa da kuma abinda dimu kuradiya keciki.
Ya kamata ke nan mu gano cewa
dimukuradiya bata tsaya kadai gayin takaraba, ko kuma wace Jam'iya tafi rinjaye.
ko da yake hakanma ba
abu ne mai saukiba, kamar yadda daya daga cikin kasashen duniya mai tin kaho
da dimukuradiya ta nuna mana. Amma matsalar ta Amurka bashi zaisa mu tsorata
ba da dimukuradiya. A waje daya ma, wanna ya
tunatardamu amfanin gudanar da zabe a kasa mai al'ummomi da yawa da kuma al'adu.
E, ma'anar mulkin dimukuradiya shine rinjaye. Amma hakan ba zai hana marasa
rinjaye ba tofa albar kacin bakinsu wajen yanke shawarwari ba. Bai kyautu a
hana marasa rinjayeba fadar ra'ayinsu. Ya wajaba, a rika
ba marasa rinjaye damar gabatar da bukatarsu, kuma aji ta bakin kowa kamin
a yanke wata shawara. Amma ta yaya Jama'a zasu san da haka? A kauye , watakila
suna iya koyan hakan kai tsaye, ta hanyar cudanya gaba
da gaba da Juna. Amma a halin da ake ciki yanzu Jama'a sunfi dogara ne ga kafafen
yada labarai. kamin a gudanar da zabe na gaskiya, ya kamata a baiwa Jam'iyu
da 'yantakara dama dai-dai a kafafen yada labari
kada kuma ayi amfani. da karfin iko kona kudi wajen yayata wata Jam'iyar fiye
da wata. Ya zama dole ga
kafafen yada labaru. su binciko gaskiya, su kuma kasance sun fadi gaskiyar al'amari
kamar yadda yake. Musammamma kada kuma ayi amfani da karfin iko koma a yada
wataJam'iyar fiye da wata . A duk lokacin
da wani rikici ya kunno kai, lokacin ne da ake bukatar yanJarida su sadaukar
da kansu. Da yawa sun rasa rayuwarsu wajen neman gaskiya. Ku ma suna da hakki
a kan mu . Bugu da kari hakkin mune mutabbatar
damun basu kyakkyawar kariya.
Domin kuwa ra'ayoyinmu da no hakkokinmu ne suke bayyanawa. A cikin mulkin dimukuradiya
na hakika, Jam'iyu suke sasantawa a tsakanin masu Janragamar mulki da "yan adawa,
kasancewa da akwai canjin ra'ayoyi,
kuma marasa rin Jaye na iya zama masu rinjaye. Amma ba haka abin ya keba a
ko'ina. Ba kuma ko wadan ne 7
7 Page 8 9
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
10
Shi kuwa shugaba Mogabe na Botswana cewa yayi ya wajaba garesu dasu kwabi mayan
kamfanoni hada magunguna nasu rage tsadar magungun ta yadda za'a iya sayensua
Afrika. Shugaban kasar Rwanda yayi nuni
ga Jama'a irin matakan da kasashen wannan yanki suka dauka tun shekarar 1999
domin yakar wannan cuta. Yace yayi La'akari dacewa koda shike kashi biyu ne
daga cikin dari na Jama'ar kasar ne kawai suka kamu
da cutar bayan mace-macen da akayi a shekarar 1994, abinya haura zuwa kashi
goma sha daya a shekarar 1998. Ya karada cewa gwaunatinsa na kan yin kokarin
samar da magunguna ga Jama'a da zasu taimaka wajen
rage yaduwar wannan cuta a cikin farashi mai sauki. Mataimakin shugaban kasar
malawi cewa yayi ya kyautu
a kara bada damar samun magungun hana daukar wannan cuta kuma ya kasance daya
da ga cikin a Jandar shugabannin kasashen afrika, kamar yadda matasa suka Jaddadaa
cikin wata takardar koke da suka aika a
wajen taron. Ya kara da cewa "ya kamata mu dukufa wajen yin yekuwar soke bashi,
bawai rage bashi ba" yana mai nuni da cewa yanzu haka bashin da ake bin kasashen
yammacin kudu ga sahara yakai dala biliyan
227. Shugaba yamassoun na kasar chadi ya sanar da mahalartataron cewa mutanen
da suka kamu da cutar
a kassarsa, da ba su wuce mutum biyu ba a shekarar 1986, yanzu sun haura mutane
12,000. Yace koda yake hakan tamkar "daya ne cikin dubu" domin kuwa kwararru
sun kiyasta cewa mutanen dake dauke da cutar a
chadi sunkai tsakanin 40,000 zuwa 50,000. Yace "mun halarci wannan taron ne
domin muyi koyi ga darussan da wadansu suka koya wajen yakar wannan cuta".
Shugaba Niasse na senegal kuwa kirayayi na a dauki. "Kwakwaran mataki domin
yakar wannan cuta. .Sakatare Janar na kungiyar hadakan kasahen afrika, O A U,
salim Ahmed salim ya, furta cewa yana da Muhimmanci
da yake sakonmu ya kai ga "Jama'ar Afrika da kuma abokanmu da suka tayamu gwagwarmaya
da yake abune mai bukatar kulawa ckikin gaggawa. "Yayi kira ga mahalarta taron
dasu maida hankali kan "yarijejeniyar
da aka kulla a wajen taron Addis Ababa da, kudurin aiwatar da ka'idojin". yace
yanjejeniyar da aka kulla
da kuma wadansu makamantan haka zaa gabatar da sune a taro na gaba da za'a gudanaar
a cikin watan Afirilu a birnin Abuja, Nijeriya.
CFC
Kaddamar Da Yaki Kan KanJamau a Afrika 8mins. 13secs. Da akwai bukatar
a tashi tsaye domin yakar kwayoyin cutar HIV/ kanJamau kamar yadda ake yaki
na sosai
idan akayi La'akarida yadda ciwon ke yaduwa tare da fadakar da kowa da kowa
ciki da kuma kasashen ketare. Dole ne muyi kawance na hakikada masu hannun Jari,
musamman al'ummomi, iyaLi da Jama'a
daban-daban, domin magance matsalar HIV/ kanJamau. A sabili da haka ya zama
wajibi ga ko wace tsangaya data dauki mataki na daban na yakar HIV da kanJamau
dangane da yadda suke daukar sabon salo na yadda
suke bullowa.
Ga kuma shawarwari da aka yanke a wajen taron ADF 2000 da aka kammala kwanan
nan. Taron mai taken.
"HIV/ AIDS: Baban kalu bale ga shugbanni" an shirya shine karkashin hukumar
tattalin arzikin kasashen Afrika ta majalisar dunkin duniya. Mahalarta taron
sunyi na'am da'a yi amfani da basirar da aka samu a wurin yaki
domin yakar HIV/ AIDS. Al'ummomi dai sun san yadda zasu timkari wannan cuta
domin haka ya kamata a basu damar yin hakan.
ya kamata ayi amfani da hanyoyin gargajiya dama wadanda bana gargajiya ba
wajen tariyar kudade kuma gwaunatoci suma su ware wani abu na daga cikin abinda
ake samu daga albarkatun kasa domin yakar wannan
annoba.
Da akwai bukatar ,manyan kasashe suma su gyara tsare-tsarensu domin duba wannan
abu mai kama da yaki.
Anyi kira ga bankin, duniya daya binciko illolin bayar da rance domin gudanar
da ayyukan kanjamau, yayinda wadansu ke kiran a soke bashi koma a mayar da bashin
a matsayin taimako. An kumayi kira ga gwaunatoci
dasu bullo da wadansu hanyoyi da zasu iya taimakawa wajen daukar kudi daga
wannan wuri zuwa wancan. An 8
8 Page 9 10
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
halin yanzu fiye da mutane miliyan 36 ne suke fama da cutar kanjamau a duniya
ko kuma suke dauke da kwayoyin cutar dakan haddasa kamuwa da cutar kanjamau,
inji majalisar dunkin duniya, yayinda mutane
miliyan 20 suka mutu sanadiyar kamuwa da cuta a duniya.
Ciwon wanda yake karye garkuwar jiki, akan kamu dashine ta hanyar haduwar jini,
mafisauki daga ciki itace hanyar yin Jamai, maida jinin wani ga wani tare da
yin amfani da allurar da mai dauke da wannan ciwo
yayi amfani da ita. Ciwon yafi yawaita a nahiyar Afrika, ammayanzu haka ya kunno
kai a Asia dakuma Rasha abinda ke neman ya zama tamkar wata annoba. Kamfen da
Majalisar dunkin duniya keyi a wannan shekarar
shine, ki ra ga "maza su nuna banbnci "inda manufar itace ta fadakar da maza
da kuma yara matasa irin hadarin
dake tattare ga yin Jama'i barkatai ko saduwa da mace ba tare dayin amfani da
kororon roba ba tare da kin kula da kiwon lafiya. ko da yaushe kamuwa da wannan
cuta kan iya haddasa mutuwar mata da yawa, kasancewa
su suka fi rayuni kamar yadda UNAIDS wadda wata kungiyace, ta duniya data
daura damarar yaki da kwayoyin cutar HIV dakan hallaka rayuwa.
"An tsammani maza su kasance masu karfi, tausayi zuciya da kuma mazakuta.
Ire-Iren wadannan abubuwan ne kan Jefa mazacikin wani hali da kuma takwarorinsu
mata. Yayinda sakataren majalisar dunikin duniya Mr,
kofi Anan ke cewa "Maza kan iya nuna muhimmin bambanci......................
ta hanya kulawa, saduakar da kai tare da fuskantar cutar kanJamau kai tsaye".
A cikin wani rahoto daya fito daga Majalisa dunkin duniya wanda
aka gabatar aranar Jajibirin bukin ranar kamJamau, na cewa makasudin ganin an
cimma wannan manufa shine
domin hana bazuwar wannan cuta ga yaran da za'a haifa nan gaba ta hanyar Ilmantarwa
kan Jamai da kuma hanyo yin amfani da kororon roba.
Andai kirkiro ranar KanJamaune a wajen wani taro na ministocin kiwon lafiyar
na kasashen duniya daaka kira domin shirye -shiryen magance kanjamau a cikin
watan Janainru na shekarar 1988 .Kuma shine taro kadai
irinsa da akeyi a kowace shekara domin daukar matakai a gameda ciwon kanjamau.
CFC
Shugabannin Kasashen Afrika Sun Sake Jaddada Ra'ayinsu Na Yakar Cutar Kanjamau
11mins . shugabannin kasashen afrika sun Jaddada ra'ayinsu na yakar kwayoyin
cutar HIV da kanjamau awajen wani
taro karo na biyu kan raya kasashen afrika da aka gudanar a cikin watan Disamba
. Daga cikin abubuwan da aka tattauna a wajen taron kuwa sun hadane da kalubalen
da kwayoyin cutar HIV da kanjamau keyi ga
al'amuran raya kasa a nahiyar, hakazalika shugannin sun nuna mahimman cin dake
akwai na wayar dakan Jama'a , inda aka nemi gwaunatocin da suyi yekuwa domin
hana bazuwar wannan cuta. shugaban kasar
uganda yoweri musveni yayi imani da cewa irin wannan yekuwar kantaimaka "sosai
wajen Fadakar da
Jama'a bala'oin dake tattare da wannan cuta". taron wanda ko wane shugaban kasa
ya tofa albarkacin ba kinsa, wanda kuma sakatare Janar na kungiyar hada kan
kasashen afrika Salim Ahmed Salim ya Jagoranta, ya
bayyana cewa cutar kanJamau wani babban kalubale ne ga shugabani kamar dai
yadda yake a cikin ainihin dalilin kiran wannantaro. kasashen Ethiopian, Bostwana,
Rwanda, Malawi , Chadi da kuma senegal dukkansu
sun bayyana irin kokarin da sukeyi a kasashensu domin magance cutar kanJamau.
Prime Ministan kasar Habasha (Ethiopia) meles Zenanawi ya bayyana cewa shi baiga
wani dalili ba da zai hana Afrika samun nasarar a wannan yaki domin kare nahiyarnan
gaba. Yace "abin bukata shine kamata yayi kowa
da kowa a tashi haikan wajen yakar wannan cuta". Shugaba museveni, wanda ake
karamawa a matsayin shugaba na farko a Afrika daya fara daukar babban mataki
a game dawannan cuta, ya bayyana cewa a
lokacin daya fara yekuwa dangane da bullowar cutar kanjamau a wajen tarukan
siyasa, akwatunan rediyo da na talabijin da kuma gun-gun Jama'a kasar sai ya
kasance kowa masaniya a game da wannan cuta dari bisa
daria Uganda. 9
9 Page 10 11
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
8
Aukuwar Wani Hatsari Ya Hana Gano Wani Abin Tarihi 8mins. An gano wani
nau'in kifi (coelacath) mai shekaru miliyan dari hudu a gabar kogin st. Lucia
dake yankin
kwazulu -Natal a kasar Afrika ta kudu. kifin wanda ya zama abin al'ajabi a sabili
da wadansu siffofi dake gareshi, an dauki cewa ya kare kwata -kwata har sai
bayan da akaci karo da gawar irin wannan kifi a cikin
wani taru na wani masunci a gabashin London, a Afrika ta kudu a shekarar 1939.
Wannan Labari ya zama abin bugawa a matsayin kanun labarai ga wadansu Jaridu
na kasa da kasa.
Wasu Jami'ai masu aiki karkashin teku sun samu nasarar dauko hoto sawun irin
wannan kifi guda shida wadanda tsawansu yakai kimanin mita biyu da suka kwashe
shekaru da dama, a cikin wani ruwa mai zurfi
mita 115.
Aukuwar wani hatsari a farkon wannan ma kon ya hana gano wani abu mai ban mamaki
a lokacin da daya daga cikin Jami'an masu aiki karkashin teku mai suna Dennis
Harding dan shekaru 34 ya mutu, a lokacin
da yake daukar hoton wannan kifi. Haka shima takwaransa wanda ba'a fadi sunan
saba ya shiga mawuyacin hali inda da kyar aka cetoshi. Shekaru biyu da suka
gabata irin haka ya taba faruwa, a inda wani wani
Jami'i mai suna Riaan Bouwar ya rasa ransa a wannan wurin a dai-dai lokacin
da yake neman wannan kifi.
Wani mutum kwararre kan al'amurran wannan kifi (coelacath) mai suna Dr, phil
Heemstra wanda ya duba sawun kifayen ya hakikance cewa kifayen ne. A cikin watan
disamba da ya gabatane aka saka sunan gabar
kogin st. Lucia daga cikin jerin sunayen wuraren tarihi na duniya dake Afrika
ta kudu, kuma ya yiwu wannan
abin da aka gano na baya-baya nan ya kara martaba wurin a matsayin wurin yawon
shakawa. Nau'in irin wadannan kifaye da zuriyarsu ta jima tsawon shekaru miliyan
30, sa iya zama misali na karshe na daga cikin
ire-iren kifayen da ake samu, wanda kuma kanyi amfani da filafilan dake gefen
jikinsa a matsayin garkuwa da kuma kafafu.
Daga bayane masana ilimin kimiya suka gano cewar wannan halita mai kafafuwa
hudu na iya rayuwa a sarari. Gano irin wannan kifin da ba'a taba ganin irinsa
ba a Afrika ta kudu a shekarar 1939 an dauke shi tamkar gano
wani abu daga cikin ruwa mai kafafuwa hudu dakan iya rayuwa. Da yake tofa albarkacin
bakinsa dangane da rahoton da aka bayar kan wannan ki fin wani masanin kimiya
a India mai suna ILB smith yace an gano kifin ne
a indian ocean kusa da tsibirin madagascar da Comoro, ya kuma bada sanarwa taredasa
ladan fam 100 ga duk wanda ya kamo irin nau'in wannan kifi. Abinda ya gagara
har ya zuwa shekarar 1952, a Lokacin da aka
sake kama irin wannan kifi karo na biyu a tsibirin comorians dake Ajouan.
Kan hakane gwaunatin Africa ta kudu ta bayar da wani Jirgin saman yaki ga smith
da tawagarsa ya zuwa
wannan tsibiri domin dauko wannan kifi. Aka kuma ci gaba da kama kifin har ya
zuwa shekarar 1980, inda mafi yawan kifayen aka rika kaisu gidajen tarihi da
wadansu wurare domin gudanar da bincike. Sai dai
kuma duk da hakan masana kimiya sunyi imani da cewa yawan kama kifayen da
akeyi domin yin bincike, shi kansa wata barazana ne ga rayuwar wadannan kifayen.
Ya zuwa wannan sati, ba wani nau'in irin wannan kifi
da aka taba kamawa a ruwan Afrika ta kudu.
Da akwai nau'o'in irin wannan kifi guda 125 a cikin wani kudin ajiye sunayen
kayan tarihi, amma nau'i daya ne
kawai aka sani wanda shima yanzu haka ke kan hanyar Salwanta. Pansfrican
News Agency
A wajen Bukin Ranar KanJamau Ta Duniya Na Majalisar Dunkin Duniya An 7mins.
yadda Cewa Cutar Na Karuwa
Ya zama tilas ga maza sun canza fasalin yin Jama'i muddin da akwai bukatar
hana yaduwar cutar nan dake kisa wato kanJamau, kamar yadda majalisar dunkin
duniya tayi gargadi a wajen bukin ranar kanJamauta duniya.
Kwayoyin cutar sun bazu ya zuwa Africa ta kudu, kana kuma abin na kara yawaita
a Asia tare da yin barazanar yaduwa a ciki kasashe masu arziki daka iya sayen
magunguna masu tsada domin kariya ga wannan cuta. A 10
10 Page 11 12
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
rahoton ya bayyana cewa an tabo a tattaunawar da akayi kuwa sun hada da yakin
da akayi tsakanin kasar rasha da chechniya a inda aka nuna halin ko oho ga wahalar
da Jama'a farar hula suka sha a wannan lokaci. Ko
da yake majalisar dunkin duniya tayi Allah wadai da abinda kasar Rasha ta aikata,
ba kuma wata dokar kasa da kasa data ladabatar da moscow dangane da rawar da
ta taka a chechnya.
A saliyo kuwa yanzu haka sabbin abubuwan kuntatawa na dada kunnokai, tsawon
shekaru tara da akayi ana yakin basasa a kasar. Haka kuma kokarin da akeyi na
kafa kotan laifufu kan yaki a kasa, abin na tafiyar
hawainiya.
Sojoji a Colombia kuwa haryanzu basu sasantaba da takwarorinsu wadanda ake cewa
sun keta hakkin
bil'adama. Shugaban kasar Amurka Mr, Bill Clinton wanda shine yasa hannu kan
wadansu ka'idoji a gameda kare hakkin bil'adama a "tsarin colombia: tare bada
dimbin taimako daga Amurka, yayi kusa ya
tabbatar da dagulewar wannan lamari.
Gwaunatin kasar indonesia itama taki tsawatawa ga "yanta'adar Timor ta yamma
wandanda keda alhakin
kai farmaki a Timor ta gabas a shekarar 1999. "Yantawaye a Amboh da Aceh kuwa
suna Jaraba mulkin farar hula ne kan sojoji. Yayin da ita kuwa kasar Isra'ila
tamaida hankali kan boren da palasdinawa keyi aci gaba
mamaye wadansu wurare da sojojin isra'ila keyi ayammaci da kuma zirin Gaza,
wanda hakan ya haddasa mutuwar farar hula da dama.
Da yake buki na goma sha biyar da huklumar kula da 'yangudun hijira ta shirya
wanda za'ayyi a ranar 14 ga watan disamba na matsowa, wasu kasashe masu tasowa
sun dauki nauyin kula da "yan gudun hijirar.
kasashen da sukaci gaba kuwa, wadanda sune sukayi Jagoranci wajen kafa hukumar
kula da masu gudun hijirar (UNHCR), ya kyautu su bada gudunmuwar kudi mafi tsoka
tare da bada damar shigowa kasashen ga
"yan gudun hijira.
Hukumar kula da kare hakkin bil'adama ta furta cewa ba shakka tattalin arziki
na duniya ya samar da dukiya, zarafi da kuma ayyuka. Amma duk da haka bore-boren
da akeyi akan titi na tsawon shekara a seattle, prague,
Washington, D. C. da kuma sauran wurare ya nuna yadda Jama'a suka maida hankali
a wadansu abubuwa marasa kyau da ake aiwatarwa, da suka hada da barin Jama'a
cikin halin talauci da kuma cin zarafin da akewa
bakin ma'aikata. A wata mahawara da akeyi kan tsarin hada duniya, kare hakkin
bil'adama yanada muhimmin amfani ta hanyar tattauna matsaloli da dama, kamar
na yadda wadansu gwaunatoci da hukumoni ke gasa da
Juna domin morar wani abu na daga irin wannan tsaurarawa.
A wurin aiki kuwa, kamata yayi a baiwa ma'aikata damar cudanya da Juna tare
da kafa kungiyoyi domin
neman karin albashi tare da kyautata yanayin aiki. Hakakuma ya kyautu a kawad
da banbanci ta hanyar taimakawa wadanda a tarihi an dakushesu domin suma su
amfana daga cikin guminsu kamar sauran Jama'a.
A bagaren zaman takewa kuwa, ya kyautu ayi Ladabi tare da mina Mutunci da
kuma "yanci na siyasa da suka hada da "yancin zabe da kuma bada dama ga kowa
na ya tofa albarkacin bakinsa dangane da ci gaban kasa ta
harkokin rayuwa da tattalin arziki, da suka hada da karin albashi, kariya ga
shugabannin kungiyoyi domin hana yin ramuwar gayya, hana nuna banbanci, kula
da rage masana'antu, ko kuma tabbatar da cewa an saka
hannayen Jari da kyakkyawar niyya a zuciya.
Duk kuwa da irin giramamawar da mukeyi kan "yanci ba wani tabbas a gameda matsayin
albashi, kyautata yanayin aiki, ko kuma kula da wadansu tsare-tsare. Kuma ba
zai hana nuna banbanci ba a wajen ciniki ko
kawad da wadansu abubuwa marasa kyau. Amma samun "yancin zai iya bada dama
ga al'umma dasu gabatar da kokensu, tare da bada dama ga Jama'ar duniya nasu
tofa albarkacin bakinsu ga ayukan raya kasa.
Human Rights Watch 11
11 Page 12 13
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
6
cewar wani darektan hukumar mai suna clifton curtis "Wanna itace damar da Masu
kulla yarjejeniyar ya kamata suyi amfani da ita domin nuna matsayinsu na kyamar
sinadarai masu guba tare da kammala yarjejeniya
ta farko kan muhalli a cikin wannan sabon karni".
Sinadarai masu guba (Pops) wadansu abubuwa ne da kanyi illa sannu a hankali
ga muhanlli, kuma su kanyi tafiya mai nisa ta iska da ruwa, tare dayin mummunar
illa ga dabbobi da kuma bila'dama.
Salsalarsu kuwa ana danganta ta ne ga haifuwa, ciwon daji da kuma wandansu
matsaloli na raya kasa.
Amma gaskiyar wannan Lamari shi ne da akwai irin wadannan sinadarai a jikin
ko wane dan Adam, maza, yara harma da dabbobi.
Afrika ta kudu ta samu nasarar gano wadansu daga cikin irin wadannan sinadarai
da yanzu haka aka kawad dasu. Wadannan kuwa sun hadane da sinadaran kashe kwari
da wadansu sinadaran kamar su
aldin, dieldrin, chlordane, hexaclorobaizane mirex, toxaphen da kuma heptachlor
wadanda dukkaninsu aka ki yiwa rajista. Biyo baya n illar da wadannan sinadarai
kanyi ga lafiya da muhalli, harilayau su kanyi illa ga
tattalin arziki da kasuwanci, Daga cikin sanadarai da aka fi baiwa fifi ko wajen
kawad dasu kuwa sune wadanda ke fitowa daga masanaantu a duk lokacin da suke
aiki.
Kungiyar hadin gwiwa ta "yanJari bola ta duniya (GAIA) tayi imani da cewa
hanya kadai mafi sauki da za'a iya magance matsalar bola itace ta sake sarafata
tare da bullo da wadansu fasahohi na daba domin
tinkarar wannan matsalar. An dai kulla yarjeniyar hadin gwiwa wadda aka kaddamar
a Afrika ta kududomin dakile matsalar bola wadda kuma tazo dai-dai da shawarar
karshe da gwaunatoci suka dauka. Fiye da
Jami'an kula da Muhalli da kiwon lafiya 70 ne daga kasashe 23 daban-daban suka
hayara domin tattaunawa
dangane da hanyoyin da az'a bi domin magance wannan Malsalar bola domin kariya
ga muhalli da kuma kiwon lafiya.
A farkon taron kungiyoyin kula da muhalli na kasa da kasa sun nuna kin amincewarsu
da tattaunawar da za'ayi, suna masu kira da kulla wata yarjejeniya ta hakika
domin kawad da sinadarai masu guba da kanyi illa
sosai ga bil'adama wadanda kuma sune aka ya waye da su. All African. Com
Bukatar Kariya Ga hakkin Bil'adama a Duniya 13mins. Sha'anin Matsalolin
kare hakkin bil'adama a duniya abune wanda yafi karfin kungiyoyi, kamar yadda
kungiyar
sa ido ga kare hakkin bil'adama ta bayyana. A cikin bincikenta na shekara-shekara
da take gudanarwa dangane da kae hakkin bil'adama a duniyar, kungiyar tayi kira
"da'a kara kaimi domin tinkarar wannan kaluble.
A cikin wani rahoto da kungiyar sa ido ga kare hakkin bil'adama ta gabatar
kamin ranar bukin kare hakkin bil'adama a ranar goma ga watan Disamba, ta bayyana
irin ci gaban da aka samu a kasashe 70 a cikin
shekarar data gabata. Haka kuma tayi sharhi na sosai na yadda al'ummomin kasa
da kasa suka bijirawa cin zarafin da akewa biladama. Ya kamata ga kungiyar "yankasuwa
da masu hannun saka Jari nasu samar da
babbar kariya ga hakkin bil'adama kamar yadda kungiyar sa ido ga kare hakkin
bil'adama ta ambata. Rahoton ya kuma kara da cewa da akwai bukatar majalisar
dunkin duniya nata taimaka wajen kawo
karshen yake-yanken da akeyi da warware matsala "yan gudun hijira.
Tsarin kafa kotunan Laifufukan yaki na kasa da kasa, ciki kuwa harda kutunan
hukunta masu mugun laifi, ya
kamata arinka basu taimako mai tsoka daga kasashe daban-daban ciki kuwa hada
kasar Amurka. A cewar kenneth Roth, wanda darektanea hukuma sa ido ga kare hakkin
bli'adama. ya furta cewa " A duniya ba muda
wadansu kungiyoyi da ke da karfin magance matsalolin kare hakkin bil'adama
kai tsaye a wannan lokaci" ya kara yana mai cewa" da akwai bukatar gyara cikin
gaggawa a wadannan kungiyoyi" Daga cikin abubuwan da 12
12 Page 13 14
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
dasu a cikin shiryen-shiryen kiwatawa, kuma duk mafi yawansu naa kasashen
da suka kaci gaba," Hammond yace "Matsalar da ake fama da ita a game da Muhalli
a koda yaushe a kasahe masu tasowa, da keda yanayi
mai zafi, busashe da laima-laima na bukatar wadansu nau'in dabbobi na musammah
dakan iya rayuwa a cikin irin wannan yanayi". Ya kara yana mai cewa a kasashen
kudu da yammacin sahara dake Afika da akwai Jimlar
nau'in dabbobi 738 inda kimanin kashi 15 na wadannan dabbobi rayuwarsu ke cikin
hadari Pan Afrikan news Agency
An Kasa Cimma Matsaya a Wajen Taron Neman Kawo Sauyi Dangane Da Yanayi
6mins. 30secs. An tashi baram-baram a wajen wani taro da aka gudanar a binin
Hague domin tattaunawa danganedakawo
sauyin yanayi wanda akayi a cikin karshen watan satumba, bayan da aka kwashe
tsawon sati biyu ana tafka mahawarori, a sabili da kin amincewar da wadansu
Ministoci da Jami'an diflomasiya su kayi dangane da fara
aiki da yarJeniyar da aka kulla a kyoto. Haka kuma sunki amincewa kan yadda
za'a karfafa samar da kudade da fasaha a tsakanin kasashen da suka ci gaba da
kasashe masu tasowa kan amintaka dangane da harkokin
yanayi da kuma kere-kere.
Da yake bayyana bacin ransa. Jan pronk, wanda shine shugaban taron kuma minista
kula da muhalli na
kasar Netherlands ya furta cewa "wani babban abin kunya ne ga shugabani na kasa
shata kaidoji rage hayakin dake fita daga manyan gidaJe, duk kuwa da cewa Jama'a
na matukar bukatar haka." Mr, Pronk ya kara da
cewa " Nayi imani da cewa da akwai bukatar yin nasara, kuma nayi amanna da
cewa zamu sake taruwa nan gaba kadan domin kammala wannan batu wanda zai taimaka
wajen daukar wadansu kwararan matakai domin
shawo kan wannan matsalar tare da samar da kariya ga kasashen duniya dake fama
da bala'in zafi".
A wajen taron an samu nasarar samun ci gaba ta hanyar shata ka'idojin bayar
da tallafin kudi da musayar fasaha domin taimakawa ga ksashe masu tasowa nasu
taimaka wajen kawo sauyi dangane da sha'anin yanayi
a kasashen duniya. Amma babbar matsalar itace na yadda za'a rika saye da sayarwa
na daga abinda ake fitarwa daga kasa da kasa wato "hanya kyakkyawa tayin hakan",
da shimfida dokoki domin rage yawan
abinda ake fitarwa na daga cikin iskar da ake shaka wato wadda ke "shiga' kamar
a dazuka, wanda abune mai wuya na samun yin hakan a cikin lokacin da ya rage.
"Shi dai wannan taro ya bayyanar da amfani da kuma matsaloli dake tattare
da kadan na daga cikin abinda ake fitarwar daya shafi tattalin arziki". A cewar
darektan zartawa na shirin kula da muhalli na majalisar dunkin
duniya "ya zuwa wani lokaci na gaba yakamata mu tabbatar da cewa komai ya dai-daita
a maimakon mu dau wani matakin na daban da zaisa muyi dana sani" Wannan daidaitawar
da Mr, Pronk yayi itace zata taimaka
wajen gabatar da taro na gaba na shida da za'a gudanar karkshin Jagorancin taron
kawo sauyin yanayi na majalisar dunkin duniya. Wannan tattaunawar kuwa za'a
yi tane a karshen watan mayu a birnin Bonn, maJalisar
kula da canji yanayi. This Day
Anfara Tattaunawa Kan ILLar Sinadarai a Afrika ta Kudu 8mins. Taron
kulla yarjejeniya na biyar na Majalisar dunkin duniya da aka gudanar a cikin
watan disamba a Johannes
burg, wata damace mai tattare da dimbin tarihi da kan iya hana ko kuma dakatar
da samar da sinadarai masu dauke da guba da kan yi illa kai tsaye ga rayuwar
bila'adama.
Masana sun ambata cewa mahalarta taron wadanda ke tattaunawa domin kulla yarjejeniya
a game da wadannan sinadarai na fatar kawad da sinadarai goma sha biyu masu
tsananin hadari a duniya. Hakazalika
kudurin mahalarta taron ne na ganin cewa sun dakile sauran irin wadannan sinadarai
tare da samar da taimako ta fanin fasaha da kudade ga kasashe masu tasowa domin
suma suci gaba ta wannan bangaren.
Amma a cewar hukumar bayar da tallafi ga halittu ta duniya kamin wannan yarjejeeniyar
ta fara aiki ko kuma a kawad da wadannan sinadarai, ya kamata a taimakawa kasashe
masu tasowa da kudade da kuma fasaha. A 13
13 Page 14 15
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
4
"Hakan shiya nuna cewa kwazo da kwarewar aikin Jarida na taimakawa wajen nuni
ga yadda Jama'a su kayi marhabin da fafutukar kaddarma da kare hakkin bil'adama,
a cewar Aidan white, wanda shine sakatare Janar
na kungiyar tarayyar yanJarida na kasa da kasa, wadda ke shiyar wannan gasa
a kowance shekara. "Alkalan kuwa su kanyi zabe ne daga cikin rahotanni da aka
shigar da kuma rahotanni da ake aikowa daga kasashe
Ar ba'in da hudu. A cikin rahoton nasu da suka gabatar, bayyanai su nuna cewa
ya wajaba Musammamma ga kasashen Arewanci nasu maida hankali ga bayar da rahoto
a wannan bangare".
International Fedeation of Journalists
Ana Hasarar Nau'in Dabbobin Cikin Gida Guda Biyu A Kowane Mako a Duniya
10mins.
An bayyana cewa ana hasarar nauin dabbobi biyu masu mahimmanci a kowane
mako a duniya kamar yadda hukumar kula da abinci da harkokin noma ta maJalisar
dunkin duniya ta bayyana, "Wannan matsala kuwa tafi
kaima ne a Afrika, inda yawan dabbobin da ake hasarar ya karu daga kashi 18
zuwa kashi 19 tun daga shekarar 1995". kamar yadda aka sanar a cikin wata takardar
bayan taro da aka rabawa manema Labarai.
Wannan Matsala tafi yawaita ne a cikin nau'in tsuntsaye inda yawan tsuntsayen
da suka salwanta ya haura
kashi 20 daga cikin 100 a shekarar 1995 zuwa kashi 34 daga cikin 100 a shekarar
1999".
An kuma gano hakanne a cikin wani bincike karo na Uku da aka buga "wanda hukumar
kula da dabbobin cikin gida ta buga" a karkashin wani shiri na hadin gwiwa a
tsakanin hukuma kula da abinci ta duniya
(FAO) da kuma shirin kare muhalli na majalisar dunkin duniya. Tsawon shekaru
goma da suka gabata,
hukumar kula da abinci ta duniya ta taimaka ainun wajen tara bayyanai daga kasashe
guda 170 kan nau'in dabbobi cikin gida 6,500 da tsun tsaye da suka hada da shanu,
awaki, tumaki, kwanta rafi, tankarki, aladu,
dawaki, zomaye, kaji, talatalo, agwagwa, dinya, tantabaru harma da jimina.
"A cikin shekaru 100 da suka gabata anyi hasara kusan nauo'indabbaobi dubu daya.
Hakama a cikin wani sabon bincike damuka gudanar
mun gano cewa rayuwar dabbobin, daake kiwo cikin gida na cikin hadari, inda
kashi 25 na daga cikin irin
wadannan dabbobi ke fama da barazanar karewa", inji keith hammond, wanda Jami'ine
a hukumar kula da abinci ta majalisa dunkin duniya a sashen kula da harkokin
nau'in dabbobi.
Daga cikin wani bayani da hukamar kula da abinci ta majalisar dunkin duniya
ta gabatar, ta sanar da cewa da akwai nau'in dabbobin dake cikin gida kimanin
6,379 wandansu 30 daga cikin su dabbobin ne da
tsunsaye. Bayanan kididigar da aka gudanar sun nuna cewa da akwai kimanin nau'o'in
dabbobi , 183 wadanda daga cikinsu da akwai 740 dasuka kare, yayinda 1335 ko
kuma kashi 35 na daga cikin 100 na irin wandanna
dabbobi ke fama da barazanar karewa. Acewar Hammond, tun daga shekarar 1995
ne yawan dabbobi dake karewa ke yawaita daga kashi 23 zuwa kashi 35 daga cikin
100, da yake a koda yaushe kasashe da dama na
gudanar da bincike tare da samar da bayanai a game da nau'o'in dabbobi. Ta bangaren
tsun tsaye kuwa kusan
matsalar tafi kamari, inda nauin tsantsayen da suka salwanta ya haura kashi
51 daga cikin 100 a shekara 1995 zuwa kashi 63 daga cikin 100 a shekarar 1999.
"Muddin kuwa ba a dau wani mataki ba, ba makawa za'a iya
hasara dabbobi 2, 255 da yanzu haka ke fama da barazanar salwanta a cikin
shekara ashirin masu zuwa." inji Hammond, abune na daban kuma wani abune mawuyaci
da za'a maye gurbinsa. "ko da yake Jami'an kula da
sha'anin nau'o'in dabbobi na kokarin inganta kiyon dabbobi, abune mawuyaci a
maye gurbin nau'o'in dabbobin
da suka salwanta . Irin wannan hasarar abune dakan dore har abadin abada.
Babbar barazana da dabbobin na gida ke fuskanta itace na daukarsu daga kasashen
da sukaci gaba zuwa wadansu kasashe masu tasowa, wanda hakan kan haifar da samun
nau'in dabbobin wata kasa zuwa wata
ko kuma maye gurbin wadansu nau'o'in dabbobin na karkara. A cewarsa. Ko da yake
Jamaa da dama daga
kasashe masu tasowa na ganin cewa dabbobin da aka dauko daga kasashe masu masana'antu
sunfi yawan haifuwa "matsalar itace, irin wadannan dabbobi sunfi sabawa dayanayin
kasashen da suka fito kuma yanada
wuya su saba da yanayin kasashe masu tasowa wanda yake yana da zafi sosai
"Mum kiyasta cewa kimanin nau'in dabbobi 4000 ne Manoma suka waye dasu, amma
kimanin 400 ne na daga cikin dabbobin aka shigar 14
14 Page 15 16
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
Kasar Zimbabwe Ta Tashi Tsaye Domin Mangance Gurbacewar Muhalli 4mins.
17sec. "Wanna Shine Labari Mafi al'jabi dana taba ji tsawon shekarun da
akayi ana yekuwa", inji Emmanuel koro,
wani sananen Jami'in kula da Muhalli, wanda ya furta hakan a dai-dai lokacin
da gwaunatin kasar Zimbabwe ta yanke shawarar ladabar da wandanda ababen hawansu
ke gurbata Muhalli tun daga farkon watan Janairu
na shekara ta 2001.
Shi dai Emmanuel koro na daya daga cikin Jami'an kula da Muhalli dake yekuwa
na tsawon shekaru a gameda
gyara Muhalli, wanda hakan ya tilastawa hukumomin kasar nasu maida hankali a
gameda gyara Muhali wanda suka dauki cewa wani bakon abune kuma wanda bai kamata
a kula da shi ba.
Kawo ya zuwa wannan lokaci, shekaru da dama da suka gabata kasar Zimbabwe
bata taba kafa wandansu dokoki ba dangance da gyara muhali, yanzu haka ma dai
dokokin a rarrabe suke a sabili da cewa suna tattare
da Matsaloli. Amma a wajen Jami'an kula da Muhalli duk wani abu da gwaunti tayi
dangane da rage gurbacewar muhalli ko kuma lala tashi, kamar sabuwar dokar da
aka bullo da ita na sanya haraji ga ababen hawa, wani ci
gaba ne daya kamata ayi Marhabin da shi.
Ministan kudi na kasar Simba Makoni shi ne ya gabatar da wannan doka ta kabar
haraji ga masu ababen
hawa a cikin kasafin kudin da akayi a cikin watan Nuwamba, abinda akesaran ya
taimaka wajen rage gurbacewar Muhali, amma kuma ya kasance wani abu mai Mahimmanci
na fadakar da Jama'a a game da tasftace Muhalli.
Ba shakka hakan yayi dai-dai, sai dai kuma su kansu dokokin da aka shata basu
isa su hana Jama' alalata Muhalli ba, inji mr, koro. Yana mai cewa "abinda muke
bukata anan shine a fadada hanyoyin magance wannan
matsala ta hanyar ilmantarwa tare da tabbatar da kiyayewa da al'adar matsalar
data shafi muhalli. Ya kuma
kara da cewa da akwai bukatar yin amfani da daukacin hanyoyi mafi a'ala a rayuwarmu
ta yau da kullum da za'a rika amfani dasu domin gyara sha'anin muhalli".
A cikin wani bincike da Majalisar dunkin duniya ta gudanar dangane da iska
a kasar Zimbabwe a babban birin kasar, Harare, binciken ya nuna cewa bai dace
ba mutane na shakar wannan iskar, abinda aka danganta
da hayakin dake fitowa daga motoci 400, 000 dake kai kawo a kowace ana. Jami'an
kula da muhalli dai sun dangana gurbacewar MUhallin ga wadannan kananan motoci
da kuma haya kin dake fitowa daga kamfonin da
suaran ma'aikatu. Pan African News Agency
An Bayyana Sunayen "YaJaridar Da Suka Lashe Gasar Tarayyar Turai 3mins.
19secs. Wata kugiyar tarayyar "yanJarida ta kasa da kasa ta bayyana sunayen
"yanJaridar da suka Lashe gasar hukumar
tarayyar turai ta Lorenzo Natali. Ita dai wannan kyautar dakayiwa Lakabi da
kyautar Natali. an fara bayar da itane bayan mutuwar wannan dan taliki wato
Natali wanda kwamishina ne na ayukan ra ya kasa kuma
Jagoran yekuwar kula da kare hakkin bi'adama, wadda ake bayarwa a shekara -shekara
ga duk wani danJarida da yayi rawar ani wajen bayar da rahotanni kan al'amurran
si yasa da kuma kare hakkin bil'adama
a matsayin wani bangare na ci ga ba.
A wannan shekarar dai kyautar wadda ta kai kudin euro 10,000 za'a raba tane
gida biyu, daya ga "Jaridar kungiyoyi hudu da sukayi rawar gani a gasar. Wadanda
suka kuma lashe gasar a bagarorin na duniya guda
biyu, sun hadane da Atiya Achak Ulwisut daga kasar thailand da fariah razak
haroon wani dan Jarida mai zaman kansa dake aiki da wata MuJallah Dawin dake
kasar pakistan.
Wanda ya lashe kyautar farko a bangaren tarayyar turai shi ne Marco Bello
da paolo moiloa wanda ke aiki da wata muJallar Mondo e Missione dake kasar Italy
dakuma wani danJarida mai zama kansa dake taimakawa
MuJallar Deutsches Allgemenies Sonnasblatt . 15
15 Page 16 17
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
2
Ra'ayoyi DIMUKURADIYA DA MULKI MAI KYAU
Kishirwar Afrika kan Dimukuradiya 13mins. 11
Sakatare -Janar na maJalisar dunkinduniya Mr, kofi Anan ya bayyana
ra'ayinsa kan fahimtar daya yiwa mulkin dimukuradia duk kuwa da cewa
kasarsa na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da wani zabe mai dimbin tarihi.
Abin La'akari
KIWON LAFIYA
Cutar Ebola ta Kashe Mutane 160 a Uganda 4mins. 5secs. 12
Yawan Jama'ar da suka kamu da kwayoyin cutan nan mai kisa nan take
wato Ebola yakai mutane 400, haka kuma 160 sun mutu sanadiyar kamuwa da
wannan muguwar cuta.
MATA DA MATASA
"Yanmata sunyi yunkurin Hana yiwa mata kaciya 2mins. 8secs. 13
Wadansu "yanmata biyu a kasar Kenya sun samu izni daga kotu na hana mahai
finsu
tilasta musu ayi masu kaciya.
Bow You Must: Wani Kira na Daukar Mataki 5mins. 13
Gwagwaryar da akeyi na hana nuna bambanci Jinsi an bayyanar da ita a
cikin wani littafi da aka rubuwa kan "yancin mata da Ada Okere Agbasimalo ta
rubuta mai suna "Bow You Must"
Dandano Jiran Rabo
Kira Kan Nade-Nade 4mins. 50secs. 13
MaJalisar kiwon lafiya ta duniya tayi kira da'a aike dusunaye Jam'an
kiwon lafiya
da suka yir awar gani kan ayyukan kiwon lafiya da kare hakkin bil'adama domin
samun
kyauta Jonathan Mann.
Afrika Ta Kudu Zata Dauki Nauyin Bakuncin Taro Na Kasa A Shekara Ta 2002
6mins. 22secs. 14
Ma'aikatar kula da al'amurran da suka shafi muhalli da yawon shakatawon
ta
Afrika ta kudu ta sanar da zaben da akayiwa kasar na daukar nauyin bakuncin
taron maJalisar dunkin duniya kan muhalli da raya kasashe (UNCED)
Lambobi
An tsoma Baki Dagane da cin zarafin da akewa mata 3mins. 10secs.
15
Da yake ranar white ribbon tazo ta wuce, wasu daga cikin al'kallumma
sun nuna
amfani dakatar dacin zarafin da akewa Mata
Shashin Yara
Meke Baka Dariya, Ketu? wata Tatsuniyar tabuwa 21mins. 15
Labarin na wani mutum ne da ake kira Ketu da kuma yadda ya Jefa kansa
cikin hatsari
Abubuwan karshe
Wasu daga cikin karin maganganu na da dana yanzu daga cikin basirar
"yan Afrika. 17 16
16 Page 17
Vol. 11 No. 24
January, 2001 (Hausa) CHANGE Radio
Ayyukan Raya Kasa
KAFOFIN YADA LABARAI
An bayyana sunayen "yanJardar da suka lashe Gasar "yanJarida ta tarayyar
turai 3mins. 19secs. 3
Kungiyar "yanJarida ta kasa da kasa ta bayyana sunayen "yanJaridar da
suka Lashe
gasa tarayyar turai ta Lorenzo Natali.
ADALCI
Bukatar kare hakkin bil'adama a Duniya 13mins. 6
Kamar yadda hukumar kula da kare hakkin bil'adoma ta bayyana, matsalar
kare
hakkin bil'adama a halin yanzu tafi karfin kungi yoyi su magance ta.
KIWON LAFIYA
An yadda da karuwar Bazuwar Cutar KanJamau a duniya wajen taron kanJamau
na 7mins. 8
majalisar dunkin Duniya
Ya waJaba ga maza su Canza fasalin halayyar yin Jama'i muddin da akwai
bukatar
dakile bazuwar cuta kanJamau a duniya, maJalisar dunkin duniya ce tayi wannan
gargadi a wajen taron ranar KanJamau a duniya.
Kaddamar Da Yaki Kan Cutar KanJamau 8mins. 13secs. 10
Bukatar a tashi tsaye domin yakar wannan cuta kamar yaki na gasikya ta
hanyar wayar
dakan Jama'a na kasa da kuma kasa da kasa an bullo da itane a wajen taron raya
kasashen Afrika a shekara ta 2000.
Shugabannin Afrika sun sake Jaddada Ra'ayinsu na yaki da Cutar kanJamau
11mins. 9
Shugabannin Afrika sun aiyana yaki da kwayoyin cutar HIV da kanJamau
a wajen
taro na biyu na raya kasashen Afrika da aka gudanar a Addis Ababa.
Muhalli
GURBACEWAR MUHALLI
Zimbabwe taja Damarar MaganceGurbacewar Muhalli 4mins. 17secs. 3
Shawarar da kasar Zimbabwe yanke na hana abubuwan hawa dasuke gurbata
muhalli yawatawa daga watan Janairun shekara ta 2001 ya samu karbuwa a ko
ina cikin kasar.
An Fara Tattaunawa Kan Sinadarai Masu Muguwar Illa A Afrika Ta Kudu 8mins.
5
Taron sasantawa na biyar na majalisar dunkin duniya da aka gudanar a
birnin
Johannesburg a cikin watan Disamba ya samar da wata dama mai dimbin tarihi
data hana ko kuma ta tsaurara hana yi tare da amfani da sinadarai wadanda
keda guba kai tsaye ga Jama'a.
DABBOBIN DAWA
Ana hasarar nau'in Dabbobin gida Guda biyu a kowane mako a Duniya 10mins.
3
A cewar hukumar kula da abinci da kuma harkokin Noma ta maJalisar dunkin
duniya, ana hasarar nau'in dabbobin gida guda biyu a kowane mako a duniya.
Aukuwar wani hatsari ya hana Gano wani abin Tarihi 8mins. 8
An gano wani kifi mai shekaru dubu 400 a gabar kogin st Lucia dake cikin
yankin
kwazulu -Nataln dake Afrika ta kudu, amma mutuwar rayuka yasa andakar da binciken.
YANAYI
An Kasa Cimma Matsaya A Wajen Taron Neman kawo Sauyi Kan Yanayi 6mins. 30secs.
5
Taron da aka gudanar a Hague domin kawo sauyi kan yanayi ya tabarbare,
bayan da
aka kwashe makwanni biyu ana tafka mahaawarori, a sabili da cewa ministoci da
kuma
Jamai'an diflomasiya sun nuna kin amincewarsu da fara aikida yarJeniyar da aka
kulla a kyoto 17
© 2002 Communicating for Change. All Rights Reserved
Developed by George Mbuagbaw